Ko sake ɓullar cutar shan'inna zai karya gwiwar kawo ƙarshenta a duniya?

Hoton yaro ana ɗiga ma sa rigakafin cutar polio

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cikin shekaru 10 sama da yara biliyan goma aka yi wa digon rigakafin cutar a duniya.
    • Marubuci, Swaminathan Natarajan and Zarghuna Kargar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 7

Hukumar lafiya ta duniya WHO na da ƙwarin gwiwar za a kakkabe cutar shan'inna ko Polio daga ban kasa zuwa shekarar 2025, duk da sake bullarta a cikin shekarar nan.

A shekarar 1988 aka kaddamar da shirin shafe cutar shan'inna a duniya, a lokacin da kwayar cutar ta kama mutane 350,000 a ƙasashe 125.

A halin da ake ciki ƙasashe biyu ne kaɗai aka samun rahoton samun cutar: a shekarar da ta gaba ne aka samu rahoton mutane 39 sun kamu da cutar a Afghanistan, sai kuma Pakistan mai mutum 24.

Shin sake bullar cutar zai karya gwiwar fatan kakkabe polio a doron kasa?

Jaleel Ahmad rike da dan shi Jawad, su na magana da wani mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jaleel Ahmad rike da dan shi Jawad, ba shi da tabbacin ƙalubalen da dan shi zai fuskanta nan gaba

Iyaye matasa

Watan Jawad 30 da haihuwai, iyayensa 'yan asalin arewa maso gabashin birnin Quetta a kasar Pakistan ne. Ya na daga cikin wadanda suka kamu da ƙwayar cutar Polio a baya-bayan . A watan Nuwamba da ya wuce ya yi fama da matsanancin zazzabi da ciwon kirji.

“Lokacin da ɗana ya wayi gari da safe, sai muka lura kafar shi daya bata aiki, ya gagara tashi tsaye,” in ji Jaleel Ahmad mahaifin Jawad.

Likitoci sun tabbatar Jawad ya samu matsalar shanyewar barin jiki.

“Abin tashin hankali ne gare ni da maiɗakina. Na sa ke kai shi wurin wani likitan na daban, amma sun shaida min babu abin da za su iya.”

Cutar polio ba ta da magani, sai dai ayi rigakafin kariya daga kamuwa da ita.

“A lokacin da aka haife shi, ba mu taba ba shi ko ɗigo daya ba, amma bayan watanni uku da haihuwarsa an yi ma sa. Amma ba mu kai shi an yi masa allura ba.”

Jaleel Ahmad ya kan tafi da ɗan na sa shagon da ya ke saida kayan masarufi domin ya faranta ma sa. Amma duk da haka da ya tuna makomar ɗan na shi sai hankalin shi ya tashi.

“Idan ya yi kokarin mikewa tsaye ko tafiya ba zai iya ba saboda kafar ta samu tawaya.”

Fata na gari

Jami'ar lafiya na ɗigawa yaro rigakafin cutar polio a lokacin gangamin yaki da cutar a birnin Karachi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cutar polio ba ta da magani, sai dai za a iya yin rigakafin kariya daga kamuwa da ita

Duk da karuwar cutar polio, amma WHO ba ta da masaniya.

“ƙwayar cutar polio ta sake bulla a shekarar nan,” in ji Dakta Hamid Jafari, daraktan gangamin kawo karshen polio na WHO, a yankin Mediterranean.

Idan ana son kakkabe cutar polio a ƙasashen Afghanistan da Pakistan, sai an hada da yi wa yara 'yan ƙasa da shekara biyar rigakafin cutar akan tsari.

“Ma su yin rigakafin da ke zuwa gida-gida, su ne za su iya aikin nan na duba duk inda ake da yara da tabbatar da an yi musu ɗigon rigakafin,” in ji Jafari.

Masu rigakafin na tafiya mai nisan gaske, ko dai a mota ko babura ko adaidaita sahu domin shiga yankunan karkara.

