Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ƴanbindiga na cin karensu ba babbaka a jihar Katsina'
A Najeriya, a daidai lokacin da Muslimi ke azumin watan Ramadana yanbindiga a wasu jihohin arewacin kasar har yanzu ba su kakkauta ba wajen kai hare-hare kan farar hula.
Na baya-bayan nan shi ne wanda suka kai a ranar Asabar da daddare a garin Mairuwa na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina kan masu sallah.
Shugaban karamar hukumar Musa Ado Faskari ya tabbatar wa BBC, lamarin inda ya ce an kashe mutum biyu an kuma sace mata biyu.
Shugaban ya shaida wa BBC cewa hare-haren ƴanbindiga na ƙara ƙamari a yankinsu ; " Wannan al'amari sai dai mu ce Innalillahi Wa Inna ilaihiraji'un saboda kwanan nan mun rasa gane kan al'amarin, abin ya dawo fiye da yadda yake a da, suna ta shiga garuruwa kullum, ko ranar Juma'a sun shiga garin Yanmalamai sun kashe mutum biyu sun tafi da mata."
Bayanai sun nuna cewa ƴanbindiga sun yi manyan sansanoni a yankin na ƙaramar hukumar Faskari, lamarin da ke haddasa yawan kai hare-hare a garuruwan yankin, "Kuma ko ranar Juma'a da yamma sai da suka kashe wani soja," cewar Musa Ado.
Shugaban ƙaramar hukumar Faskarin ya shaida wa BBC cewa abin ya ta'azzara kuma suna neman taimako daga gwamnatin tarayya a yankinsu saboda suna cikin matsala babba "wannan al'amari yana neman ya gagari kundila."
"Mutanen nan dole a shiga cikin daji a yaƙe su ba sai an jira su saboda suna da dabaru kala-kala da suke mana ta'annati."
Al'ummar yankin ƙaramar hukumar Faskari na cikin fargaba saboda hare-haren ƴanbindiga, lamarin da ya janyo rufe wasu hanyoyin yankin.
A hirar sa da BBC a kwanakin baya gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin da ƴanbindiga ke cigaba da kai hare hare a wasu yankunan jihar.
Gwamnan ya ce tun bayan da ya karɓi mulki, gwamnatinsa ta samu nasara sosai a yakin da take yi da ƴan bindiga, ciki har da kafuwar rundunar tsaro ta musaman wadda a cewarsa ta taimaka wajan dakile hare-haren yan bindigar.
Ya ce: "Mutumin Jibia da mutumin Batsari da na Kankara da na Danmusa da na Sabuwa da na Faskari da na Dandume sun san cewa an samu sauƙi a matsalar tsaron da muke fuskanta a jihar Katsina’’
Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ta ‘yan fashin daji wadanda ke kai hare - hare garuruwa da kauyukan jihar baya ga satar mutane don neman kudin fansa da kuma sace dukiyoyin mazauna yankin.