Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Daga ranar Lahadi ba zan kara buga gasar cin kofin duniya ba'
Kyaftin din kwallon Argentina, Lionel Messi ya ce daga wasan karshe na gasar cin kofin duniya a ranar Lahadi ba zai kara buga gasar cin kofin duniya ba.
Kawo yanzu, dan kwallon mai shekaru talatin da biyar ya ci kwallo biyar a gasar da ake buga wa a Qatar.
Duk da cewa sau biyar yana halartar gasar cin kofin duniya, amma har yanzu bai taba lashe gasar gasar.
"Ina murna zan kammala wannan gasar a matakin wasan karshe. Abun jindadi ne", in ji Messi.
Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or sau bakwai sannan ya lashe gasar zakarun Turai sau hudu da kuma na Copa America sau daya tare da Argentina.
A 2014, Argentina ta sha kashi a wasan karshe na gasar cin kofin duniya inda Jamus ta daga kofin a Brazil.
A shekara ta 2026 ne za a sake buga gasar cin kofin duniya inda kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su dauki bakunci.