Ku San Malamanku Tare da Sheikh Muhammad Shugaba Abdurrahman

Sheikh Muhammad Shugaba Abdurrahman
Lokacin karatu: Minti 1

Cikin Shirin namu na wannan makon mun tattauna da Sheikh Muhammad Shugaba Abdurrahman

An haifi Shehin malamin a birnin Maiduguri gidan wani babban ɗan siyasa mai suna Shugaba Darman.

Ya kammala karatunsa na furamare a shekarar 1981, kafin nan ya fara ne da karatu a Islamiyyar unguwar Hausari.

Ya tafi makarantar sakandire kafin ya kammala, ya kuma samu shaidar diploma, sannan kuma ya kammala digirinsa a shekarar 1998, sannan ya fara karatun digiri na biyu a 2013, inda ya kammala a 2020, yayin da yanzu haka yake digirinsa na uku duka a fannin ilimin addinin musulunci.

Malamin ya ce babban malamin da ya tasirantu da shi, shi ne Sheikh Muhammad Abba Aji, da kuma Sheikh Muhammad Mustapha, wanda a yanzu suke tafsiri tare.

Malamin ya ce ya fi ƙwarewa a ilimin karatun Qur'ani da hadisai.

Ma'aikata:

  • Ɗaukar bidiyo: Fatawul Mohammed