Yahudawa na ƙwace filayen Falasɗinawa da sunan yaƙi

- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
- Marubuci, Toby Luckhurst
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, In Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 7
Rayuwa na ci gaba da gudana kamar yadda take tsawon ɗaruruwan shekaru a ƙauyen Battir na Falasɗinawa, inda ƙoramu ke gudana, a filaye da kwazazzabu masu ban sha'awa na tun zamanin da.
Wannan ƙauye na Battir, wanda ya yi fice wajen itatuwa na inabi da lemo, yana daga cikin wuraren da hukumar kula da ilimi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Unesco, ta ware a matsayin na musamman.
To amma kuma a yanzu ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da suka fi ɗaukar hankali a wuraren da Yahudawa ƴan kama-wuri zauna ke ƙwace wa Falasɗinawa a Gaɓar Yamma.
Yanzu Isra'ila ta amince da kafa sababbin unguwanni na Yahudawa, inda take ƙwace filaye na Falasɗinawa domin gina gidaje ga Yahudawa. Kuma an kakkafa sababbin unguwanni wasu ma ba ma tare da izinin hukumar Isra'ila ba.
“Suna sace mana filaye su gina rayuwarsu su jefa mu cikin bala'i,” in ji Ghassan Olyan, wani Bafalasɗine da filinsa na daga cikin waɗanda aka ƙwace.
Unesco ta ce ta damu a kan abin da ke faruwa a Battir, to amma ba a wannan ƙauyen Falasɗinawan ba ne kaɗai abin ke faruwa akwai wasu da dama da Yahudawan ke ƙwacewa.
A ƙarƙashin dokokin duniya dukkanin matsugunan Yahudawa na kama wuri-zauna haramtattu ne, kodayake Isra'ila ba ta yadda da hakan ba.
Mista Olyan ya ce: “Ba su damu da dokokin duniya ba, ko dokokin ƙasa, kai hatta dokar Allah ma ba su damu da ita ba.”

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A makon da ya gabata ministan leƙen asiri na cikin gida na Isra'il Ronen Bar, ya rubuta wa ministocin gwamnatinsu inda yake gargaɗin su cewa Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a Gaɓar Yamma na aikata ta'addanci a kan Falasɗinawa, inda suke haifar da gagarumar illa ga ƙasar.
Tun bayan da aka fara yaƙin Gaza, ana ta samun ƙaruwar matsugunan Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yamma.
Masu tsattsauran ra'ayi a gwamnatin Isra'ila na bugun ƙirji da cewa wannan sauyin zai hana samar da ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta.
Ana ganin masu wannan manufa suna son tsawaita yaƙin domin cimma wannan buri nasu.
Yonatan Mizrahi na ƙungiyar wanzar da zaman lafiya ta Peace Now, wadda ƙungiya ce ta Yahudawa da ke sa ido kan faɗaɗar matsugunan Yahudawa 'yan kama-wuri zauna, ya ce Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a Gaɓar Yamma na ƙara ta'azzara zaman tankiya da ake ciki a yankin inda suke ƙara sa da wuya a shawo kan rikicin na Isra'ila da Falasɗinawa.
A tsakanin 7 ga watan Oktoba da Agusta na 2024, an kashe Falasɗinawa 589 a Gaɓar Yamma - aƙalla 570 sojojin Isra'ila ne suka kashe su aƙalla 11 kuma ƴan kama-wuri-zauna ne suka kashe su, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.
A tsakanin wannan lokaci su ma Falasɗinawa sun kashe ƴan kama-wuri-zauna da jami'an tsaro na Isra'ila tara.
A watan da ya gabata an kashe wani Bafalasɗine mai shekara 22, lokacin da wani gungun 'yan kama-wuri-zauna ya yi kutse a ƙauyen Jit, abin da ya janyo suka a duniya.
Jami'an tsaron Isra'ila sun kama mutum huɗu kuma sun bayyanna lamarin a matayin tsabagen ta'addanci.
To amma bincike a kan irin waɗannan hare-hare ya nuna cewa kusan hukumomin Isra'ila ba sa hukunci a kai.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Isra'ila ta Yesh Din ta gano cewa tsakanin 2005 zuwa 2023, kashi uku cikin ɗari ne kawai na irin waɗannan laifuka aka hukunta a kotu.
'Abu ne mai tsananin haɗari'
Yahudawa baƙi na zaune ne a garuruwan Yahudawa kawai da aka kafa a sassan Gaɓar Yamma.
Matsugunai da dama suna da goyon bayan gwamnatin Isra'ila - wasu kuwa waɗanda ɗakuna ne na tafi-da-gidanka ko kwantainoni, haramtattu ne hatta a ƙarƙashin dokokin Isra'ila. To amma Yahudawa masu tsattsaura'an ra'ayi na ci gaba da gina matsugunan da nufin ƙwace ƙarin filaye.
A watan Yuli lokacin da a karon farko babbar kotun majalisar ɗinkin duniya ta ayyana mamayen na Isra'ila a Gaɓar Yamma ciki har da gabashin birnin Ƙudus cewa haramtacce ne, ta umarci ƙasar ta dakatar da gina dukkanin waɗannan matsugunai ta kuma janye daga cikinsu.
Ƙawayen Isra'ila na yammacin duniya sun nanata cewa waɗannan matsugunai cikas ne ga samar da zaman lafiya. To amma gwamnatin Isra'ila ta yi watsi da hakan da cewa, ''Yahudawa ba masu mamaye ba ne a ƙasarsu.''
Yanzu dai ana fargabar cewa Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun himmatu wajen ganin sun kafa unguwannin 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yamma, ta yadda ba za a iya kawar da su ba a nan gaba.
Suna kuma yin hakan ne tare da taimakon gwamnatin masu tsattsauran ra'ayi da ba a taɓa samu ba a tarihin Isra'ila.
Masu wannan manufa na ci gaba da mamayar yankunan Falasɗinawa a Gaɓar Yamma har ma suna fitowa fili suna maganar cewa idan an gama yaƙi za su kama wurare a Gaza su zauna.
Yanzu dai baƙin Yahudawa - 'yan kama-wuri-zauna na nan a cikin gwamnatin Isra'ila - a manyan ma'aikatu.
A daidai lokacin da shugabannin duniya ke nuna kin amincewa da mamayen na Isra'ila, tare da fatan ganin an kai ga kafa ƙasashe biyu - shirin zaman lafiya da aka dade ana fatan gani, masu kishin addinin Yahudawa, waɗanda suka yi amanna dukkanin ƙasar tasu ce sun lashi takobin ganin ba a kafa ƙasar Falasɗinu ba.
Wannan ne ma ya sa wasu masu sharhi suke ganin wasu daga cikin 'yan siyasar Isra'ila ba su son a cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta.
Saboda ta haka ne Isra'ila za ta ci gaba da mamaye yankunan na Falasɗinawa.

