Ƴar Najeriyar da ta zama Birgediya-janar a rundunar sojin Amurka

Asalin hoton, TWITTER/@CG_ARMYROTC
Ba’amurkiya ‘yar asalin Najeriya mai suna Amanda Azubuike ta samu ƙarin girma daga muƙamin Kanal zuwa Birgediya-janar a rundunar sojin Amurka.
Ta samu ƙarin girman ne bayan da majalisar dattawan Amurka ta amince da ita a watan Yuni.
Azubuike wacce iyayenta suka kasance ‘yan Najeriya, an haife ta ne a birnin Landan, inda ta shiga rundunar sojin Amurka a shekarar 1994.
Da yake taya ta murnar samun ƙarin girman a wani sako da ya wallafa a shafin twita, Manjo-janar Antonio Munera da ke jagorantar makarantar sojoji ta Amurka, ya ce suna farin ciki da samun matsayin a wani biki da aka yi a cibiyar sojoji a Fort Knox a Kentucy da ke Amurka.

Asalin hoton, TWITTER/@CG_ARMYROTC
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Yadda ta samu ƙarin girmar zuwa muƙamin Birgediya-janar

Asalin hoton, INSTAGRAM/AZUBUIKE_IG
Birgediya-janar Amanda I. Azubuike ta kammala karatunta na digiri a Jami’ar Central Arkansas a watan Disamban 1993 a fannin sadarwa.
Ta kuma samu kammala makarantar sojoji a shekarar 1995 a matsayin kwararriya kan tukin jirgin sama.
Ta fara aiki da fara rundunar sojin sama a Georgia, inda ta zama mai jagorantar wata ƙaramar runduna.
Daga baya ta rike muƙamin jami’ar tukin jirgin sama da shugaban wata kamfani ta rundunar sojin sama da wasu rundunoni hadaƙa da masu sanya ido na Sinai da ke Masar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan horo kan bayanan sirrin sojoji, ta kuma yi aiki da runduna ta 3 mai tattara bayanan sirri a Koriya ta Kudu a matsayin jami’ar tuka jirgin sama ta RC-12.
Bayan kammala horo a Koriya ta Kudu, a aike da kanal Azubuike zuwa Fort Jackson da ke South Carolina, a matsayin kwamandar wata runduna mai suna Victory Brigade.
Bayan nan, ta yi horo na jami’an hulda da jama’a, inda ta yi aiki a bangaren dakarun hadaka a ƙasar Kuwait a matsayin jami’ar hulda daga watan Yulin 2005 zuwa watan Yunin 2006.
Daga bisani an tura ta zuwa hedkwatar rundunar sojojiin Amurka a Fort McPherson da ke Georgia.
Bayan halartar kwalejin jami’an rundunar sojoji ta Amurka, kanal Azubuike, ta rike muƙamin shugabar ƴada labaru da hulda da jama’a tare da hedkwatar rundunar sojojiin Amurka a Fort McPherson da ke Georgia.
Duk da cewa an tura ta zuwa Fort McPherson, ta dauki tsawon lokaci a Kuwait tana mara baya ga shirin kwato yanci a Iraqi mai suna Operation Iraqi Freedom.
Daga baya ta halarci jami’ar Georgetown, inda ta yi karatu a fannin Hulda da Jama’a da kuma Sadarwa. Daga bisani an aike ta zuwa ofishin shugaban sashin hulda da jama’a na shirin taimakon al’umma a Pentagon.
Bayan halartar kwalejin horo kan ƴaki na rundunar sojin Amurka, an tura ta zuwa sashin runduna ta 3 a Fort Stewart da ke Georgia, a matsayin daraktar hulda da jama’a, inda bayan hakan, aka sake tura ta zuwa hedkwatar sojoji ta Bagram da ke Afghanistan.

Asalin hoton, TWITTER/@CG_ARMYROTC
Bayan Azubuike ta samu ƙarin girma zuwa kanal, an tura ta zuwa hedkwatar sojojin hadaka da ke birnin Washington a matsayin darektar hulda da jama’a, inda ta jagoranci mambobin jami’an hulda da jama’a, wadanda suka ba da taimako wajen kaddamar da shugaban kasa na 58.
Bayan haka, kanal Azubuike, ta rike muƙamin shugabar jami’an hulda da jama’a a hedkwatar sojoi na Amurka da ke Kudancin Doral, a jihar Florida.
Ta kuma kai matsayin shugabar ma’aikata da kuma babbar mataimakiya a ofishin sakataren tsaro a Pentagon.
Ayyuka da ta je yi zuwa ƙasashe daban-daban ya hada da na samar da ‘yanci a Iraqi, har da Kuwait da Bagram da Afghanistan.
Ta samu lambobin yabo da dama saboda kwazo da ta nuna wajen aiki.











