Mutumin da ya kashe matarsa don ta yaɗa mutuwar aurensu a Tiktok

A lokacin da aurenta mai cike da matsala ya mutu, Sania Khan ta fada wa wasu mambobin kungiyarsu ta al’ummar Musulmai ta Kudancin Asiya cewa ji ta yi kamar ‘Rayuwarta ta ƙare’.

Ta samu mafita da goyon baya ta hanyar amfani da manhajar Tiktok – har zuwa lokacin da tsohon mijinta ya dawo da kuma kashe ta.

Wannan labari na dauke da bayanai da za su tayar da hankalin masu karatu

An tara jakankunanta. Ta shirya samun mafita.

Ranar 21 ga watan Yuli, ita ce rana da Sania Khan ,mai shekara 29 tabar Illinois da ke Chicago – bayan samun matsala da aurenta – inda ta koma garin mahaifarta na Chattanooga domin fara sabon babi a rayuwarta.

Maimakon haka, ta koma gida Tennessee a cikin akwatin gawa.

Kwana uku kafin nan, jami’ai sun gano Khan a cikin wani yanayi kusa da kofar gida a Chicago, inda kuma ta rabu da Raheel Ahmad, tsohon mijinta mai shekara 36.

An samu raunukan harbi a bayan wuyarta. Daga bisani aka sanar da rasuwarta a wajen.

Kafin zuwan jami’an ‘yan sanda, Ahmad ya juya bindigar zuwa kansa, inda ya harbe kansa-da-kansa da ta yi sanadiyyar daukar rayuwarsa.

A cewar rahotannin ‘yan sanda da kuma aka yada a jaridar Chicago ta Sun-Times, ma’auratan biyu sun rabu da juna.’’

Sannan Ahmad, wanda ya tafi zuwa wata jiha domin rayuwa bayan rabuwa da Khan, ya yi tafiyar nisan mil 700 zuwa tsohon gidansu ‘domin daidaita aurensu’’.

Kisan gillar, ita ce abu mai sosa rai da ya faru kann rayuwar Khan, matashiyar mai daukar hoto, Ba’amurkiya ‘yar Pakistan wacce ta sanu a baya-bayan nan a kafofin sada zumunta irinsu Tiktok.

Ana daukar ta da cewa mace ce mai fafutukar kare mata da suka samu matsala a aure da kuma tsangwama da ake nunawa matan da aka sake a al’ummomi da ke Kudancin Asiya.

Mutuwar tata ta kada kawayenta har ma da mabiyanta a kafafen sada zumunta da sauran matan Kudancin Asiya da suka ce suna jurewa zama cikin aure mai matsala saboda kar a san da su.

"Ta ce shekara 29 ita ce shekaru da za ta fara sabon rayuwa," a cewar BriAnna Williams, wata kawarta a Jami’a. "Tana cike da farin-ciki."

Ga kawayenta, Khan ta kasance wacce ake son zama da ita akoda yaushe wacce kuma ba ta da matsala.

"Ta kasance mutuniyar da za ta iya tsaya maka," a cewar Mehru Sheikh, mai shekara 31, da ta kira Khan babbar abokiyarta.

"Ko a lokacin da take cikin matsin rayuwa, ita ce ta farko da za ta kira ta tambaye ki ya kike."

A dandalin Instagram, inda ta far bude shafin sada zumunta, ta kwatanta sha’awarta ta son daukar hoto, inda ta yi wani rubutu da ke cewa: "Ina taimaka mutane fara soyayya a tsakanin su, dukkansu kuma a gaban na’urar daukar hoto."

Khan ta kasance mai daukar hoton bikin aure da asibitoci da abubuwan da ake yi wa yara wanka da sauran nasarori da ta samu musamman daga mutane da ke biyanta makudan kudade da kuma kawayenta.

"Tsayawa a bayan na’urar daukar hoto, shi ne wurin da tafi jin dadi, a cewar Ms Sheikh.

"Tana jin dadin daukar hoton mutane, musamman ma hotuna masu farin-ciki da kuma tausayi."

Hakan ya kasance abu da ke sanya ta farin-ciki a rayuwa.

Bayan yin soyayya da Ahmad na tsawon shekara biyar, daga karshe ta aure shi a watan Yunin, 2021, inda suka koma da zama a Chicago.

"Sun yi aure gagarumi, mai cike da annashuwa da kuma yan Pakistan,’’ a cewar wata kawarta da suka taso tare. ‘Sai dai an gina auren kan karya da kuma rashin kula."

Wata kawarta, ta bayyana cewa, Ahmad ya dade yana da matsalar kwakwalwa. Ma’auratan sun dauki tsawon lokaci suna soyayya kafin su yi aure, wani abu kuma da kawayenta suka ce na daya daga cikin abubuwan da suka janyo samun matsala a auren.

Abubuwa sun rincabe ne a watan Disamban bara, lokaci kuma da kawarta ta ce ta fada mata cewa Ahmad na fama da matsalar kwakwalwa da ya sanyata rashin kwanciyar hankali.

BBC ta kasa samun iyalan Ahmad domin martani.

Mambobin iyalan Khan da kuma kawayenta sun ki cewa uffan kan labarin.

Ana samun gomman mutane da ake kashe wa a Amurka a kowan mako, inda kashi biyu bisa uku ke faruwa kan ma’aurata, a cewar cibiyar bincike kan cin-zarafi tsakanin ma’aurata.

Ana danganta matsalar kwakwalwa da kuma matsala a aure a mastayin abubuwa na gaba-gaba da ke sanya mata fuskantar cin zarafi daga wajen ‘yan uwansu maza.

