Matar da ke bayar da gudumawar ruwan nono ga masu buƙata

Chelimo Njoroge ta fara bayar da gudumawar ruwan nononta da ya saura daga abinda jaririnta ke buƙata, wanda take tallatawa a shafin Tiktot mai mabiya 16,000
Bayanan hoto, Chelimo Njoroge ta fara bayar da gudumawar ruwan nononta da ya saura daga abinda jaririnta ke buƙata, wanda take tallatawa a shafin Tiktot mai mabiya 16,000
    • Marubuci, Saida Swaleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
  • Lokacin karatu: Minti 5

Chelimo Njoroge kan tuna ranar da ta cika firjinta da ruwan nono da ta tatsa daga jikinta.

"Sai da na cika firjina guda biyu, sannan na fara amfani da na ƴar'uwata,'' kamar yadda ta bayyana cikin dariya.

Matar mai shekara 36, ƴar asalin birnin Nairobi, mai ƴaƴa biyu, ta fahimci tana da yalwar ruwan nono.

Ko da ta shayar da jaririnta, za ta iya samar da rarar litoci da dama na ruwan nonon a kowane mako.

Don haka a maimakon ta bar shi kawai a jikinta ba tare an amfana da shi ba, sai ta fara tatsarsa domin bayar da gudumawa ga masu buƙata.

Bayan shafe kusan shekara guda tana wannan taimakon, Chelimo ta tallafa wa iyaye mata da dama, yayin da take bayar da ruwan nonon nata ga wasu mata takwas a garinsu, ciki har da ƙawayenta da suka jima tare da kuma waɗanda suka tuntuɓe ta bayan fara ganin bidiyoyinta a shafukan yanar gizo.

"A shafukan TikTok na fara ganin bidiyoyinta na yadda take bayar da gudumawar ruwan nono, abin ya ba ni mamaki,'' in ji Maryann Kibinda, ɗaya daga cikin matan da ke karɓar ruwan nonon Chelimo.

"Sai kawai na yi mata magana ta shafin, bayan mun gaisa na ce mata ina buƙatar ruwan nono, da haka muka fara."

A ranar ƙarshe da ta raba ruwon nonon, Chelimo ta bayar da lita 14.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da fari shayarwar Chelimo ta zo ta tangarɗa, lamarin da ya sa ta fara shan magungunan da za su samar da ruwan nono.

A lokacin da nonon ya fara zuwa kuma, sai ya zo fiye da yadda aka saba gani a sauran mata masu shayarwa.

"A lokacin da yake kan ganiyar zuwan sa, zan iya shayar da jarirai 50 da ke ɗakin kula da jarirai,'' in ji ta.

Daga nan ta fara wallafa bidiyoyi a shafukanta na TikTok, tana mai bayyana irin matsalolin da mata ke fuskanta wajen shayar da jariransu, sannan ta riƙa bayar da dabarun adana ruwan nono cikin tsafta.

Da fari bidiyoyinta ba su fiye samu masu kallo ba, to amma daga baya shafinta ya samu karɓuwa sosai inda a yanzu haka shafin nata ke da mabiya 16,000.

Wasu daga cikin mabiyan nata irin ta ne masu bayar da gudumawar ruwan nono, yayin da wasu kuma iyaye ne masu buƙatar ruwan nono.

"Akwai iyaye da dama da ke son bayar da gudumawar ruwan nono. Amma akwai da dama da ke buƙatar tallafin ruwan nonon,'' in ji ta.

A hukumance Kenya na da rumbun ajiyar ruwan nono da ke ɗakin haihuwa na asibitin Pumwani da ke birnin Nairobi.

To amma ana karɓar ruwan nono ne kaɗai daga iyaye matan da ke kwance a asibitin waɗanda ba sa iya shayar da jariransu, kuma ana amfani da ruwan nonon ne kaɗai ga jariran da ke kwance a asibitin.

Hakan ya sa mata irin su Chelimo ba sa iya bayar da gudumawar ruwan nonon a hukumance.