Duk da karuwar masu cutar, Dakta Jafari ya ce, ya ce tasirin yaduwar cutar da karfinta ya ragu matuka idan aka kwatanta da shekarar 2020.

Me cece cutar polio kuma ta yaya take yaɗuwa?

Matan Afghanistan sanye da burqa ta rufe fuska, ya yin da ake yi wa yarinya digon rigakafin polio a Jalalabad ranar 21 ga watan Agusta 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gwamnatin Taliban ta dakatar da digon rigakafin polio da mata ke yi a gida-gida
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Polio ƙwayar cuta ce yaɗuwa tamkar wutar daji, musamman idan mai cutar ya yi tsuguno, ko wanda ya yi tari ko atishawa.

Yawanci yara ƙanana cutar polio ta fi kamawa, daga shekara biyar zuwa kasa.

“Ɗaya cikin 200 da suka kamu da cutar su na ƙarewa da shanyewar ɓarin jiki, kashi biyar zuwa goma cikin waɗanda suka samu shanyewar jiki su na mutuwa da zarar sun garkuwar jikinsu ta yi rauni, sun kuma fara kokawa jan numfashi,” in ji WHO.

Shirye-shiryen da ake gudanarwa na rigakafi sun yi nasarar kakkaɓe biyu cikin uku na kwayar cutar, sai dai har yanzu tsugune ba ta kare ba.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce: “Matuƙar za a ci gaba da samun ko da yaro ɗaya ne da ƙwayar cutar, dukkan yaran ƙasashen duniya na cikin haɗarin kamuwa da polio.”

Sai dai za a iya magance polio ta hanyar karfafa rigakafi wadda ke dauke da rarraunar kwayar cutar da ba za ta yi wa lafiya illa ba. Wanda aka yi wa rigakafin idan ya yi bahaya zai bi ta cikin magudanar da ya ke wucewa ta haka zai raunana wanda ya ke cikin magudanar.

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Amurka ta ce yawan rigakafin da aka yi musamman a nahiyar Afurka ta rage cutar.

Ya yin da ake fama da yaki a zirin Gaza, wani yaro dan shekara 10 ya samu shanyewar jiki sakamakon kamuwa da cutar polio a watan Agusta da ya wuce. Ba tare da bata lokaci ba hukumar lafiya ta duniya ta dauki matakin kaddamar da rigakafin polio.

Rigakafi

Gulnaz Shirazi na digawa yaro rigakafin polio

Asalin hoton, Gulnaz Shirazi

Bayanan hoto, Gulnaz Shirazi ta ci gaba da yi wa yara digon rigakafin polio, duk da mutuwar danginta biyu

Shirin kakkabe cutar polio ya ce cikin shekaru goma da suka gabata, an yi wa yara digon rigakafin biliyan goma, cikinsu biliyan uku yara kanana ne a fadin duniya.

Ƙasar Pakistan na yawan yin gangamin rigakafin da jami'an lafiya ke zuwa gida-gida, na baya-bayan nan da kasar ta yi shi ne watan Satumba da ya wuce.

Bayan giɓin da aka samu na shekaru biyar, a watan Yunin 2024 an ci gaba da yin rigakafin na gida-gida a Afghanistan. Amma an gwamnatin Taliban ta soke gangamin a watan Satumbar bana.

Sai dai ma'aikatar lafiya da ke ƙarkashin gwamnatin Taliban, ba ta amsa tambayar da BBC ta yi ba kan makomar gangamin rigakafin.

Kai wa masu aikin rigakafi hari

Amir Ali zaune akan kujera, da sanfar guragu a gefensa na dama

Asalin hoton, Amir Ali

Bayanan hoto, Amir Ali na amfani da fadi-tashin da ya yi fama da shi, domin karfafa gwiwar karin mutane shiga gangamin yaki da polio

Tsoro, da camfi, da bayanan karya da kai hari, na daga cikin dalilan da suka sany aikin rigakafin polio ya samu nakasu a kasashen Pakistan da Afghanistan.

