Me matasan Iran ke so bayan shafe sati uku suna zanga-zanga?

Asalin hoton, UGC
Mako uku ke nan da fara zanga-zanga a faɗin ƙasar Iran, wadda mutuwar wata matashiya ta haddasa.
Tun daga wancan lokaci kuma buƙatun masu zanga-zangar ke ƙara yawa game da abin da matasan ke neman a sauyi a kai.
Abin da ya fara haddasa rikicin shi ne mutuwar Mahsa Amini - matashiyar 'yar ƙabilar Kurdawa wadda ta mutu bayan 'yan sandan addini na Iran sun tsare ta saboda zargin ta da karya dokar rufe gashinsu da hijabi ko ɗan-kwali.
Akasarin masu zanga-zangar mata ne da ke neman sanin dalilin abin da ya kashe ta.
Sun buƙaci bayanai da soke dokar saka hijabi da kuma soke 'yan sandan Hisbah na Iran da ke tabbatar da bin dokar.
'Mace, Rayuwa, 'Yanci'

Asalin hoton, Getty Images
Taken masu zanga-zangar shi ne "Mata, Rayuwa, 'Yanci" - kiran samun daidaito da kuma adawarsu ga dokokin tabbatar da bin addinin Musulunci.
"Wannna sabon take ne da ba mu taɓa ji ba a wuraren zanga-zanga," a cewar Baran Abbasi, babban wakilin Sashen Fasha na BBC.
Su ma maza sun shiga macin suna faɗar taken.
"Lokacin da Mahsa ta rasu, 'yancin mata aka saka a gaba. Sai dai kuma samun 'yancin mata da haƙƙoƙinsu na nufin kowa zai samu 'yanci a Iran," in ji Negin Shiraghaei, wata 'yar gwagwarmayar neman 'yancin mata 'yar Birtaniya da Iran.
Amma yayin da zanga-zangar ke ƙara ƙamari, buƙatun matasan ma na ƙara yawa.
Ana iya jin "Allah ya la'anci shugaban kama-karya" da wasu daga cikin masu zanga-zangar ke faɗa suna nufin shugaban addini na Iran Ayatolah Khomeini.
"Har yara 'yan makaranta za ka ji suna faɗa," in ji Negin Shiraghaei. "Sukan fita tituna...suna neman a hamɓarar da gwamnatin."
Sannan kuma akwai "azadi, azadi, azadi", abin da ke nufin "'yanci, 'yanci, 'yanci," da ake yawan jin wasu ɗalibai na faɗa a jami'o'i.

Asalin hoton, Getty Images
A saƙonnin da suke wallafawa a shafukan zumunta, mutane na amfani da kalmar 'yanci don bayyana sauye-sauyen da suke buƙata, 'yancin ƙyale su su saka abin da suke so da 'yancin ƙyale su su ji kaɗe-kaɗen da suke so - ba tare da tsoron kama su ba.
Buƙatun masu zanga-zangar a taƙaice, Negin Shiraghaei ya ce: "Kawai dai a kan neman 'yanci ne.
Abin da suke fada a kan tituna a kan 'yanci ne, da haƙƙin mata, da kuma neman kifar da gwamnati."
Shahararriyar waƙar zanga-zanga

Asalin hoton, Getty Images
Wani dogon saƙon Twitter da 'yan Iran ke yada wa a shafukan zumunta ya karaɗe gari, inda suke bayyana dalilansu na zanga-zangar.
Kowane saƙo ya fara ne da kalmar "Saboda..." kamar: "Saboda burina,"Saboda daidaito," "Saboda daidaitacciyar rayuwa."
Wata matashiyar mawaƙi da bai shahara ba a Iran mai suna Shervin Hajipou ya ɗauki wasu layuka daga saƙon kuma ya rubuta waƙa. Baitocin waƙar gamayyar saƙonnin ne.
Miliyoyin Iraniyawa na jin daɗin ta. Mutum miliyan 40 ne suka kalle ta a Instagram cikin awa 48 da sakin ta.
"Abu ne da ba a taba gani ba a ce mawaƙin da bai shahara ba ta samu mutane haka," a cewar Taraneh Stone, ɗan jaridar shafukan sada zumunta a Sashen Fasha na BBC.
Jim kaɗan bayan haka 'yan sanda suka kama Shervin Hajipour sannan aka goge waƙar daga shafukansa. An sake shi daga baya.
Ran matasa ya ɓaci
Akasarin masau zanga-zangar matasa ne, wasu ma ba su gama sakandare ba. "An kawo wa jami'o'i tsaiko a faɗin Iran, azuzuwan a rufe suke.
Ɗaliban sun ce ba za su koma ba har sai an saki 'yan uwansu ɗalibai," kamar yadda Negin Shiraghaei ya bayyana.
Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da rayuka ke fusace a wannan ƙarnin. Cin hanci tsakanin 'yan siyasar Iran, da hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kashi 50 cikin 100 da kuma ƙaranci a siyasance da na zamantakewa sun sa ba sa jin daɗi.
A karon farko tun bayan juyin-juya hali na Musulunci a 1979 - lokacin da aka tumɓuke mulkin masarauta aka sauya shi da Jamhuriyar Musulunci - mutane daga ɓangarorin al'umma da dama na gudanar da zanga-zanga a ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Zanga-zangar da aka taɓa yi kafin yanzu
Wannan ce zanga-zanga mafi tsawo da aka taɓa yi a Iran tun bayan juyin juya-hali na 1979.
Zanga-zangar da aka yi a baya - game da sakamakon zaɓen 2009, da matsin tattalin arziki a 2017 da na baya-bayan nan game da ƙarin kuɗin man fetur a 2019 - sun fuskanci rashin imani daga jami'an tsaron Iran.
Yanzu ma abin da mahukunta ke yi ke nan a wannan karon. An kashe gomman mutane tare da kama ɗaruruwa. An yi ta katse intanet don dakatar da mutane daga wallafa bidiyo da hotuna.
Amma duk da haka zanga-zangar ta ci gaba. Ko hakan zai sauya wani abu? "Ina ganin haka," in ji Negin Shiraghaei.
"Idan mata suka fahimci 'yancinsu, kuma suka koya wa 'ya'yansu, dole ne sai an samu sauyi."










