Abu biyar da za su ɗauki hankalin majalisar Amurka da ta fara aiki a 2025

    • Marubuci, Rachel Looker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
  • Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da duniya ta shiga sabuwar shekara, sabuwar majalisar dokokin Amurka na zama a zauren Capitol a zamanta na farko.

Juma'a ce ranar farko ta fara zaman majalisar ta 119, inda jam'iyyar Republican take da rinjaye a zaurukan majalisun guda biyu ta wakilai da ta dattawa.

Hakan na nuna gagarumar nasarar jam'iyyar a zaurukan biyu yayin da sabon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar ke shirin komawa fadar White House nan gaba cikin wannan wata.

'Yan jam'iyyar Republican sun zaƙu a fara gudanar da harkokin mulki, to amma da alama abin ba zai zo musu da sauƙi ba, domin kuwa rinjayen da suke da shi a duka zaurukan majalisun biyu ba zai sa su samu duk abin da suke so cikin sauƙi ba.

Gwajin haɗin kan jam'iyyar da za a yi na farko, shi ne zaɓen jagororin majalisun da aka yi a yau Juma'a.

Ga wasu abubuwa biyar da za a iya lura da su a yayin da majalisar take soma zamanta.

1. Rinjayen Republican, amma maras yawa

Jam'iyyar Republican na da rinjaye a majalisar, amma ba mai yawa ba.

Kuma za a fara gwajin tasirin rinjayen da zarar an fara zaman majalisar.

Majalisar ba za ta ci gaba da gudanar da zamanta ko yin dokoki ba har sai ta zaɓi kakaki - wato shugaban majalisar.

Bayan samun goyon bayan Trump, kakakin majalisar na yanzu, Mike Johnson ya samu nasarar sake zama shugaban majalisar, bayan da a zagayen farko na ƙuri'ar ya fuskanci turjiya daga wasu 'yan majalisar Republican uku.

A shekarar 2023, sai da aka kaɗa ƙuri'ar har sau 15 a cikin kwana huɗu, kafin Kevin McCarthy ya samu nasarar zama kakakin majalisar.

Republican na da tazarar kujeru biyar a rinjayen da take da shi a majalisar a lokacin da aka bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen 2024.

To sai dai tazarar ka iya sauyawa sakamakon yadda Trump ya bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar muƙami a gwamnatinsa.

2. Amincewa da naɗe-naɗen gwamnati

A zauren majalisar dattawan ƙasar, 'yan majalisar sun zaɓi shugaban masu rinjaye, Sanata John Thune daga South Dakota na jam'iyyar Repblican.

Hakan na nufin sanatocin ka iya fara ayyukansu a ranar Juma'a, to amma suna iya cin karo da wasu ƙalubale.

Majalisar dattawan na shirin tantance tare da amincewa da naɗe-naɗe da dama daga sabuwar gwamnatin Trump, yayin da tantance wasu zai ɗauki hankalin mutane.

Daga cikin waɗanda tantance su zai ja hankali har da sakataren tsaro, Pete Hegseth, wanda ke fuskantar zarge-zargen cin zarafin lalata tun daga 2017, zarge-zargen da ya sha musantawa.

Haka ma akwai sakataren ayyukan jama'a Robert F Kennedy Jr, wanda ke da tarihin yaɗa labaran da ba na gaskiya ba.

An yi ta ganin mutane da Trump ɗin ya bai wa muƙamai na karakaina a harabar majalisar a watan da ya gabata domin kamun ƙafa ga wasu sanatocin, to amma hakan ba zai hana su fuskantar tambayoyi a lokacin da suka halarci majalisar domin tattancewar ba.

Haka ma majalisar na shirin gaggauta tantance naɗin jagororin tsaro, musamman bayan harin ta'addanci da aka kai New Orleans, inda mutum 14 suka mutu, da kuma samun wata fashewa a wata mota a wajen hotel ɗin Trump da ke Las Vegas.

