Shin ɗiga wa jariri nono a kunne yana sa wa ya daina kuka?
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Al'umma da dama a sassa daban-daban na nahiyar Afirka sun yarda da wasu camfe-camfe a kan yara kanana da kuma sauran abubuwa da suka shafi rayuwarsu.
Akasarin wadannan camfe-camfen ba su da tushe a kimiyyance.
A ci gaba da jerin bidiyo da BBC ke kawo a kan wasu camfe-camfe da iyaye mata ke yi ga jarirai, wannan bidiyon ya duba camfin diga wa jariri nono a kunne, kuma likitocin yara kamar su Dakta Naja'atu Hamza ta ce 'ba dadai ba ne'.