Shirin kakkaɓe polio a Pakistan, ya ce a wannan shekarar kadai an kashe masu aikin digon rigakafin polio 22 aka kai wa hari ta re da hallaka su.

Wani mummunan hari da aka taba kai wa masu digon cutar polio a Afghanistan, shi ne na shekarar 2004, wanda aka kashe jami'an lafiya takwas a hare-hare hudu da aka kai mu su a rana guda.

Sai dai ana da kyakkyawan fata da ƙwarin gwiwa kan jajircewar da mace kamar Gulnaz Shirazi da Amir Ali suka yi.

Tun a shekarar 2011 ne Gulnaz Shirazi ta fara aiki a matsayin jami'ar lafiya mai digon rigakafin cutar polio, a babban birnin Muzaffarabad na yankin Kashmir. Ta na aikin gangamin tare da 'yan uwanta hudu, amma an kashe biyu daga cikinsu.

“Da ido na, na ga matar yayana da 'yar ɗan uwana ƙwance miki a makara. Madeha mai shekara 18 ta fi min kama da wadda ke bacco, matashiya ce. Matar yayana Famida mai shekara 46 na kwance a dayar makarar, jini duk ya lullubesu, anan ta ke suka mutu.

''Kisan rashin imani akai mu su.''

Shirazi ta ce ba ta san dalilin da ya sa ake kai wa masu digon polio hari ba, ta sancewa ana yawan hararsu amma duk da hakan ba ta sare ba.

Amir Ali ya kamu da cutar polio ya na da shekaru hudu a duniya, lamarin ya shanye masa kafa daya. Sun yi kaura daga Swat Valley zuwa Karachi, a yanzu ya na aikin digon rigakafin polio.

“Lokacin da na ke tasowa, an yi min tiyata har sau takwas amma sam ban warke ba, dole na hakura.''

Saboda rashin takamaimai abin hawa, dole ya na ji ya na gani ya daina zuwa wasannin da ya ke yi domin balaguro na ma sa wuya. Mahaifiyarsa ma ta shiga damuwa ba kadanba.

“Wata rana sai na ga an tallan neman ma'aikata da za su yi aikin digon polio, nan da nan na cike, saboda burina a kawo karshen cutar daga doron kasa.''

Amir mai shekara 36 a duniya, da sandar guragu ya ke tafiya, ya na amfani da tarihin rayuwarsa domin fadakar da jama'a da karfafawa masu lalurar gwiwa.

“Ina fadawa mutane idan har ba a yi wa 'ya'yansu digon rigakafin polio ba, to kuwa za su zama tamkar ni.''

Amir na shirye-shiryen gangamin rigakafin cutar Polio da za a fara ranar 28 ga watan Oktoba.

Pakistani policemen escort a team of polio health workers during a polio vaccination campaign in Quetta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Despite heavy security polio workers are routinely targeted in Pakistan. This year 22 people got killed while doing vaccination

Kakkaɓe cutar polio daga ban ƙasa

Hukumar lafiya ta duniya WHO na aiki tukuru domin wayar da kan wadanda ke kin yi wa 'ya'yansu rigakafin Polio.

Da magance labaran karya da canfin da ake yi kan cutar, damagance karairayin da ake yadawa kan polio kakafen sada zumunta.

Shirin na digon polio zai yi amfani da dabarun yada labarai masu saukin fahimta akan cutar, da janyo fitattun mutane na shafukan sada zumunta da wakilai da shugabannin al'umma a gangamin.

“Mu na da kuduri da burin da muka ci na kakkabe cutar polio baki daya daga ban kasa zuwa shekarr 2025, kuma za mu tabbatar da mun yi aiki tukuru kan cikar burinmu,'' In ji Dakta Jafari.