Ko za mu iya taɓa sanin asalin wanda ya ƙirƙiro Bitcoin?

- Marubuci, Joe Tidy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Sashen Intanet
- Lokacin karatu: Minti 5
Bitcoin ya kasance ginshiƙin masana'antar kuɗin intanet na kirifto a duniya da darajarsa ta kai dala tiriliyan biyu, yanzu kuma ana hada-hada da shi a manyan gidajen saka hannun jari na duniya, har ma ya zama kuɗin wata ƙasa a hukumance a halin yanzu.
Amma duk da tagomashin da wannan kuɗi ke samu a duniya, har yanzu akwai wani babban abu da ba a sani game da shi ba: mene ne asalin wanda ya ƙirƙiro da wannan kuɗi, Satoshi Nakamoto?
Mutane da yawa sun yi ƙoƙarin amsa wannan tambayar, amma ya zuwa yanzu duk sun kasa.
Don haka, hankali ya karkata a duniyar kirifto baki ɗaya - lokacin da a ranar Alhamis da ta gabata aka yi iƙirarin cewa wanda ya ƙirƙiro da Bitcoin zai bayyana kansa a wani taron manema labarai.
A watan Oktoba, wani fim da kamfanin HBO ya yi ya nuna cewa wani masanin bitcoin na Kanada mai suna Peter Todd shi ne ya ƙirƙiro shi. Matsalar da aka samu ita ce: ya ce ba haka ba ne, kuma duniyar kirifto ta yi watsi da wannan batun.
Mista Todd ne na baya-bayan nan a cikin dogon jerin sanayen wadanda ka iya zama Satoshi - kuma a ranar Alhamis jerin sunayen ya ƙara tsayi.
Akwai sha'awa mai yawa kan ko wane ne Satoshi Nakamoto saboda ya kasance wani ƙasurgumin mai sarrafa manhajoji, wanda ya taimaka wajen kafuwar masana'antar kirifto a duniya.
Muryarsa da ra'ayoyinsa za su yi matuƙar tasiri a kan masana'antar da ke da mabiya da dama a duniya.
Amma wani abu kuma shi ne, a matsayinsa na mamallakin fiye da Bicoin miliyan ɗaya, na iya zama hamshaƙin mai kudi, saboda yadda darajar kuɗin ta kai mataki mafi girma a halin yanzu.
Ganin wannan dimbin arzikin, abin mamaki ne a ji cewar wanda ya shirya taron manema labaran na makon da ya gabata ya buƙaci sai na biya kuɗin kujerar halartar wannan muhimmin bikin.
Idan ina son zama a gaba sai na biya fan £100. Zan kuma ƙara biyan fan £50 idan ba na son a ƙayyade adadin tambayoyin da zan yi. Wanda ya shirya taron, Charles Anderson, har ma ya ƙarfafa min gwiwa da in biya £500 domin samun damar yin hira da "Satoshi" a kan dandalin da za a gabatar da shi.
Na ƙi dai amincewa.
Mista Anderson ya ce duk da haka ina iya halarta amma ya yi gargadin cewa ba lallai ne in samu wurin zama ba.
Amma daga baya mun gano cewa wurin zama ba ita ce matsalar ba.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kimanin ƴan jarida 12 ne kacal suka hallara a shaharren wurin da ake kira Front Line Club - wanda masu gudanar da wurin suka yi bayanin cewa sun bayar da ɗakin ne kawai ba wai suna tabbatar da sahihancin abin da zai gudana ba ne.
Cikin lokaci ƙalilan ya tabbata cewa mafi yawan waɗanda suka halarci taron suna waswasi kan lamarin.
Bayan gudanar da ƙaramin bincike lamarin ya bayyana cewa wanda ya shirya taron da kuma wanda ke kiran kansa Satoshi suna fafatawa a wata shari'a mai sarƙaƙiya kan zargin zamba - mai alaƙa da iƙirarin zama Satoshi.
Ba dai fara da ƙafar dama ba, kuma abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa daga nan.
Mista Anderson ya gayyaci "Satoshi" ya fito kan dandali.
Wani mutum mai suna Stephen Mollah, wanda ya ke zaune shiru a gefe duk tsawon lokacin, ya tashi ya furta cewa: “Na zo nan don in faɗi cewa da gaske: Ni ne Satoshi Nakamoto kuma ni na ƙirƙiri Bitcoin akan fasahar Blockchain.”
A cikin sa'a guda da ta biyo bayan hakan, ƴan jarida sun kasance daga shiga halin nishaɗi zuwa na ɓacin rai saboda ya kasa ba da wata shaida kamar yadda ya yi alkawari domin gaskanta iƙirarin nasa.
