Saudiyya ta kusa samun damar daukar bakuncin gasar kofin duniya ta 2034

World Cup Trophy

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Bisa dukkan alamu, kasar Saudiyya ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta maza a shekara ta 2034, bayan janyewar Australia daga takarar neman bakuncin gasar.

Hukumar kwallon Australia ta tabbatar da janyewar kafin wa'adin da Fifa ta bayar na ranar Talata ga kasashen da ke da sha'awar daukar bakuncin.

A yanzu Saudiyya ce kadai ta rage cikin kasashen da ke neman wannan danar.

"Mun yanke shawarar jingine neman bakuncin gasar a 2034," in ji sanarwar da hukumar kwallon Australia ta fitar.

Za a buga gasar cin kofin kwallon duniya ta 2026 a kasashen Amurka da Mexico da kuma Canada.

Morocco, Portugal da kuma Spaniya ne za su karbi bakuncin gasar da za a yi a 2030, amma kuma za a buga wadansu wasannin a Argentina, Paraguay da kuma Uruguay.

Saudi Arabia ta karbin bakuncin gasar wasanni da dama tun daga shekara ta 2018 a kwallon kafa da Formula 1 da golf da dambe.

Yarima Abdulaziz bin Turki bin Faisal wanda shi ne ministan wasannin Saudiyya ya ce karbar bakuncin gasar kwallon kafa "na da mahimmanci kuma abu ne da ke da farin jini a tsakanin 'yan kasarmu".