Ƙasar da hodar Iblis ke neman durƙusar da al'ummarta

Hoton matashi Jude
Bayanan hoto, An sha ɗaure Jude Jean a kurkuku saboda sata domin ya sayi hodar da yake sha

Kusan kashi 10 cikin 100 na ƴan ƙasar Seychelles sun dogara ne a kan ta’ammali da hodar Iblis ta heroin wadda ta zamar wa tsibirin annoba a yanzu, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta faɗa da kanta.

Ko da tura mutum aka yi aka garkame shi a gidan yari wannan ba ya raba shi da ita.

BBC ta samu wata dama da ba kasafai ake samun irinta ba inda ta shiga babban gidan yarin ƙasar wanda ke kan tsauni, inda ta gudanar da bincike kan wannan matsala da ke neman mamaye ƙasar.

A ƙofar wannan gidan yari inda ake ajiye fursunonin, bayan ka wuce ƙofofi daban-daban da kuma waya mai tsini duk domin tabbatar da tsaro, za ka iske wani zanen hoton tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela, wanda kusan kowa ya san irin zaman da ya yi na gidan yari.

A gefen hoton akwai rubutun da aka yi da cewa‚ ‘An ce ba wanda ya san wata ƙasa kamar wanda ya shiga kurkukunta.’’

Zanen hoton Mandela

Ba shakka ta fuskoki da dama yanayin gidan kurkukun na nuna irin halin da ƙasar take ciki, bayan fice da sunan da ta yi na wuraren shaƙatawa.

Wakilan BBC sun shiga wannan kurkuku domin ganawa da ɗaya daga cikin fursunonin mai suna Jude Jean.

To amma an fara kai wakilan na BBC wurin da fursunonin suka ce wuri ne na yaudara ko ƙaryar nuna ainahin yadda gidan yarin yake.

Wannan wuri ne da ke da tsafta da kuma yanayi mai kyau dai-dai gwargwado a matsayinsa na kurkuku.

Ɗaki ne da ke da gadaje har guda takwas, hudu a kowane gefe, ɗaya a kan ɗaya ba tare da wani wuri da mutum zai iya zama a miƙe ba.

A ɗakin akwai banɗaki da shaya, amma kuma babu wani shinge da zai kare mutum idan yana banɗaki, domin babu sirri.

Dab da wannan ɗaki wurin cin abincinsu ne, wanda ganinsa kaɗai ya isa ya tayar wa da mutum hankali saboda lalacewa da kuma ƙazantar da ke wurin. Ga warin da ke tashi, kana iya ganin ƙudaje suna ta kai-komo.

Daga nan sai babban ɗakin kurkukun. Duk da cewa da rana ne muka shiga wurin to amma wurin duhu ne duɗum. In banda wasu ƴan ƙananan ƙwayayen lantarki da ke ɗan haska wurin ba wani haske.

Fursunonin suna amfani da kwalaye ne su kare ɓangaren da suke zaune kamar ɗakinsu ke nan. Wurin ya kasance kamar kowa na cikin wani ɗan keji ne, ga katifu nan baƙiƙƙirin a ƙasa.

Hoton gado
Bayanan hoto, Ɗakunan gidan yarin ƙanana ne kuma babu shinge

Duk da wannan yanayi da ake ciki a kurkukun da kuma irin tsaron da ya kamata a ce yake da hakan bai hana gudanar ta’ammali da hodar iblis ta heroin ba.

Kasancewarsa gidan yari bai hana shigar da hodar ba zuwa ga fursunonin.

Wannan yanayi ya jefa wannan ƙasa cikin abin da za a iya cewa annoba.

An yi ƙiyasin kashi goma cikin ɗari na al’ummar ƙasar sun kamu da jarabar shan hodar.

Wannan ne ma ya sa sai ma’aikata ‘yan ƙasashen waje ne ke yin wasu ayyukan da ya kamata a ce ‘yan ƙasar ne suke yi, saboda ‘yan ƙasar da ke ta’ammali da hodar ba za su iya ba.

Wannan ne ya sa ‘yan ƙasar Tanzania ke aikin gadin kurkukun duk domin magance rashawar da ake yi a wurin da kuma shigar da hodar kurkukun- to amma fa duka wannan kusan ba ya aiki.

Rashawa da miyagun ƙwayoyin da ke kai komo a gidan yarin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hatta shugaban ƙasar, Wavel Ramkalawan ya yarda cewa wannan gidan yari bai dace da wannan ƙoƙari da magance ta’adar ta’ammali da hodar Iblis ɗin ba.

Ya ce, ‘’idan kana fama da wannan matsala to wannan wuri tamkar wata matattara ce ta habaka rashawa, inda miyagun ƙwayoyi za su ci gaba da shiga gidan yarin ,’’ kamar yadda ya gaya wa BBC.

Sai dai ya ce yana shirin gina wani gidan yarin. Kuma ya yarda cewa matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyin ta yi muni ƙwarai.

Bisa ƙiyasi yanzu za a iya cewa Seychelles ce ta ɗaya a duniya a wurin ta’ammali da hodar iblis ta heroin, in ji shugaban.

Ya ƙara da cewa wannan ba abu ne da ke faranta masa rai ba ko kaɗan.

Yau take ranar masu ziyara a gidan yarin. Jude wanda ke zaman waƙafi a gidan yarin saboda laifin sata, yana jiran mahaifiyarsa a lokacin da muka je.