"Dole ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin tawagar da za ta jagorancin tsaron ƙasarmu cikin gaggawa, saboda rayuwar mutane ta dogara da tsaro,'' kamar yadda Sanata John Barasso ya wallafa a shafinsa na X.

3. Dokar haraji

Wani abu da zai iya zama babba cikin ƙudurorin majalisar shi ne batun ƙudurin rage haraji da ayyuka ta 2017, da za ta ƙare a 2025.

Dokar - wadda aka yi a 2017 lokacin da Republican ke da rinjaye a majalisun Wakilai da na dattawa - ta ƙunshi sake fasalin harajin da rage yawan haraji da masu biyan haraji.

Ta kasance dokar da ta rage haraji mafi girma a cikin gomman shekaru, musamman lokacin da kasuwanni da attajirai, wadda 'yan jam'iyyar Democrats ke ta kiraye-kirayen janye shi.

Trump ya yi yaƙin neman zaɓensa kan tattalin arziki - inda ya alƙawarta tsawaita dokar rage haraji, da ma janye shi kan wasu abubuwa, kamar biyan kuɗin aikin ƙarin lokaci da ka fi sani da 'overtime'.

4. Nasarar muradun jam'iyyar

Ana kuma sa ran ganin dokoki kan wasu batutuwan da jam'iyyar Republican ta sanya a gaba, kama daga batutuwan da suka shafi rage 'yan cirani zuwa rage wasu dokokin gwamnati.

Akwai ƙuiurin rage tallafin soji ga Ukraine, da sanya sabbin haraje-haraje, da kuma rage kashe kuɗi a makamashin da ba ya gurɓata muhalli da ƙarfafa tsaron kan iyakoki.

A cikin jawabin da ya yi wa taron manema labarai cikin watan Nuwamba, Johnson ya zayyano manufofin Republican na rage hauhawar farashim da tsaron kan iyakoki da maido da mamayar Amurka a fannin makamashin da zartar da ƙudirin 'ilimi kyauta'.

Haka ma Trump ya buƙaci 'yan majalisar sun ƙara ko ma su dakatar da taƙaita bashin da gwamnati ke karɓa.

Akwai yiwuwar duƙa muradun jam'iyyar ka iya tsallakewa a majalisar, musamman ƙudirin haraji da kashe-kashen kuɗin gwamnati da kuma taƙaita bashi.

5. Tasirin sabbin fuskokin gwamnati

Ƙarshen Majalisar da ta gabata an ga irin tasirin da Trump da abokansa ke da shi kan tsare-tsaren majalisar.

Hamshakin attajirin nan, Elon Musk, wanda Trump ya naɗa a matsayin mai bai wa gwamnatinsa shawara kan rage kashe kuɗaɗen gwamnati, ya wallafa saƙonni masu yawa a shafinsa na X, don yin Allah wadai da yarjejeniyar kashe kuɗi da Johnson ya jagoranta tare da 'yan jam'iyyar Democrat don hana rufewar gwamnati.

Dukansu, Trump da Musk sun yi barazanar janye kuɗaɗensu da goyon bayansu ga 'yan Republican da suka goyi bayan ƙudirin kashe kuɗaɗe, lamarin da ya sa mutane suka yi ta aza ayar tambayar ko wane irin tasiri mutanen za su yi kan ayyukan majalisar.

Musk da ɗan kasuwar magunguna, Vivek Ramaswamy na iya samun ƙarin damarmaki. Mutanen biyu za su kasance tare wajen jagorancin sabon kwamitin shawarwari da aka kafa wanda ke mai da hankali kan tsara ka'idojin kashe kuɗi.

Yayin da Republican ke waɗannan tsare-tsare, a gefe guda 'yan jam'iyyar Democrats na sake haɗa kansu, tare da fatan ƙwace rinjayen majalisar wakilai a zaɓen rabin wa'adi da za a yi a 2026.

Wani mataki da masana ke ganin zai iya yi wa 'yan majalisar masu sassaucin ra'ayi tasiri wajen cimma muradinsu.