Shugaban El Salvador ya tura dubban dakaru domin yakar kungiyoyin miyagu

Asalin hoton, PRESIDENT NAYIB BUKELE
Shugaban El Salvador ya tura dubban sojoji da 'yan sanda zuwa wani yanki na gefen babban birnin kasar wanda matattarar manyan kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka ne kuma kungiyoyin bata-gari ke da karfi.
Shugaba Nayib Bukele, ya ce dakarun sun yi wa yankin Soyapango, da ke gabashin babban birnin, San Salvador, kawanya, inda aka ba su umarnin su kamu miyagun da duk wani dan daba, daya bayan daya.
A watan Maris ne shugaban kasar ya sanya dokar-ta-baci bayan kashe-kashen jama'a da aka rika yi, inda ya yi alkawarin ganin bayan duk wani mugu, da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Bukele ta yanke shawarar cewa za ta tura dakaru dubu goma zuwa gundumar Soyapango karkashin wani shiri da aka yi wa lakabi da 'Extraction'.
Gundumnar ta Sayapango da ke wajen garin San Salvador babban birnin kasar El Savador ta dade da zama matararar kungiyar masu aikata miyagun laifuka ta MS 13, daya daga cikin kungiyoyi biyu masu karfin fada a ji a kasar.
A karkashin tsarin Shugaba Bukele ya ce za a tura sojoji da yan sanda domin kama mutanen da ake zargin mambobin kungiyar ne ta hanyar amfani da na'urar leken asiri ta zamani da kuma wani bangaren na yankin da aka yi wa kawanya domin hana duk wani da ke da alaka da wadannan kungiyoyin shiga ko fita daga yankin.
Haka kuma a karkashin wannan tsari na kebancewa da Mista Bukele ya bayar da umarnin a watanni tara da suka gabata sakamakon karuwar da aka samu a tashin hankalin da ake fuskanta daga kungiyoyi masu aikata miyagun laifuka an kama mutane kusan dubu 57.
Kuma an tura wasu gidajen yarin da ake fama da cunkuson mutane. Gwamnatin kasar ta yi ikirarin cewa shirin ya haifar da sakamako mai kyau musaman a yankunan da a baya ke karkashin ikon kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka.
Kuma kuri'ar jin ra’ayoyin jama'a ta nuna cewa tsarin wanda mai tsauri ne ya samu karbuwa daga wurin 'yan kasar da dama.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil'Adama da ke ciki da wajen kasar na ci gaba da nuna damuwa a kan halin da wadanda aka kama suke ciki a samamen da sojoji suka kai musaman wadanda iyalinsu suka kafe cewa ba sa cikin kungiyoyin da ke aikata miyagun laifuka.











