Man United na son Bellingham, Arsenal da Man City na zawarcin Brown

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Crystal Palace suna sa ido kan dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila, Jobe Bellingham, mai shekara 20. (Bild)
Arsenal da Manchester City da Real Madrid na daga cikin kungiyoyin da ke son dauko dan wasan bayan Jamus Nathaniel Brown mai shekaru 22 daga Eintracht Frankfurt, amma kulob din na Bundesliga ba zai saurari tayin ba har sai bazara mai zuwa. (Bild)
Chelsea ta tsananta neman dan wasan Crystal Palace Adam Wharton, ko da yake tana fuskantar turjiya daga Manchester United kan dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 21. (Teamtalk)
Dan wasan gaban Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 21, na shirin kin amincewa da sha'awar Arsenal da Chelsea da kuma Manchester United ke nunawa kansa, domin rattaba hannu kan wani sabon kwantiragi na dogon lokaci a Juventus. (Tuttosport)
Manchester United na sa ido kan dan wasan Jamus da Bayern Munich Aleksandar Pavlovic, mai shekara 21. (Football Insider)
Real Madrid na tunanin sayar da dan wasan Brazil Vinicius Junior, mai shekara 25, a bazara mai zuwa ga wata kungiya a Saudi Arabiya. (Sky Sports)
Watford na neman dan wasan gaba Emmanuel Dennis bayan da Nottingham Forest ta sako shi a watan Agusta, yayin da itama West Ham ke sha'awar dan wasan na Najeriya mai shekaru 27. (Mail)
An shaida wa Paris St-Germain cewa za ta biya fam miliyan 52 don siyan dan wasan tsakiyar Roma mai shekara 24, Manu Kone. (Corriere dello Sport)
Wakilin dan wasan gaban Barcelona Robert Lewandowski ya nuna shakku kan makomar tsohon dan kwallon Poland din mai shekaru 37 a kulob din, inda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa, kuma kungiyar bata nuna sha'awar sabunta kwantaraginsa ba. (Sports Spanish)










