Daga ina TikTok ya samo asali kuma me ya sa yake haifar da cece-ku-ce?

Asalin hoton, Getty Images
Manhajar wallafa bidiyo ta TikTok ta kasance fitacciyar manhaja tsakanin matasa a faɗin duniya.
To amma shekaru da dama kamfanin mallakin China na fuskantar tuhuma kan kariyar bayanan masu amfani da shafin, da kuma alaƙarsa shafin da gwamnatin ƙasar.
Ƴan siyasar Amurka na gudanar da muhawara don samar da dokokin da za su tilasta wa kamfanin TikTok ɗin sayar da wani bangare na manhajarsa, to amma tsohon shugaban Amurkan, Donald Trump ya soki ƙudurin dokar, duk kuwa da cewa a baya ya goyi bayan ƙudurin.
Mene ne TikTok, sannan ya tasirinsa yake?
TikTok wani shafi ne da ake wallafa gajerun bidiyoyi, kamar Youtube, shafin na bai wa mutane dama wajen wallafa bidiyo ko yaɗa shi da kuma yin tsokaci kan bidiyon da wani ya wallafa.
Tsawon bidiyon kan kama daga daƙiƙa uku zuwa tsawon minti uku, kuma masu amfani da shafin ka iya yin gyare-gyare a bidiyon da suke son wallafawa ta hanyar ƙara ko rage musu haske, da sanya kiɗa ko jera hotunan da suke muradi.
Shafin ya fara shahara ne tsakanin matasa inda suke gudanar da gasanni da dama "Challege'' na raye-raye da wasu abubuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Dangane da shekaru da inda masu amfani da shafin suke, wasu masu amfani da shafin kan wallafa bidiyoyi kai-tsaye ga mabiyansu, da kuma tallafa wa wasu masu amfani da shafin da kyaututtuka.
Shafin na TikTok, yana kuma tallata kaya a intanet, inda yake bai wa masu amfani da shi damar sayen kaya, ciki har da waɗanda aka gani a bidiyon wasu.
Tun farkon shekarar 2019, shafin ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan manhajoji da aka fi saukewa kan wayoyin hannu.
Shafin ya zarta Intagram a matsayin shafin da aka fi saukewa a shekarar 2023, kamar yadda Sensor Tower -da ke sanya ido kan rawar da shafukan sada zumunta ke takawa - ya bayyana.
A watan Maris ɗin 2023, shafin ya samu masu amfani da shi kusan miliyan 150 a Amurka.
Wane ne mamallakin TikTok?
Kamfanin ByteDance na ƙasar China ne da aka samar a shekarar 2012, ya mallaki shafin TikTok.
Kamfanin na China, wanda aka fara yi wa rajisata a tsibirin Cayman - na da ofisoshi a faɗin ƙasahen Turai da Amurka.
Shafin na da manhajar gyaran bidiyo da ake kira Capcut, da manhajoji da kawai ake iya samu a China, ciki har da Douyin, shafin TikTok da ƴan china ke amfani da shi.

Asalin hoton, Getty Images
Shou Zi Chew, ɗan kasuwa ɗan asalin ƙasar Singapore shi ne shugaban shafin, duk da cewa wasu na ganin cewa mamallakin kamfanin ByteDance, Zhang Yiming ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da shafin.
Yaya TikTok ke aiki?
Amfani da shafin TikTok lissafi ne.
Wannan wasu tarin ƙa'idoji ne da ake amfani da shi domin samar da abubuwan wallafawa a shafin, dangane da abubuwan da masu amfani da shafin suka fo muradi.

Asalin hoton, Getty Images
Shafin kan bai wa masu amfani da shi zaɓin abu uku, wato waɗanda kake bibiya a shafin, da abokai da kuma kai kanka mai amfani da shafin.
Ɓangaren mutanen da kake bibiya da abokai, kan gabatar wa mai amfani da shafin abubuwa daga mutanen da ya zaɓi ya bibiya a shafin da waɗanda suma suke bibiyar ka, amma dangane da shafin abin da zai zo maka a ɓangaren kai kanka , shafin ne ke kawo shi kai tsaye.
Wannan wuri ya zama wurin da masu amfani da shafin suka fi dubawa don ganin sabbin abubuwa, sannan masu wallafa abubuwa ke muradin abin da suka wallafa ya faɗa ciki, domin ya samu yaɗuwa.
Me ya sa shafin TikTok ke janyo ce-ce-ku-ce?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƴan siyasa da masu lura da shafin a faɗin duniya, na nuna damuwa kan ƴan Chinan da suka mallaki shafin, duk kuwa da ƙoƙarin da mamallakin shafin ke yi na nusar da su cewa shafin ba shi da wata barazana.
Kamar sauran shafukan sada zumunta, TikTok na tattara bayanai daga masu amfani da shi, to amma shafin na fuskantar matsin lamba kan yadda yake tattara bayanan mutane tare da tantance su.
A taƙaice dai masu suka na fargabar cewa bayanan masu amfani da shafin ka iya faɗawa hannun gwamnatin China, wani abu da TikTok da ByteDance suka sha musanta faruwarsa.
A ƙarshen shekarar 2022, wata ƴar jaridar Birtaniya ta ce ta gano ana bibiyar shafinta.
Kuma a shekarar 2023 wasu cibiyoyi masu yawa, ciki har da gwamnatin Birtaniya da majalisar dokokin ƙasar da Tarayyar Turai da fadar gwamnatin Amurka suka dakatar da ma'aikatansu daga amfani da shafin a kan wayoyinsu na aiki.
Shafin na TikTok ya sha nesanta kansa daga mamallakansa na China, tare da yin ƙoƙarin tabbatar da kula da shafin ta hanyar ɓullo da sabbin matakai ciki har da ''Project Clover'' wanda aka fara amfani da shi wajen adana bayanan masu amfani da shafin a Turai.
Mene ne kudurin dokar TikTok? Shin Amurka za ta haramta TikTok?
A wannan watan Maris da muke ciki ƴan siyasar Amurka daga manyan jam'iyyun ƙasar biyu sun gabatar da ƙudurori da suka buƙaci a samar da dokokin da za su sanya ido kan kamfanin.
Idan ƙudurin ya yi nasara, zai tilasta wa kamfanin ByteDance ya sayar da TikTok cikin wata shida, ko ya fuskanci haramcin amfani da shafin a Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai sanya hannu kan ƙudurin don ya zama doka da zarar majalisa ta miƙa masa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Amurka ke yunƙurin taƙaita aiki da shafin, ''saboda barazana tsaron ƙasar''

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump bai yi nasara kan yunƙurinsa na haramta amfani da shafin a 2020 ba, a lokacin da yake shugabancin Amurka.
To amma Mista trump - wanda ke fatan zama ɗan takarar jam'iyyar Republican a zaɓen 2024 - ya soki sabon kudurin, yana mai cewa taƙaita amfani da shafin TikTok, zai taimaka wa Facebook.










