Ƴan ƙwallo shida da suka haskaka a duniya cikin 2024

....

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Shekarar 2024 ta zo ƙarshe, kuma a harkar ƙwallon ƙafa ta duniya an fafata, har ma wasu sun kafa tarihi.

Argentina ta lashe gasar Copa America, Cote d'Ivore ta lashe Afcon, Sifaniya ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta Euro, yayin da ƙungiyoyi kamar Real Madrid suka yi nasara a manyan gasannin ƙungiyoyi na nahiyoyi.

Ga wasu daga cikin ƴan wasan da taurarinsu suka haska a cikin shekarar ta 2024.

Rodrigo Hernández - Spain/Manchester City

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Spain da Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Spain da Manchester City

Rodri shi ne ya lashe kyautar Ballon d'Or ta maza a 2024.

Babu tabbas ko akwai wata shekara da za ta yi wa Rodri daɗi fiye da 2024.

Ɗan asalin ƙasar Sifaniya, Rodri ya taka muhimmiyar rawa ga nasarar ƙungiyarsa ta Manchester City da kuma ƙasarsa Sifaniya, inda Spain ta lashe gasar Euro 2024 yayin da City ta lashe gasa Premier League.

Ɗan wasan mai shekara 28 a duniya, ya yi rashin nasara a wasa ɗaya ne kacal a kakar wasan da ta gabata a kulob ɗin da kuma ƙasarsa

Ya taimaka wa ƙasarsa Spain ta lashe gasar Euro 2024 a watan Yuli.

Ya lashe gasar Premier da Uefa Super Cup da kuma gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi tare da City.

Rodri shi ne ɗan wasa na farko a tarihin City da ya lashe kyautar Ballon d'Or.

City ta samu nasarar lashe gasar Premier ta Ingila karo na biyar a jere a kakar wasa ta 2023/2024, kuma ana kallon Rodri a matsayin wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen wannan nasara.

An haifi Rodrigo Hernández ne a watan Yunin shekara ta 1996. Duk da raunin da ya samu a farkon kakar 2024, ana wa Rodri kallon ɗan wasan tsakiya mafi ƙwazo a tarihi saboda ƙwarewarsa wajen rarraba ƙwallo a fili, da tsara wasa da kuma dagiya.

Vinicius Junior - Brazil/Real Madrid

Vinicius Junior

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Vinicius Junior

Gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na hukumar Fifa a 2024.

Vini mai shekara 24 da ƙungiyarsa ta Real Madrid sun ƙaurace wa bikin bayar da lambar yabo ta gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na Ballon d'Or a lokacin da ta bayyana ƙarara cewa ɗan wasan Manchester United, Rodri ne zai lashe kyautar.

Wannan lamari ya haifar da zazzafar muhawara a harkar wasanni a faɗin duniya.

Sai dai ana tunanin kyautar ta ɗan wasan Fifa da Vini ya lashe za ta yayyafa ruwa ga zuciyarsa.

Vinicius ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da ƙungiyarsa ta samu na lashe gasar La Liga ta 2023/2024.

Sai kuma kuma ta zakarun Turai (Champions League) a kakar wasar, inda ya zura ƙwallo 24 ya kuma taimaka aka zura guda 11.

Ya zo a matsayi na biyu kyautar Ballon d'Or.

Ɗan Brazil ɗin ya kasance a gaba-gaba wajen yaƙi da wariyar launin fata a harkar wasanni.

Jude Bellingham - Ingila/Real Madrid

Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jude Bellingham ya taka muhimmiyar rawa ga ungiya da kuma ƙasarsa a shekara ta 2024.

Ya zura ƙwallo biyu ga ƙasarsa Ingila a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Euro 2024.

Ya lashe ɗan wasa mafi ƙwazo a La Liga - bayan taimaka wa ƙungiyarsa ta Real Madrid lashe kofin - da lambar yabo ta matashin ɗan ƙwallo mafi ƙwazo a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League.

A watan Afrilu, Bellingham ya zura ƙwallon da ta bai wa Real Madrid nasara a karawar hamayya tsakaninta da Barcelona

Kasancewar ya zura ƙwallo 19 a raga, shi ne ɗan wasan Real Madrid da ya fi kowa zura ƙwallo a kakar ta bara, inda aka sanya shi a matsayi na uku cikin jerin waɗanda suka fi zura ƙwallo a raga a kakar da ta gabata.

