Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Netherlands ta fitar da Falconets daga Gasar Kofin Duniya ta 'yan shekara 20
Tawagar kwallon kafa ta mata ta Najeriya ta yi ban kwana da Gasar Kofin Duniya ta 'yan kasa da shekara 20 da Costa Rica ke karbar bakunci.
Netherlands ta doke Falconets 2-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a karawar da suka yi a daren Lahadi.
Najeriya ta kai wannan matakin ne, bayan da ta ci dukkan wasa uku a rukuni na uku ta hada maki tara, bayan doke Faransa da Korea da Canada.
Ita kuwa Netherlands ta yi ta biyu a rukuni na hudu da maki shida, biye da Japan ta daya mai maki tara.
Ghana wadda ta wakilci Afirka, ba ta kai zagayen daf da na kusa da na karshen ba, bayan da ta yi ta karshe a rukuni na hudu, amma ba maki ko daya.
Ranar Litinin za a karkare wasan daf da na kusa da na karshe tsakanin Japan da Faransa.
Nasarar da Netherlands ta yi za ta buga wasan daf da karshe da duk wadda ta kai bantenta tsakanin Japan da Faransa ranar 26 ga watan Agusta.
Sifaniya da Brazil za su fara karawar daf da karshe ranar 25 ga watan Agusta a Gasar ta Kofin Duniya.
Japan ce mai rike da Kofin Duniya a Gasar mata 'yan shekara 20 da ta dauka a 2018.