Matsaloli biyar da sabuwar haɗakar ADC ke fuskanta

Asalin hoton, X/Multiple
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Tun bayan sanar da sabuwar haɗakar ADC ta ƴan hamayya a Najeriya, jam'iyyar ke fama da tarin matsaloli na cikin gida da kuma adawa daga sauran jam'iyyu.
A baya-bayan nan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu ya zargi jam'iyyar da yunƙurin tabbatar da ɗan arewa a matsayin shugaban ƙasa.
Zargin da ADC ta yi watsi da shi, tare da bayyana shi a matsayin bi-ta-da ƙullin APC.
A farkon watan Yuli ne wasu jiga-jigan siyasar Najeriya suka dunƙule a wuri guda da nufin ƙalubalantar jam'iyyar APC a zaɓen 2027.
Ƴansiyasar waɗanda suka fito daga manyan jam'iyyun ƙasar uku - APC mai mulki da PDP da LP masu hamayya - sun zaɓi jam'iyyar ADC ne sakamakon abin da suka kira jan ƙafa da hukumar zaɓen ƙasar ke yi wajen yi wa sabuwar jam'iyyarsu rajista.
Sai dai da alama tsugune ba ta ƙarewa sabuwar tafiyar ba, sakamakon wasu matsaloli da masana ke ganin na yi wa sabuwar tafiyar tarnaƙi.
Waɗanne matsaloli ADC ke fama da su?
Akwai wasu matsaloli aƙalla guda biyar da jam'iyyar ke fuskanta, kamar yadda Farfesa Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya ya bayyana.
Ya ce matsawar jam'iyyar ba ta yi ƙoƙarin magance matsalolin ba, za su iya kawo mata cikas a babbar manufar kafata, wanda shi ne kawar da APC daga mulki a 2027.
Rikicin Shugabanci

Asalin hoton, Social Media/David Mark
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 2 ga watan Yuli ne tsohon shugaban jam'iyyar ADC, kuma wanda ya kafa ta, Ralph Nwosu, ya sanar da rushe jagorancin jam'iyyar domin bai wa sabbin ƴan hamayya da suka shiga jam'iyyar dama.
Lamarin da ya bai wa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata David Mark damar zama sabon shugaban jam'iyyar haɗakar ta ADC.
To sai dai aƙalla wata guda bayan haka sai aka jiyo tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ta ADC, Nafi'u Bala na ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar haɗakar.
Yayin wani taron manema labarai a Abuja a ƙarsen watan Yuli, Nafi'u ya zargi, Sanata David mark da ƙwace ragamar jagorancin jam'iyyar da kuma yi wa kundin tsarin jam'iyyar karan tsaye.
Nafi'u Bala ya kuma sha alwashin ƙalubalantar al'amarin da ya bayyana da "juyin mulkin siyasa ido biyu daga baƙi" a gaban kuliya.
Farfesa Kari ya ce idan aka tafi a haka haɗakar za ta iya samun matsala.
''Saboda akwai barazanar wannan matsala za ta iya wargaza haɗakar'', in ji shi.
Raba ƙafa