Bellingham ya zo a matsayi na uku cikin jerin masu neman lashe kyautar Ballon d'Or ta 2024, a bayan ƴan wasa Rodri da Vinicius Jr.

Wannan ne karo na farko da sunan wani ɗan wasan ƙasar Ingila ya shiga cikin uku na farko a jerin na Ballon d'Or tun daga 2005 lokacin da Frank Lampard ya zo a irin wannan matsayi.

Lamine Yamal - Spain/Barcelona

Ɗan ƙwallon Sifaniya da Barcelona, Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan ƙwallon Sifaniya da Barcelona, Lamine Yamal

Ya zamo ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya buga gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai Euros yayin da yake da shekara 16 kacal da haihuwa.

Ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo a gasar ta Euro 2024 kuma shi ne ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya zura ƙwallo a raga a tarihin gasar, lokacin da ya zura ƙwallo a gasar da Sifaniya ta doke Faransa a matakin kusa da na ƙarshe.

Shi ne ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya yi wa ƙungiyar Barcelona wasa, lokacin yana ɗan shekara 15.

Masu bibiyar harkar ƙwallon ƙafa na da kyakkyawar fata a kan Lamine Yamal, wanda yanzu haka ake kwatanta tsarin wasansa da na shahararren ɗan ƙwallon duniya, Lionel Messi.

Duniya ta sanya ido domin ganin rawar da zai taka a wannan kakar wasanni ta 2024/2025 da kuma shekaru masu zuwa.

Phil Foden - Ingila/Manchester City

Phil Foden

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Phil Foden

Phil Foden, ɗan wasan Ingila da ƙungiyar Manchester City, shi ne ya lashe lambar yabo ta 'Professional Footballers Association' ta Birtaniya a kakar 2023/2024.

Foden, mai shekara 24 a duniya na daga cikin waɗanda suka taimaka wa Manchester City ta lashe gasar Firimiyar Ingila karo na huɗu a jere, inda ya zura ƙwallo 19 a raga tare da taimakawa aka zura guda takwas.

Haka nan kuma Foden shi ne ya lashe kyautar ɗan wasa mafi ƙwazo a gasar Premier ta 2023/2024 wanda ƙungiyar marubuta wasanni ta Birtaniya ke bayarawa.

Ademola Lookman - Najeriya/Atalanta

Ademola Lookman

Asalin hoton, X/CAFOnline

Gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka, CAF 2024.

Nasarar Lookman ta sanya Najeriya ta lashe wannan kyauta sau biyu a jere, bayan Victor Osimhen wanda ya lashe ta a 2023.

Lookman ya samu nasarar hakan ne bayan namijin ƙoƙarin da ya yi a kakar wasanni ta 2023/2024.

Ya taimaka wa ƙungiyarsa ta Atalanta sosai wajen lashe kofin Europa a karon farko a tarihi, inda ya zura ƙwallo uku rigis a ragar Bayer Leverkusen a wasan ƙarshe na gasar.

Wannan ya sanya Lookman ya zama na shida a cikin jerin ƴan wasan da suka taɓa zura ƙwallo uku rigis a wasan ƙarshe na wata gasar kulob-kulob ta nahiyar Turai tun daga shekara ta 1975.

Haka nan Lookman ya kasance cikin ƴan wasa mafiya nuna ƙazo a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka da aka buga a Ivory Coast a watan Fabarairun 2024.

Ya zura ƙwallo uku a raga a lokacin gasar, lamarin da ya sa Super Eagles ta ƙare a matsayin na uku.

Lookman, wanda tsohon ɗan wasan Everton da Fulham da kuma Leicester City ne shi ne ɗan Afirka ɗaya tilo da ya shiga cikin jerin ƴan wasan da suka yi takarar lashe kyautar Ballon d'Or ta 2024, inda ya ƙare a matsayi na 14.

Ya zuwa ƙarshen 2024, Lookman na ci gaba da wuta a ƙungiyarsa ta Atalanta, bayan zura ƙwallo takwas a raga a gasar Serie A.