Jude mutum ne da za ka so shi – mai faram-faram da yakana. To amma shi ma ya kamu da jarabar shan hodar Iblis.

Ya ce shi kansa yana jin kunya a ce yana ta’ammali da ita, to amma ba yadda zai yi dole ne, in ji shi a lokacin da BBC ke tattaunawa da shi.

Yayin da ya zauna muke tattaunawa da shi kuma yana jiran mahaifiyarsa, da ka ga idonsa za ka san cewa ya sha hodar, duk kuwa da cewa yana gidan yari yana samun hodar.

Hoton mahaifiyar Jude Ravinia
Bayanan hoto, Mahaifiyar Jude, Ravinia, ta shaƙu da shi duk da shan ƙwayar da yake yi

Jude ya shafe shekara goma yana shiga gidan yari yawanci saboda sata domin ya sayi hodar da zai sha.

Da haka mahaifiyarsa, Ravinia take faman haƙuri. A lokacin da ta zo ganinsa tana cike da farin ciki, duk kuwa da irin abubuwan da ke damunta a rai.

Tsawon shekaru take faɗi tashin kula da ‘ya’yanta huɗu inda take harkar sayar da abinci a kanti.

Duk da irin wannan faɗi tashi da take yi a 2011 babban ɗanta, Tony.

Har zuwa wannan lokaci mutuwar tasa ta ɗaure wa mutane kai. To amma shi kansa yana ta’ammali da ƙwayar.

Ravinia ta yi amanna cewa ba shi ya kashe kansa ba.

Yadda take magana kana iya ganin yadda take tunani mai zurfi, cikin damuwa.

Har zuwa yau ɗin nan tana mamaki da damuwa kan yadda za a ce ba ɗanta ɗaya ba har ma biyu za su samu kansu cikin wannan muguwar ta’ada.

Lokacin da Jude ya iso inda take sai ta kama murmushi, inda suka rungumi juna.

Wannan ƙauna da soyayya da ke tsakanin ɗa da mahaifi, ita ce ta bayyana a lokacin wadda ta ɗan kore mata wannan damuwa, tana zub da hawaye.

Ta bayyana mana irin yadda rayuwa take a tsakaninta da Jude, da irin fatan da take cike da shi na ganin ya rabu da wannan ta’ada da ta’ammali da hodar iblis ɗin.

Ta gaya mana irin yadda ya rinƙa kwashe kayansu yana sayarwa duk domin ya samu kuɗin da zai sayi ƙwayar, hatta zanin gado ma bai ƙyale ba.

A lokacin da aka fara kai shi gidan yari sai ta ji dadi. To amma daga baya sai ta fahimci cewa kamar ta ma tura shi gidan miyagun masu laifi ne.

Hatta a lokacin da yake tsare a gidan yari ana tilasta mata biyan kuɗin hodar da yake sha, wadda ake satar shiga da ita.

Ta ce, ‘’ana yi maka barazana za a kashe shi idan ba ka biya ba.’’

Har kullum Jude yana yi wa mahaifiyar tasa alƙawarin cewa zai bar wannan ta’ada, yayin da ita kuma cikin hawaye take ce masa ya hanzarta kafin lokaci ya ƙure masa.

Duk da halin da ake ciki a gidan yarin ba za a ce za a yanke ƙauna ba domin akwai shiri da ake gudanarwa na dawo da masu ta’ammali da hodar kan hanya.

Hoton bakin teku
Bayanan hoto, Ƙasa ce mai wuraren shaƙatawa amma kuma take fama da wannan matsala

Yawanci ana satar shigar da hodar ne Seychelles daga Afghanistan da Iran ta ƙananan jiragen ruwa ta iyakokin ruwa marasa tsaro na ƙasar.

Kusan duk wani kanti ko shago na unguwa ka leka a bayan manya-manyan otal na ƙasar za ka samu hodar.

Sana’a ce da za a ce ta samu gindin zama a kasar kusan mutane da dama suna cikinta.

Wani abin fargaba shi ne yayin da wannan ta’ada ta ta’ammali da hodar ke wanzuwa wani babban bala’in kuma shi ne na fara ɓullar wasu miyagun ƙwayoyin masu tsada da ake harhaɗawa a ɗakunan kimiyya.

Waɗan nan miyagun ƙwayoyi irin su koken da sauransu yanzu sun fara samun karɓuwa a kasar kuma matsalarsu ita ce ba kamar hodar heroin ba su ba a maganinsu kamar yadda ake yi wa masu shan hodar.

Neman rabuwa da ƙwayar

Hoton Jude da ma'aikaciyar asibiti
Bayanan hoto, Jude na ƙoƙarin rabuwa da shan hodar iblis

‘Yan kwanaki bayan ziyarar da mahaifiyarsa ta kai masa gidan yari Jude, ya yi ƙoƙarin barin wannan ta’ada inda ya je asibitin gidan yarin inda ake yi wa masu shan hodar magani.

To amma ko a lokacin ya je ne cikin maye. Da aka gwada fitsarinsa an ga yana ɗauke da hodar saboda haka aka ce masa in dai har yana son a sa shi cikin waɗanda ke musu maganin barinta to dole ne sai ya yi watsi da ita gaba ɗaya.

Ya yarda zai yi, to amma ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba yana yin hakan amma kuma ya koma ruwa daga baya.

Duk da haka mahaifiyarsa ba ta yanke ƙauna ba tana cike da fata da addu’a a wannan karon zai jure.