Muhimman abubuwa huɗu kan fita a kaɗa kuri'a a ranar zaɓe

Asalin hoton, Getty Images
Yau ne ake gudanar da zaben gwamnonin jihohi 28 a Najeriya tare da na wakilan majalisun dokokin jihohi.
Malaman addinai da masu fafutika da masana na jan hankalin 'yan kasar kan muhimmnacin fita a kaɗa kuri'a.
'Abin da ya kamata a sani'
Fitar jama'a su je rumfunan zaɓe, su kaɗa kuri'a wani muhimmin abu ne a kowane zabe.
Barista Muhammad Mansur, malami a jami'ar Usmanu Dan Fodio da ke Sakkwato, ya yi wa BBC bayani bisa dogaro da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce sashi na 77 na kundin tsarin mulkin kasa ya tanadi duk wani ɗan Najeriya wanda ke zaune a kasar kuma ya kai shekara 18 a yi masa rajista ya yi zaɓe.
Zabe ƴanci ne ga 'yan kasa duk bayan shekara hudu ya zaɓi wanda yake so, idan mutum bai yi masa ba sai ya sauya su.
'Zaɓi sonka'
Shi kuwa Dokta Kole Shettima, shugaban cibiyar tabbatar da dimokuradiyya da raya kasa, wato CDD, a Najeriya, ya ce yin zaɓe wata dama ce irin ta zaɓi sonka ga 'yan kasa.
Ya ce ƴancin ɗan adam ne mutum ya zaɓi wanda zai shugabance shi, ba wai mutum ya ɗauki bindiga ya ce zai mulki mutum ba.
Don haka yana da muhimmanci mutane su fito su kaɗa kuri'arsu domin samun mutumin da zai shugabance su cikin adalci.
Kuma mutum na da dama bayan wasu shekaru idan bai gamsu ba, ko bai cika burinsu ba, ya sake zaɓen wani mutum ko shugaba na gaba.
Ba dai-dai ba ne mutum ya noƙe ko ya ƙi fitowa a ranar zaɓe.

End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta

'Kuri'arka 'yancinka'
Shi kuwa Farfesa Ibrahim Ahmad Makari, limami daga cikin limaman babban masallaci na kasa da ke Abuja, ya ce yin zaɓe wani wajibce ne.
Ya ce ta hanyar fitowa a yi zaɓe ne kawai za a iya tabbatar da adalci a bayan kasa.
Kuma wajibi ne mutum ya yi iya kokari wajen bayar da gudumawarsa, cikin tabbatar da adalci domin kuri'arka ɗaya na iya samar da bambanci, mutum ya samu daukaka kan wani.
Zaɓe na da kyakyawan tasiri a ciki al'umma.
'Zabe wani abu ne mai dadadden asali'
Rabaran Murtala Mati Dangora, wani jigo a kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato CAN, ya ce yin zaɓe wani abu ne mai dadadden asali.
"Zaɓe ba sabon abu ba ne a cikin littafi mai tsarki, saboda sarki Isra’ila na farko jama’a ne suka fito suka zabe shi lokacin Annabi Isma'il", in ji Mati Dangora.
"Sannan lokacin salwantar ɗaya daga cikin almajirin Yesu, zaɓe sauran almajirai suka kira domin maye gurbinsa."
Ya ci gaba da cewa, zaɓe wajibi ne domin bai wa mutane da suka dace damar mulki.
Zaɓe 'yancin 'yan kasa ne don haka dole kowa ya fita ya kada kuri'arsa.
Mutane su daina tunanin cewa kuri'arsu ba za ta yi tasiri ba, domin 'yancinsu ne da ke iya kawo sauyin da ba su taɓa tunani ba.











