Wane ne Anura Kumara Dissanayake, sabon shugaban Sri Lanka?

..

Asalin hoton, Sri Lanka President Media via Reuters

    • Marubuci, Joel Guinto
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Marubuci, Ayeshea Perera
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

An zaɓi Anura Kumara Dissanayake mai ra'ayin kawo sauyi a matsayin sabon shugaban ƙasar Sri Lanka bayan da ya samu nasarar lashe zaɓen ƙasar mai cike da basuka a kanta tun a zaɓenta na farko tun bayan karyewar tattalin arziƙinta a 2022.

Ɗansiyasar mai shekaru 55 ya kayar da abokin takararsa Sajith Premadasa wanda ya zo na biyu da kuma shugaban ƙasar mai barin gado Ranil Wikremesinghe wanda shi ne ya zo na uku a zaɓen.

Zaɓen Dissanayake na da mamaki kasancewar a 2019 ya samu kaso uku ne kacal na kuri'un da aka kaɗa amma yanzu ƙarƙashin jam'iyyar haɗaka ta NPP ya samu goyon bayan ɗimbin magoya baya saboda manufar ƙyamar rashawa da kuma ɗaukar tsare-tsare da za su inganta rayuwar talaka.

Yanzu haka zai gaji gwamnatin da ke ƙoƙarin farfaɗowa daga rikicin karyewar tattalin arziƙi da ta samu kanta a ciki.

Wane ne Dissanayake?

An haifi Dissanayake ranar 24 ga watan Nuwamban 968 a Galewela, wani gari mai mutane masu al'ada da addini daban-daban da ke tsakiyar Sri Lanka.

Dissanayake ya taso a iyalai masu matsakaicin arziƙi sannan makarantun gwamnati ya yi, inda ya samu digiri a fannin Physics.

Daga 1987 zuwa 1989, jam'iyyar Janatha Vimukti Peramuna (JVP), jam'iyya ce ta ƴan gurguzu wanda Dissanayake zai kasance mamba ta jagoranci bore ga gwamnatin Sri Lanka.

A wannan lokacin an samu tarzoma da bore a tsakanin matasa yaƴan talakawa da matsakaitan masu arziƙi inda abin ya shafi ƴan adawa da fararen hula wani abu da ya janyo rasa dubban rayuka.

Dissanayake, wanda aka zaɓa a matsayin ɗan kwamitin jam'iyyar ta JVP a 1997 kuma ya zamo jagoranta a 2008, ya nemi afuwa dangane da halayyar da ƴan ƙungiyar suka nuna a lokacin tarzomar.

..

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Magoya bayan Dissanayake sun hau titunan suna murnar samun nasararsa ranar Lahadi

Alaƙarsa da Talakawa

Ɗaya daga cikin manufofin Mista Dissanayake shi ne ganin rayuwar talakawan ƙasar ta inganta.

Mista Dissanayake ya sha alwashin rushe majalisar dokokin ƙasar wadda ya ce ba ta tare da talakawa.

"Za mu rushe majalisar dokokin...babu amfanin tafiya tare da zauren majalisar da ba ya tare da talakawa sannan ba ya yin abin suke so." In ji mista Dissanayake a wata hira da BBC.

Kimanin kaso 76 na al'ummar ƙasar Sri Lanka miliya 17.1 suka fita domin kaɗa ƙuri'a a ranar Asabar.

..

Asalin hoton, EPA