Allah ya yi wa birin da ya zamarwa jama'a alakakai rasuwa

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai sun ce an kama, tare da kashe wani hatsabibin biri, da ke cikin gungun wasu birrai da suka zamar wa jama'a alakakai a Japan.
Ana kyautata zaton birin ya illata akalla mutane 50 shi kadai.
Wasu mafarauta ne suka yi arba da shi a galabaice, abun da ya sa suka kwantar da shi don ba shi kulawa, amma daga bisani suka halaka shi, bayan gano yana cikin birran da suka addabi gari.
Hukumomi dai na farautar birrai tun lokacin da aka fara kai hare-hare kan manya da yara kimanin makonni uku da suka gabata.
Yawancin raunukan cizo ne, da yakushi da kuma targade da mutane ke ji idan birran suka fafaro su.
Har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin faruwar irin wannan lamari, kuma ana ci gaba da neman sauran birran da ke yawo a gari, kamar yadda wani jami'i a sashen aikin gona na yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
“An samu rahoton sabbin hare-hare,” in ji shi.
Birin da aka kama an kiyasta shekarunsa hudu, kuma tsayinsa ya kai kusan rabin mita.
Irin wadannan hare-hare dai ba a saba ganinsu ba a Yamaguchi.
“A baya-bayan nan, an kai hari ga tsofaffi mata da maza,” a cewarsa.
Tun da farko kokarin da aka yi na kama birin ya ci tura, duk da sinitrin da 'yan sanda suka yi ta yi a farkon watan Yuli.
Lamarin ya rutsa da wata yarinya yar shekaru hudu, da biri ya yakusa bayan bankawa gidansu.











