Saudiyya ta nada Mancini sabon kociyanta

Asalin hoton, BBC Sport
An nada Roberto Mancini a matsayin sabon kocin Saudiyya makonni biyu bayan ya yi murabus a matsayin kocin Italiya.
Mai shekaru 58 ya jagoranci Italiya ta samu nasara a gasar Euro 2020, inda ta doke Ingila a bugun fanariti a wasan karshe a Wembley.
A karkashin Mancini tawagar Italiya ta kafa tarihin buga wasa 37 ba tare da an doke ta ba a jere, amma ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022.
Ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa 2027. Wasansa na farko da zai jagoranta zai zama ranar 8 ga Satumba da Costa Rica a filin wasan St James' Park da ke birnin Newcastle.
A gasar cin kofin duniya da aka yi a bara a karkashin tsohon kociyan tawagar Herve Renard, Saudi Arabiya ta gigita Argentina da ci 2-1 a Qatar amma ta kasa tsallake matakin rukunin farko a gasar.
Mancini ya jagoranci Manchester City ta lashe gasar Premier na farko a shekara ta 2012, sannan ya jagoranci Fiorentina da Lazio da Inter Milan da Galatasaray da Zenit St Petersburg.