Mun kama hanya a mota zuwa ƙauyen al-Qanoub tare da Ibrahim Shalalda, mai shekara 50, da baffansa mai shekara 80, Mohammed, waɗanda suka gaya mana cewa Yahudawa 'yan kama wuri-zaun sun lalata masu gidajensu a watan Nuwamba.
Lokacin da muka nufi wajen sai wani Bayahude mai tsattsauran ra'ayi ya sa motarsa ya tare mana hanya.
Nan da nan kuma sai ga jami'an tsaron Isra'ila, inda suka tsayar da mu domin bincike.
Jami'an sun tilasata wa Falasɗinawan fita daga motar suka bincike su. Bayan sa'a biyu sai sojojin na Isra'ila suka kori masu kama-wuri-zaunan, suka bar motar BBC ta bar wajen.

Isra'ila ta fara kafa matsugunai ne a Gaɓar Yamma tun bayan da ta ƙwace yankin daga Jordan sama da shekaru 50 da duka wuce. Tun daga nan kuma duk gwamnatin Isra'ilar da ta biyo baya tana barin a yi ta faɗaɗa matsugunan Yahudawa.
A yau an yi ƙiyasin akwai Falasɗinawa miliyan uku a yankin - bayan gabashin Birnin ƙudus da Isra'ila ta kama - inda ake da kusan Yahudawa rabin miliyan a matsugunai sama da 130.
Ministan kuɗi na Isra'ila, Bezalel Yoel Smotrich mai tsattsauran ra'ayin kishin Yahudawa, ya yi alƙawarin nunka wannan yawan - zuwa Yahudawa miliyan ɗaya.
‘Burin rayuwata’
Yahudawa masu kishin ƙasa da addininsu sun kasance a gefe-gefen siyasar Isra'ila tsawon gomman shekaru.
To amma sannu a hanakil aƙidarsu yanzu ta yaɗu a tsakanin al'ummar Isra'ila.
A zaɓen 2022, jam'iyyu masu ra'ayinsu sun samu kujeru 13 daga cikin 120 a majalisar dokokin Isra'ila - kuma wannan ya sa suka zama masu ikon fadi-a-ji a gwamnatin Firaminista Netanyahu.
A lokacin yaƙi, Bezalel Smotrich da ɗan uwansa mi tsattsauran ra'ayi, Itamar Ben-Gvir, wanda yanzu shi ne ministan tsaro na cikin gida, sun riƙa furta kalamai na raba kan jama'a tare da harzuƙa ƙawayen Isra'ila na ƙasashen yamma.
Bayan da sojojin Isra'ila suka kama wani sojin ƙasar na jiran ko-ta-kwana bisa laifin cin zarafi na lalata da ya yi wa wani fursuna Bafalasɗine, Ben Gavir sai ya fito yake cewa abin takaici ne da kunya a ce Isra'ila ta tsare fitattun gwarazanta.
Sannan a watan nan kuma, Mr Smotrich ya nuna cewa, “abu ne da ya dace a jefa mutanen Gaza cikin yunwa.''
To amma a Gaɓar Yamma ne da kuma Gaza masu tsattsauran ra'ayin suke so su kawo sauyi na dindindin. “Wannan rukuni ne na Yahudawa da ke adawa da duk wani shiri na sasantawa da Falasɗinawa ko Larabawa da ke maƙwabtaka da Isra'ila,” in ji Anshel Pfeffer, tsohon ɗanjaridar mujallar The Economist.
Masu tsattsauran ra'ayin na ganin yaƙin Gaza a matsayin wata dama ta cimma wannan buri nasu.
Mr Smotrich ya yi kira ga Falasɗinawa da su fice su ba Yahudawa waje - waɗanda ya ce za su raya yankin - za su mayar da hamada ta zama dausayi.
Duk da cewa Mr Netanyahu ya kawar da yiwuwar mayar da matsugunan Yahudawa a Gaza, to amma yana ɗanfare da jam'iyyun masu tsattsauran ra'ayi wadanda suke barzanar ruguza gwamnatinsa idan ya ƙulla yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta sakaka domin sakin Yahudawa da Hamas ke riƙe da su.
Duk da cewa ƙila 'yan Isra'ila kaɗan ne ke da aƙidar masu tsattsauran ra'ayin. To amma tana taimakawa wajen tsawaita yaƙin tare kuma da sauya fasalin Gaɓar Yamma - inda take haddasa illa ta tsawon lokaci ga shirin zamn lafiya.