Asalin hoton, Mansur Ahmed/Facebook
Akwai mambobin haɗakar da har yanzu suka ƙi amincewa su fice daga jam'iyyunsu, wani abu da Farfesa Kari ya ce zai iya zame wa jam'iyyar matsala.
Masanin siyasar ya ce batun raba ƙafa wata matsala ce da za ta yi wa jam'iyyar illa.
''Waɗanda suƙa ƙi ficewa daga jam'iyyunsu sun yi hakan ne saboda fargabar da suke da ita game da makomar jam'iyyar'', in ji shi.
Peter Obi da Sule Lamido na daga cikin jiga-jigan haɗakar da har yanzu suka ƙi amincewa su fice daga jam'iyyunsu.
Ko a makon da ya gabata ma, an jiyo tsohon gwamnan na jihar Jigawa na cewa tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da ya yi wa PDP takara a 2027.
Farfesa Kari ya ce idan Jonathan ya amince zai yi takara a PDP to ba shakka wasu mambobin ADC za su sauya ra'ayi zuwa wajensa.
''Ko da ma ba su yi hakan ba, takarar Jonathan ka iya zama ƙafar ungulu ga ADC, domin idan ya tsaya takara, burin ADC na samun magoya baya a yankunan kudu maso kudanci da kudu maso gabashi zai fuskanci cikas'', in j shi.
Hamayya daga manyan jam'iyyu uku
Galibi jiga-jigan ADC sun fito ne daga manyan jam'iyyun ƙasar uku APC mai mulki da PDP da LP masu hammaya.
Hakan ne ya sa jam'iyyar ke fuskantar suka da hamayya daga ɓangarori uku, wataƙila saboda haushin ficewar jiga-jigan jam'iyyun uku tare da komawa cikin ADC.
Farfesa Kari ya ce jam'iyyun uku na adawa ne da ADC ne saboda yadda suka rasa manyan ƙusoshinsu da suka koma haɗakar, don haka ba za su so ta ba.
''Saboda haɗakar za ta iya yi musu rauni da rage musu magoya baya, za ma ta iya ɗaiɗaita su, musamman PDP ta LP saboda yadda suka rasa manyan jiga-jigai'', in ji masanin siyasar.
Ya ƙara da cewa jam'iyyun za su yi duk mai yiwuwa don ganin haɗakar ba ta samu nasara ba.
'Zargin APC da kitsa rikicin jam'iyyar'

Asalin hoton, ADC/APC
A baya-bayan nan ne kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da yunƙurin jefa saɓani cikin ADC.
A yayin wata hira da gidan Talbijin na Channels, Bolaji ya ce ADC na sane da ''ƙafar ungulu da APC ke yi wa haɗakar tasu, kuma ba za su bari ta samu nasara ba.
Farfesa Kari ya ce wannan zargi ka iya zama gaskiya, domin akwai wasu alamu da ke nuna hakan.
"Akwai zuga da maƙarƙashiya da wasu ke yi, wanda kuma za a iya cewa suna yi wa jam'iyyar APC aiki ne'', in ji shi.
Jam'iyyar APC dai ta sha musanta wannan zargi, tana mai cewa babu ruwanta da batun wasu jam'iyyu.
Wanda zai yi mata takara a 2027

Asalin hoton, Atiku/Amaechi/Obi/X
Farfesa Abubakar Kari ya ce wata matsala da haɗakar za ta fuskanta a nan gaba ita ce batun wanda zai yi mata taraka a 2027.
Haɗakar ADC cike take da hamshaƙan ƴansiyasa masu burin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, kamar yadda malamin jami'ar ya bayyana.
Farfesa Kari ya ce akwai mutum huɗu a cikin haɗakar da kowannensu ke da burin yin takara.
Kawo yanzu dai akwai ƴan haɗakar da suka bayyana aniyarsu ta yi mata takara a zaɓen 2027, kamar peter Obi da Rotimo Amaechi, kuma wasu na ganin da wuya Atiku Abukakar bai yi takara a jam'iyyar ba.
''Yadda za ta fitar da ƴan takara da abubuwan da za su biyo bayan zaɓen fitar da gwanin, na tabbacin ci gaba da zama a jam'iyyar ga waɗanda ba su samu takarar ba da yadda za ta ɗinke ɓarakar, duk abubuwa ne da za su iya sauya haɗin kan jam'iyyar'', kamar yadda Farfesa Kari ya yi ƙarin haske.

Asalin hoton, Atiku/X
Zaɓen 2027 dai zai kasance ɗaya daga cikin mafiya ɗaukar hankali a siyasar Najeriya, kasancewar yadda haɗakar ADC ta fito, ƙunshe da jiga-jigan siyasar ƙasar.
Masana na ganin cewa dole ne jam'iyyar ta yi duk mai yiwuwa domin magance waɗannan matsaloli da take fuskanta, idan har tana son ɗorewa.
Farfesa Kari ya ce dole ne manyan hamshaƙan tafiyar su haɗiye maitarsu, su fifita tsarin dimokraɗiyya.
''Idan aka yi zaɓen fitar da gwani wanda ya faɗi ya goyi bayan wanda ya yi nasara''.










