'Tsadar rayuwa ta sa kuɗina ba za su kai ni Hajji ba a yanzu'

Asalin hoton, Getty Images
Tuni aka fara aikin Hajjin bana a garin Makka na Saudiyya, inda miliyoyin Musulmai suka taru don gudanar da ibadar.
Sai dai sakamakon hauhawar farashi a faɗin duniya, Musulmai da yawa ba su samu damar zuwa ba a wannan shekara.
"Adadin masu zuwa ya ragu sosai a wannan shekarar. Lamarin ya yi wa mutane da yawa tsada," a cewar wani jami'in yawon buɗe-ido a Alƙahira da ke aikin shirya tafiya Hajji.
Jami'in ya nemi a ɓoye sunansa saboda tsoron abin da zai biyo bayan sukar tsarin tattalin arzikin ƙasar.
Kujerar zuwa aikin Hajji mafi sauƙi a farashin gwamnatin Masar ta kai dala 6,000 (kusan naira miliyan 4.5) , wanda ya ninka daga na shekarar da ta gabata.
Saboda haka da yawan 'yan Masar, ƙasar Larabawa mafi shahara a duniya, da ke son zuwa aikin a bana ba su da kuɗin.
Hajji na cikin rukunan Musulunci. Ta wannan shekarar ta fara ne daga Litinin, 26 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yulin 2023.
Ana buƙatar kowane Musulmi ya gudanar da aikin Hajji a rayuwarsa sau ɗaya idan yana da iko a lafiya da kuma arzikin yin hakan.
'Burina na je Hajji'
Hauhawar farashin da aka samu a Masar ta faru ne sakamakon karya darajar kuɗin ƙasar da aka yi.
Tun watan Maris na 2022, kuɗin fan na Masar ya rasa rabin darajarsa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Sakamakon haka, tsadar rayuwa ta ƙaru sosai yayin da kusan kashi 30 cikin 100 na 'yan Masar na zaune cikin hali na 'hannu-baka hannu-ƙwarya'.
Farida, wata ma'aikaciyar gwamanti da ta yi ritaya, ta shafe shekara biyar tana tara kuɗin zuwa aikin Hajji.
"Duk kuɗin da na tara ba su isa ba. Lokacin da na ga farashin kujerar na kaɗu," a cewarta.
Farida wadda ba sunanta na gaskiya ba ne, bazawara ce mai 'ya'ya biyar. Ita ma ba ta so a bayyana sunanta ne saboda ba ta so a san tana sukar tsadar kuɗin aikin Hajjin a bainar jama'a.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa take so ta je Hajji, ta ce: "Burina ke nan. Hajji na tsarkake mutum."
Dukkan 'ya'yanta na da aure. "An ɗauke min nauyin ciyarwa da tufatarwa," in ji ta. "Sannu a hankali zan je Hajji."
Farida ta yi Umara har sau huɗu, wadda ake iya yi a kowane lokaci a cikin shekara.
"Maimakon na samu bizar zuwa Hajji, sai na samu ta yawon buɗe-ido ta wata uku kuma na isa Makka wata ɗaya kafin a fara aikin Hajji," kamar yadda ta bayyana.
Tallafin zuwa Hajji
Hajji na ɗaya daga cikin manyan tarukan addini na duniya duk shekara, kuma mutum miliyan ɗaya zuwa biyu ne ke halartar wuraren ibadar a birane Makka da Madina.
Akasin da aka samu kawai a 2020 ne, lokacin da aka rage yawan mahajjatan saboda annobar korona.

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya kan ware wa kowace ƙasa adadin mahajjata duk shekara.
Indonesia ce ta fi kowace ƙasa yawan mahajjata. Tana da al'umma miliyan 270, abin da ya sa ta zama ƙasar Musulmi mafi girma a duniya. Hakan ta sa aka ba ta mahajjata 220,000.
Gwamnatin Indonesia ta ba da tallafin zuwa aikin Hajji da kashi 60 cikin 100, amma wannan karon ta rage yawan tallafin zuwa ƙasa da kashi 50, inda maniyyata suka biya kusan dala 3,000 - kusan naira miliyan uku.
Mahajjatan Yemen
Duk da cewa maniyyata a faɗin duniya na fuskantar matsalolin kudi, lamarin ya fi ƙamari a kan maniyyatan Yemen, wadda maƙwabciyar Saudiyya ce kuma take cikin yaƙi.
Wannan ne karon farko da maniyyata daga Yemen suka tashi kai-tsaye zuwa Hajji tun 2015, bayan Saudiyya ta jagoranci dakarun ƙawance wajen ƙaddamar da yaƙi kan ƙungiyar Huthi mabiya Shia.
Babu jirgin fasinja da ke bi ta sararin samaniyar ƙasar saboda yaƙin. Sana'a babban birnin ƙasar ya kasance a ƙarƙashin ikon Huthi tun Satumban 2014.
Farashin kujerar Hajji na tsakatsaki a Yemen ya kai dala 3,000.
"A 2016, na je Hajji da rabin wannan farashin, kuɗin ya yi min tsada a yanzu," in ji wani ɗan jaridar Yemen.