Masana sha’anin cin zarafi sun ce a yawana lokaci mata ne ke shiga barazana ta kisa daga ‘yan uwansu maza muddin suka yi yunkurin rabuwa.

Lamarin da ya faru a watan Disamba ya janyo hankalin Khan – wadda ta ki fadin yadda zaman aurensu yake – na ganin ta fito fili ta yi magana kan rashin jin dadi a aure da take ciki, a cewar wata kawarta.

Sun ce Khan ta bayyana matsaloli da take fuskanta cikin aurenta, inda ta fada musu cewa baya kwanciya da ita da yin abubuwa da bai saba yi ba da kuma zuwa neman shawara, inda matsalar kwakwalwar sa ya zama abu da ke damunta. 

Sai dai kawayenya sun yi zargin cewa, lokacin da suka fad awa kawar ta su ta rabu da aurenta, wasu sun bata shawarar ci gaba da zama.

Ms Williams, mai shekara 26, ta ce ta samu Khan cikin kunci a haduwarsu ta karshe a Chicago a watan Mayu.

"Ta fada mani cewa ana daukar saki a matsayin abin kunya kuma ta kasance ita kadai,’’ inda ta tuno wata magana da Khan ta yi ‘Me mutane za su ce’’, abin da aka fi sani da ‘log kya kahenge’ cikin yaren Urdu da Hindu.

Khan ta ce ta fuskanci tsangwama bayan rabuwa da mijinta daga wajen wasu al’ummomin Kudancin Asiya kan matan da suka bar aurensu.

"Akwai matsin lamba ta al’ada daga wajen iyalai da kuma yadda duniya ke kallon abun,’’ a cewar Neha Gill, darektar Apha Ghar, wata kungiya a Chicago da ke bayar da shawarwari ga matan Kudancin Asiya da ke fuskantar cin zarafi na aure.

Yawancin al’ummomin Kudancin Asiya na kallon mata a matsayin kaskantattu da ke son ayi iko da su, a cewar Ms Gill, inda ta kara da cewa ‘Al’adun ababe ne da mutane suka sani, don haka batu ne na bai wa iyalai da kuma al’ummomi fifiko a kan kwanciyar hankali na wani mutum daya.’’

Sai dai da taimakon kawayenta, Khan ta samu nasarar kai kara da nema mijinta ya sake ta, inda aka sanya watan Augusta domin kammala sauraron ƙarar ta son rabuwa.

Ta kuma shigar da kara ta gargadi da kuma canza makullan ƙofofin gidansu, a cewar ƙawarta.

Daga nan ne ta fara yada labarinta a dandalin Tiktok, inda ta kwatanta kanta a matsayin ‘wacce aka tsana’’ a yankinta.

Wani rubutu da ta wallafa ya bayyana cewa: ‘Macen da aka yi wa saki a Kudancin Asiya na jin kamar ta rasa komai a rayuwa.’’

"Ƴan uwana sun fada mani cewa idan na bar mijina, na bai wa shaidan damar yin ‘nasara a kaina’, da cewa na yi shiga irinta karuwa sannan idan na koma garin mahaifata za su kashe ni,’’ a cewar wata.

Wata kawarta a Jami’a, Naty, mai shekara 28, da kuma ta bukaci kada a wallafa sunan mahaifinta, ta tuno lokacin farko da aka fara yayata batun Khan a kafofin sada zumunta.

"Tana hura wayata, sannan take cewa wannan shi ne abin da nake son yi da ita: Na son yada batun aure na da kuma zam jagoran mata da aurensu ke mutuwa.’’

A kan kowani wallafa da ta yi, Khan ta jajirce da kuma nuna taimako, duk da cewa ‘ana sukarta’ kan yada batun mutuwar aurenta, a cewar Naty.

A lokacin mutuwarta, sama da mutum 20,000 ke bibiyar Khan a dandalin Tiktok.

Wata Ba’amurkiya Musulma ‘yar asalin Pakistan, Bisma Parvez, mai shekara 35, na daya daga cikinsu.

"Na tuna lokacin da na ga bidiyonta na farko, addu’a kawai na yi mata,’’ a cewar Bisma.

"Ana fada wa mata da ke cikin wannan yanayi cewa su yi hakuri, amma cikin aure mara dadi, yin hakuri ba shi ne mafita ba.’’

Bidiyonta na nuna alhinin rasuwar Khan a dandalin Tiktok na daya daga cikin bidiyoyi da aka yada a dandalin.

Batun rasuwarta ya karu matuka tun bayan lokacin.

Kungiyar Apna Ghar a Chicago, da ke bayar da shawara kan cin zarafi, ta ce za ta gudanar da wata tattaunawa ta bidiyo a cikin watan nan domin tunawa da wata daya da mutuwar Khan.

Mutane da dama dai ciki har da abokai da masu bibiyarta a kafofin sada zumunta na nuna alhinin rasuwar Khan, inda tsoffin kawayenta na makaranta -ta Chattanooga School for Arts and Sciences – suka kirkiro da wani tallafin karatu da sunanta domin tunawa da ita.

"Kowaye na da sirri, sai dai kafofin sada zumunta kan taimaka maka wajen sanin wannan matsalar duniya,’’ a cewar Ms Parvez.

"Muna yawan fada wa mata cewa su kare kansu, amma yana da muhimmanci a samu yara da ke ganin darajar mata. Horon zai fara daga gida kuma ya kamata dukkan magidanta su yi abin da ya dace.’’