'An fara bai wa jaririyar da nake reno fura tun tana wata ɗaya da haihuwa'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
'An fara bai wa jaririyar da nake reno fura tun tana wata ɗaya da haihuwa'

Wata uwar marainiya da ke goyon jarirai guda biyu a jihar Katsina, ta bayyana takaicin cewa ba ta samun abinci mai gina jiki da zai ba ta damar wadata jariranta a wannan hali na matsin rayuwa.

Murja Abdulsalam ta ce: "Ina jin ciwo na ga kowanne ɗa a ƙoshe amma marainiyar da nake shayarwa tana ta ramewa" .

Uwar marainiyar na wannan bayani ne a wani asibitin kula da yara masu fama da tamowa a Katsina.

A cewarta, takan bai wa jaririyarta abinci saboda ta bari a bai wa marainiyar da take riƙo nono.

Murja ta ce ta karɓi marainiyar ne kwana biyu kafin mutuwar babarta, wadda ta yi fama da rashin lafiya, ta yadda har ba ta iya shayar da ita, sai dai kawai a ba ta fura.

Ta ce "watanta ɗaya (a duniya) sai suka ga ɗiya ta bushe. Sai suka ɗauki fura aka fara ba ta. Sai muka je dubiya, na ce ku yanzu haka ake ba ta fura?"

"Babar (wadda ta rasu daga bisani) ta ce: to Murja kin ga dai na duba cikin dangi, ba wanda zai iya ba ta nono, ke kaɗai ce Allah ya ba ni, kuma ko ke ma sai in mijinki ya yarda."

Alƙaluma daga hukumomin lafiya sun nuna cewa ƙananan yara sama da miliyan huɗu ne ke fama da rashin abinci mai gina jiki bana a arewacin Najeriya.