Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarihin Masarautar Hausawan Accra a Ghana
Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
Sarkin Hausawan Accra, Mai Martaba Muhammadu Kabiru Abdulkadir Ingilishi ya bayyana yadda kakansa ya zama Sarkin Hausawan Accra.
Sarkin wanda ya bayyana cewa kakansa ya fara ne daga ''Headman,'' inda daga bisani turawa suka tabbatar masa da sarautar Sarkin Hausawan Accra.
Ya kuma shaida wa BBC cewa har yanzu suna da alaka da Najeriya, kuma suna kai ziyara lokaci zuwa lokaci garinsu, wato garin Gaya da ke Kano.