Sunak zai maye gurbin Truss a matsayin sabon Firaiministan Birtaniya

Asalin hoton, AFP
Tsohon ministan kudin Birtaniya, Rishi Sunak ya lashe zaben jam'iyyar conservatives, inda ake sa ran rantsar da shi a matsayin sabon firaminista.
Ya samu wannan nasara ne bayan da Boris Johnson ya janye daga ƙoƙarinsa na koma wa kan kujerar.
Ya fafata da Penny Mardaunt da ta rage a cikin masu hamayya da Sunak a takarar shugabancin jam’iyyar Conservative.
Tsohon Firaiminista, Boris Johnson ya janye daga takarar duk da cewa ya ce ya samu adadin 'yan majalisar da za su mara masa baya domin shiga takarar sake neman kujerar da ya bari a makonni da suka wuce.
Tun bayan da Liz Truss ta yi murabus kwanaki 45 da hawa kujerar Firaiminista a ƙasar, shi ne aka soma yunkuri na maye gurbinta. Abin da ke nufi ƙasar za ta samu shugaba na uku a cikin wannan shekarar.
Truss ta kasance shugabar da ta fi kowa rashin daɗewa a kan mulki a tarihin ƙasar kuma wanda zai maye gurbinsa zai kasance shugaban jam'iyyar Conservative na biyar a cikin shekaru shida.
Manyan ƴan takara biyu da za su iya fafatawa su ne Rishi Sunak da kuma Penny Mardaunt.
Rishi Sunak

Asalin hoton, Reuters
Tsohon ministan kudi wanda ya sha kaye a takarar shugabancin jam'iyyar Conservative a watan da ya wuce a yanzu shi ne kan gaba.
Iyayen Mista Sunak sun koma Birtaniya ne daga gabashin Afrika kuma asalinsu Indiyawa ne.
An haife shi a Southampton, kuma Sunak ya yi karatu a makarantar kuɗi kafin daga bisani ya shiga jami'ar Oxford da kuma Stanford a Amurka.
An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokoki a Birtaniya a shekarar 2015 sannan kuma a watan Fabarairun 2020 an naɗa shi ministan kuɗi.
Penny Mordaunt

Asalin hoton, Reuters
Ta tsaya takarar shugabancin jam'iyyar Conservative a wancen karon amma Sunak da Truss sun shiga gabanta a zagayen ƙarshe.
Daga bisani ta goyi bayan Truss, inda aka naɗa ta a matsayin shugabar masu rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.
A shekarar 2019, Ms Mordaunt ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta hau kujerar ministar tsaron Birtaniya.
Yadda ake zaɓen sabon shugaba
Da farko ɗan takara na buƙatar ƴan majalisa aƙalla 100 daga cikin ƴan majalisa 357 na jam’iyyar Conservative su goyi bayansa.
Hakan na nufin cewa mutum biyu ne kaɗai za su iya shiga takarar.
Idan har mutum ɗaya ne kacal ya samu wannan adadin, to shi zai zama sabon firaiminista ba tare da hamayya ba.











