Yara dubu 250 a Zamfara na fama da tamowa - Unicef

Zamfara

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Asusun kula da ilimin ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce akwai yara dubu 250 da ke fama da matsananciyar yunwa daga cikin yara miliyan 1.2 da aka yi nazari a kansu a jihar Zamfara.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa wakiliyar asusun na Unicef, Cristian Munduate ce ta faɗi hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Gusau na jihar ta Zamfara ranar Wednesday.

Misis Munduate ta ce a duk yara 10 da ke jihar ɗaya na fuskantar barazanar mutuwa inda kuma yawan yaran da ke fama da matsalar girma ƴan wata ɗaya zuwa shekaru biyar na ƙaruwa inda suka kai kaso 45.2 cikin 1000.

"Muna ƙoƙarin magance matsalar da shafar miliyoyin yara a jihar Zamfara da ma faɗin Najeriya. Kimanin yara miliyan 5.4 ƴan ƙasa da shekara biyar a arewa maso yammaci da gabashin Najeriya na fama da matsananciyar tamowa inda kuma ake hasashen alƙaluman ka iya ƙaruwa da miliyan guda ya zuwa watan Afrilun 2025." In ji Munduate.

Ta ƙara da cewa mace-macen jarirai ƴanƙasa da wata ɗaya ya kai yara 42 a duk cikin haihuwa 1,000.

Misis Munduate ta kuma ce kaso 21.5 na masu ciki ne kawai suke zuwa awo aƙalla sau huɗu sannan kaso 15 ne cikin 100 na mata ke haihuwa a asibiti.

Wakiliyar ta UNICEF ta kuma bayyana cewa fiye da yara 700,000 kwatankwacin kaso 62 ba sa zuwa makaranta, inda kaso 60 na yara mata ke fuskantar auren dole wani abu da ke ƙara talauci a tsakaninsu.

Dangane kuma da rijistar haihuwa, misis Munduate ta ce rijistar jariri ta ƙaranta a jihar inda ake yi wa kaso 31.4 kawai rijistar haihuwa wani abu da ke sa a kasa sanin yawan yaran.

Yayin taron manema labaran, misis Munduate ta ce kaso 47 na yara a jihar ta Zamfara na zama a hannun mutanen ko kuma iyayen da ke fama da talauci, sannan kuma kaso 67 na fama da matsanancin talauci.

Hakan ya sa ta ce ana buƙatar dala miliyan 250 wajen warware matsalar a jihohin Najeriya da suka haɗa da Sokoto da Zamfara da Katsina.

"Muna kira da gwamnatocin jihohi biyu na Zamfara da Sokoto da su magance wannan matsala. Muna kuma yin kira ga dukkannin gwamnatoci da su faɗaɗa fannin lafiya a dukkan matakai." In ji ta.