Mista Mollah ya yi alƙawarin cewa zai buɗe, ya kuma yi mu'amala da Bitcoin na farko da aka ƙirƙira - wani abu da Satoshi ne kaɗai zai iya yi.
Amma ya kasa yin hakan.
Na tafi tare da wasu ƴan jarida cikin ɓacin rai, babu abin da muka tafi da shi illa shakku cewa wannan ma zai kasance wani labarin ƙanzon kurege a yunƙurin da ake yi na tabbatar da ko wane ne Satoshi.
An sake samun wani kuma
Jerin sunayen waɗanɗa ba a yi nasaran tababatar da cewa su ne Satoshi Nakamoto ba yana ta ƙara tsayi gaske.
A shekarar 2014, wani babban labari a mujallar Newsweek ya ce Dorian Nakamoto ne, wani Ba’amurke ɗan asalin ƙasar Japan da ke zaune a California, ya ƙirƙiro da Bitcoin.
Amma ya musanta hakan kuma daga baya an yi watsi da wannan iƙirarin.
Bayan shekara guda, ƴan jarida sun yi iƙirarin cewa Craig Wright wani masanin kwamfuta a Australia, shi ne Satoshi.
Daga farko ya musanta hakan, kafin daga baya kuma ya gaskata - amma ya kasa samar da wata shaidar da za ta tabbatar da hakan.
A lokacin bazara wata babbar kotu a birnin Landan ta yanke hukuncin cewa labarin nasa na boge ne.

Asalin hoton, Reuters
Hamshakin attajirin fasaha kuma mai kishin harkar kirifto, Elon Musk, shi ma ya musanta cewa shi ne ya ƙirƙiro da Bitcoin bayan wani tsohon ma'aikaci a ɗaya daga cikin kamfanoninsa, SpaceX, ya yi iƙirarin yiwuwar hakan.
Wannan ne ya kai mu ga tambayar cewa: wani muhimmanci sannin wanda ya ƙirƙiro kuɗin ya ke da shi?
Darajar masana'antar kirifto a halin yanzu na nufin ya fi kamfanin Google daraja. Kuma ba za a iya tunanin cewa wannan kamfanin fasahar da zai taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu ba tare da sanin wanda ya kafa ta ba, kuma ya mallaki kaso mai tsoka a kamfanin ba.
Wataƙila akwai kyakkyawan dalili da ya sanya Satoshi ya yi gum da bakinsa kan ko shi wanene. Saboda Bitcoin ɗin da ya mallaka yanzu ya kai darajar kimanin dala biliyan 69 kuma ba shakka za a sanyawa rayuwarsu da halayensa ido idan har an gano ko shi waye.
Peter Todd ya bayyana kwanan nan cewa sanya masa ido da aka yi ya sa ya fara fargaba kan tsaron lafiyarsa.
Mutane da yawa a duniyar kirifto suna jin daɗin cewa harb yazu an kasa gano wannan sirrin.
"Babu wanda ya san wanene Satoshi kuma wannan abu ne mai kyau," Adam Back, ɗaya daga cikin masu sarrafa fasahar Bitcoin (da kuma wani da ake ganin zai iya zama Satoshi) ya wallafa a shafinsa na X cikin kwanakin nan.
Natalie Brunel, wata mai gabatar da shirin rediyo kan Bitcoin ta na tunanin rashin sanin ko wanenne Satoshi abu ne mai matuƙar muhimmanci.
"Ta hanyar ɓoye ainihin ko waye shi, Satoshi ya tabbatar da cewa Bitcoin ba zai sami shugaba ko wani da za a alaƙanta da shi ba, wanda ra'ayinsa zai iya tasiri a kan yadda ake gudanar da hada-hada da kuɗin," in ji ta.
"Wannan yana bawa mutane damar amincewa da Bitcoin a matsayin tsari, maimakon alakanta shi da wani mutum ko kamfani."
Carol Alexander, farfesar hada-hadar kuɗi a Jami'ar Sussex - wadda ke ba da laccoci kan tarihin Bitcoin - ba ta da tabbas.
A ra'ayinta, hayaniyar da ake yi kan ko wanene Satoshi Nakamoto na ɗauke wa mutane hankali kan yadda za su binciki lamarin yiwuwar yadda kuɗaɗen kirifto za su yi babban tasiri kan yadda ake gudanar da al'amuran tattalin arziki a duniya.
Yayin da na bar Frontline Club na rasa abin da zan iya tabbatarwa daga wannan taron manema labaran, illa abu guda ɗaya.
A yanzu dai- kuma watakila har abada - za dai a ci gaba da neman ko wanene Satoshi.











