Messi zai yi ritaya a Inter Miami amma bai tsayar da lokaci ba

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya yanke shawarar yin ritaya a Inter Miami - sai dai kawo yanzu bai tsara lokacin da zai bar taka leda ba.
Mai shekara 36, mai kyautar Ballon d'Or takwas, ya koma buga gasar tamaula ta Amurka a kakar 2022/23, bayan da kwantiraginsa ya kare a Paris St-Germain.
Kyaftin din tawagar Argentina ya nuna kansa a Barcelona, inda ya lashe Champions League hudu da La Liga 10 a kungiyar da ke Sifaniya.
Wanda ya dauki kofin duniya a 2022 da Argentina a Qatar a 2022, yana da sauran kunshin yarjejeniya da za ta kare a Inter Miami zuwa karshen kakar 2025.
Kawo yanzu Messi yana wasa kan ganiya ba za ka ce zai yi ritaya kwanan nan ba, wanda ya ci kwallo 12 da bayar da 13 aka zura a raga a wasa 12 a gasar ta Amurka.
Yana kuma sa ran zai wakilci Argentina a Copa America da za a buga a Amurka a bana, wadda ita take da kofin da ta dauka a 2021 a Brazil.
Kenan za a yi karawar Copa America a Amurka, inda Messi ya kira a gidansa a lokacin da ya koma Inter Miami da taka leda.







