Kotu ta ɗaure mutum huɗu kan mummunan harin da aka kai a Austria

Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa wasu mutum huɗu ɗauri na lokaci mai tsawo bayan samun su da laifin a wani mummunan hari da wani mai iƙirarin jihadi ya kai Vienna, babban birnin Austria a watan Nuwamban 2020.
Kujtim Fejzulai ya yi dirar mikiya a wani wurin shakatawa da daddare da ake kira Bermuda Triangle, inda ya harbe mutum hudu har lahira da kuma raunata wasu 23.
Harin da ya kai har na tsawon minti tara ya zo karshe ne bayan da ‘yan sanda suka harbe shi.
An dai zargi mutanen da laifin taimaka wa mutumin kafin ya kai harin.
Sai dai ba a samu wasu mutane biyu masu shekara 22 da 23 da laifin haɗa baki ba a kisan da aka yi, sai dai, wasu ƙananan laifuka da aka same su da shi.
Maharin mai shekara 20, da ke da shaidar zama a Austria da Macedonia, an sauya masa tunani ne a Austria, inda ya shafe watanni 18 a gidan yari bayan samun sa da laifin yunkurin shiga kungiyar masu iƙirarin jihadi ta IS, wadda kuma ta ɗauki nauyin harin da aka kai.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da:
- Heydayatollah Z, mai shekara 28, an yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samun shi da laifin kisan kai a Kalashnikov, inda kuma ya zauna a gidan wanda ya kashe na tsawon makonni.
- Burak K, mai shekara 24, an yanke masa ɗaurin shekara 20 saboda kai ziyara gidan wanda aka kashen jim kaɗan bayan kai harin.
- Adam M, wanda ya amsa cewa ya samar da bindiga kan €500, ya musanta sanin abin da maharin zai yi da ita ba, inda aka yanke masa ɗaurin rai-da-rai.
- Ishaq F, mai shekara 22, wanda aka kai gidan yari da Fejzulai sannan yana sane da batun harin, an yanke masa ɗaurin shekara 19.
Sai dai, dukkan mutanen na da damar ɗaukaka kara.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin kimanin shekara 40, birnin Vienna ya tsira daga munanan hare-hare irin waɗanda suka lalata wurare a biranen Turai kamar Paris da Landa da kuma Berlin.
Hakan ya sauya a ranar 2 ga watan Nuwamba, lokacin da ɗan bindigar ya kaddamar da wani mummunan hari a birnin Vienna.
Yankin mai cike da hada-hada da tituna, wuri ne da ke ɗauke da wata tsohuwar coci mai suna St Ruprecht da kuma manyan wuraren ibada har da na yahudawa wanda ya yi nasarar kauce wa wani shiri da ‘yan Nazi suka yi kansu a 1938.
Wurin da aka kai harin yana kasancewa fayau da rana, amma cike da hada-hada da daddare.
An fara harbin ne da misalin karfe 8 na dare wanda lokacin yammaci ne da mutane ke ta nishaɗi gabanin saka dokar kullen korona a ƙasar ta Austria.
Bayan faruwar lamarin, an ga wani shagon sayar da abinci cike da jini a washegari.
Wani mutum da ya zo cin abincin daren ya kwatanta yadda shi da matarsa suka samu mafaka a wani wuri lokacin da aka fara harbe-harben.
An soki ministan harkokin cikin gidada gaza bin diddigin ɗan bindigar duk da cewa an sanar musu kan faruwar lamarin.
Gwamnatin ƙasar wadda ta amsa laifin rashin dakile harin, daga baya ta kawo wata tsatssaurar doka da ta sha suka, wadda ta bayar da damar ƙara sanya ido da kuma sabon hukunci kan waɗanda suka kai hari kan wuraren ibada.
Alkalai da kungiyoyin kare hakkin ɗan adam da kuma bangaren ‘yan adawa, duka sun soki dokar.