''Ba mu da wadatattun wuraren ajiyar ruwan nonon da za mu iya ajiye nonon da mata da wasu ke son bayarwa,'' in ji ta.

Nairobi na shirin faɗaɗa tare da samar ƙarin rumbunan ajiyar ruwan nono domin bayar da dama ga iyaye da son bayar da gudunmawar.
Bayanan hoto, Nairobi na shirin faɗaɗa tare da samar ƙarin rumbunan ajiyar ruwan nono domin bayar da dama ga iyaye da son bayar da gudunmawar.

Rumbun ajiyar ruwan nono na ƙasa

Shugabar cibiyar samar da abinci mai gina jiki ta yankin Nairobi, Esther Kwamboka Mogusu, ta ce manufar shirin shi ne faɗaɗa girman rumbun ajiye ruwan nono na asibitin Pumwani domin inganta shi.

"Za mu sake gina wasu rumbunan biyu a birnin Nairobi domin mu taimaka wa jajariran da ke buƙatar ruwan nonon waɗanda ba a cikin asibitn suke ba,'' in ji ta.

Ma'aikatar lafiyar ƙasar tare da haɗin gwiwar hukumar yankin Nairobi da ƙungiyar PATH sun ce suna ƙoƙarin yadda za su inganta samun mata masu bayar da gudumawar ruwan nono a Kenya.

''Shirin zai ɗauki shirin samar da rumbunan ajiyar ruwan nono da muhimmanci, domin tallafa wa jarirai'', in ji Veronica Kirogo Daraktar sashen kula da abinci mai gina jiki a hukumar lafiya ta Kenya.

Wata ungozoma kuma ƙwararriya a fannin shayarwa, Mary Mathenge ta amince cewa akwai giɓi a buƙatar da ruwan nono.

Ta shafe tsawon shekara 40 tana aiki da masu shayarwa , ta kuma ce ta yi imanin cewa Kenya na buƙatar shirin samar da rumbunan ajiyar ruwan nono cikin tsafta.

"Shi jariri zai iya rayuwa da ruwan nonon kowace mace,'' in ji ta.

''To amma duk abin da ke yaɗuwa ta hanyar jini, zai yadu ta hanyar shayarwa, don haka dole a yi wa kowace mace gwaji''.

''Akwai cikakken tsarin da aka tanada na tantance matan da za su bayar da gudumawar ruwan nono da yadda za a adana shi, ta yadda jarirai masu yawa za su amfana.''

A duk lokacin da uwa ba za ta iya shayar da jaririnta ba, Hukumar Lafiya ta Duniya na bayar da shawarar amfani da ruwan nonon ɗan'adama amatsayin hanya mafi inganci, har zuwa lokacin da na uwar zai samu.
Bayanan hoto, A duk lokacin da uwa ba za ta iya shayar da jaririnta ba, Hukumar Lafiya ta Duniya na bayar da shawarar amfani da ruwan nonon ɗan'adama amatsayin hanya mafi inganci, har zuwa lokacin da na uwar zai samu.

Chelimo ta ce takan yi amfani da rarar ruwan nononta ta hanyoyi da dama, wajen tallafa wa jariran wasu.

Amma kaso mafi yawa na tafiya ga iyalan da ke fama da shayar da jariransu saboda wasu dalilai.

Masu amfani da shafukan intanet da dama na yaba da kan wannan ƙoƙari da take yi inda har suka riƙa yi mata laƙabi da ''Zinariyar ruwan nono''.

Amma Chelimo ta ce ba ita kaɗai ce ke wannan sadaukarwa ba.

''Ba Chelimo ce kaɗai wannan aikin sadaukarwa ba," in ji ta.

"Akwai uwaye da dama irina."

Yayin da take rufe firinjinta a karo na ƙarshe, ta ce tana fatan batun bayar da gudumawar ruwan nono zai ci gaba a Kenya kuma mata da yawa za su samu damar bayar da tasu gudumawa a fannin domin taimaka wa masu buƙata.