Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sheikh Sharubutu: Limamin limaman Ghana ya shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya
Limamin limamai na kasar Ghana, Dr Sheikh Osmanu Nuhu Sharubutu, da kuma jagoran kungiyar agaji ta Islamic Council for Development and Humanitarian Services (ICODEHS), sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya na shekarar 2020.
Cibiyar binciken Musulunci ta Royal Islamic Strategic Studies Center ta kasar Jordan, wadda ta shirya wannan karramawa, ta yi karin bayanin cewa an karrama wadannan mutane ne saboda irin ayyukan agaji da jin kai da suke yi a cikin Ghana da ma yammacin Afirka.
'Yan kasar Ghana na ganin wannan mataki a matsayin abin da Hausawa ke cewa "alkhairi danko ne ba ya faduwa kasa banza."
A cewar cibiyar binciken Islama ta Royal Islamic Strategic Studies Centre, an zabi Sheikh Dr Osman Nuhu babban limamin Ghana da Shiekh Mustafa Ibrahim suka shiga cikin sahun Musulman duniya 500 da suke fada-a-ji saboda irin ayyukan da suka yi a bangaren agaji, jin kai, da habaka neman ilimi.
Suleman Mustapha wani dan jarida ne wanda ya wallafa wannan labari kuma ya yi wa abpkin aikinmu na Fahd Adam karin bayani cewa: ''Na farko dai, babban limami Sheikh Usman Nuhu Sharubutu dukkan ayyukan da ya yi, na zaman lafiya ne.
"Yana hada kan Musulmai da wadanda ba ma Musulmi ba.''
Ya ci gaba da cewa: "gaba daya al'ummar Ghana sun amince da shi a kan mutum ne mai son yada zama lafiya.
''Yana da taimako sosai, dukkan abin da ya samu yana zuwa ne ga wadanda ba su da galihu.
"Ya bude makarantar koyon ilimin zaman duniya da na koyar da addinin Islama wanda kowa ya amfana da ita. Shi yasa ya shiga cikin malamai 500 a duniya da suke fada a ji."
Kan batun Sheikh Mustafa Ibrahim kuwa, dan jaridar ya ce sananne ne ga al'ummar Ghana.
"Shi ma ya taimakawa al'ummar Ghana, ya gina masallatai da makarantu, da asibiti da rijiya, yana kuma bayar da karatu cikin sauki."
Wannan dai shi ne karo na biyu da babban limamin Ghana Dakta Shiekh Osman Nuhu Sharubutu yake shiga wannan sahun na Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya.
Wasu al'ummar kasar sun yi kira ga sauran Musulmai masu hali da su kwaikwayi Sharubutu da Sheikh Mustapha don su ma su samu shiga sahun gaba na masu fada-a-ji a duniyar Musulunci