Wane ne zai ja ragamar tsaro a Gaza bayan kammala yaƙi?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Salma Khattab
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Aiko rahoto daga, Cairo
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin neman zaman lafiya a zirin Gaza, gwamnatin Isra'ila ta amince da wani shiri na faɗaɗa samamen soji da take yi a zirin domin mamaye shi baki ɗaya.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar cewa burinsa shi ne sojojin ƙasar su kame iko da baki dayan Gaza.
A ƙarƙashin shirin, dakarunsu za su gama da mayaƙan Hamas gaba ɗaya, sai kuma su miƙa ikon yankin ga dakarun ƙasashen Larabawa bisa sa'idon Amurka.
Shirin na Netanyahu na samun goyon bayan 'yansiyasa masu tsattsauran ra'ayi. Amma kuma iyalan mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza sun soki shirin, da kuma ƙasashen duniya da yawa.
Dakarun tsaro na ƙasashen waje
Maganar mayar da ikon Gaza hannun dakarun ƙasar waje ba sabon abu ba ne.
Ƙasashen Larabawa sun yi watsi da tayin a ƙarshen 2023. Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya ce: "Babu wasu dakarun Larabawa da za su je Gaza. Ko kaɗana. Ba za mu je a dinga yi mana kallon maƙiya ba."
Tsohon jami'in difilomasiyyar Isra'ila Alon Pinkas, wanda a yanzu marubuci ne a jaridar Haaretz ta Isra'ila, ya faɗa wa BBC cewa "babu wata ƙasar Larabwa da za ta so ta shiga lamarin sai dai idan hukumar Falasɗinawa ta Palestinian Authority (PA) ce ta nemi ta yi hakan".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar PA ta ƙi amincewa da shirin raba ikon Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, wanda take iko da shi, da kuma Gaza.
Ta ce Gaza wani muhimmin ɓangare ne na ƙasar Falasɗinu da suke son kafawa kuma haƙƙinta ne kula da tsaronsa.
A watan Afrilun da ya gabata, Masar da Jordan sun amince da wani tsarin sake gina Gaza, wanda zai ƙunshi bai wa 'yansandan Falasɗinawa horo domin aika su cikin Gazan.
A makon nan kuma, Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya ce Masar ta fara aiwatar da shirin horar da 'yansandan PA 5,000 da za a tura Gaza bayan gama yaƙin.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), kusan kashi 87 cikin 100 na zirin ya zama filin yaƙi wanda dakarun Isra'ila ke umartar Falasɗinawa su fice daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu Ma'an ya ruwaito cewa "tattaunawar da ake yi a yanzu ta ƙunshi tsagaita wuta da kuma janyewar sojojin Isra'ila daga yankin da kuma shigar sojojin Larabawa bisa sa'idon Amurka".
Rahoton ya ce "za a naɗa gwamna Bafalasɗine da zai kula da harkokin mulki da kuma tsaron Gaza, har ma da shirin sake gina Gaza".
Babu cikakkun bayanai game da ƙasashen da za su tura dakarun da kuma ko Isra'ial da Hamas za su amince da hakan.

Asalin hoton, EPA
'Cukumurɗa ta tsaro'
Shirin na tura dakarun Larabawa zuwa Gaza "shi ne abin da ake kallon zai iya yiwuwa amma ba abu ne mai sauƙi ba," a cewar tsohon jami'in kula da harkokin Gabas ta Tsakiya a Birtaniya Alistair Burt.
Burt na ganin idan ana so a cimma wannan matsayar to dole ne a "a ƙulla cikakkiyar yarjejeniya" da Hamas da Isra'ila da sauran ƙasashe kafin a tura dakarun.
"Ba na jin akwai wata ƙasar Larabwa da za ta yi hakan. Me ya sa za su jefa dakarunsu cikin haɗari? Dole ne a samu cikakkiyar yarjejeniya kan tsaro," in ji shi.

Asalin hoton, EPA
Burt ya ce harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba zai ta'azzara fargabar da Isra'ila ke yi game da tsaronta a nan gaba. Harin ya jawo kisan aƙalla Isra'ilawa 1,200 da kuma sace wasu 251 zuwa cikin Gaza.
"Isra'ila na kallon harin 7 ga watan Oktoba a matsayin babban al'amari. Idan dakarun sojin Isra'ila ba za su ci gaba da zama a can ba, wane ne zai tabbatar da tsaron Isra'ila, kuma dole ne ƙasashe su amsa wannan tambayar."
Burt ya siffanta matsalar tsaron Gaza da "cukumurɗa", yana mai cewa "cike take da bindigogi, da gungu-gungu, da kuma kuɗin haram".

Asalin hoton, Mohammed Saber / EPA
Buƙatar ƙwace makaman Hamas
Shugaban cibiyar nazarin harkokin Larabawa ta Arab institute of Strategic Studies, Samir Ragheb, ya faɗa wa BBC News Arabic cewa "idan ana so a tura dakarun Larabawa Gaza to dole ne sai Hamas ta ajiye makamanta".
Ragheb ya ce babu ƙasar Larabawa da ta nuna sha'awar yin hakan.
Sai dai ministan harkokin waje na Masar ya faɗa a makon nan cewa ƙasarsa ba zat yi adawa da wani shirin tura dakarun ƙasashen waje Gaza ba - idan har za a bai wa PA damar jagorantar yankin.
Amma Ragheb ya yi gargadi: "Hamas ba za ta amince da wannan shawarar ba, sai dai idan an cimma yarjejeniyar ficewar baki dayan dakarun Isra'ila daga zirin. Saboda amincewa da hakan tamkar ƙwace makaman Hamas ne.
"Hakan na nufin Hamas ba za ta sake iko da Gaza ba, kuma masu shiga tsakani na yunƙurin maye gurbinta har zuwa lokacin da dakarun hukumar PA za su karɓi aikin tsaron."

Asalin hoton, EPA
Tattaunawa a Alƙahira

Asalin hoton, Reuters
A ranar Laraba ne wata tawagar Hamas ta isa birnin Alƙahira na Masar domin tattaunawa da masu shiga tsakani.
Dare ɗaya kafin haka, ministan harkokin waje na Masar ya ce manyan mutane 15 da ba su bin wani ɓangaren siyasa a Falasɗinu sun ce a shirye suke su jagoranci mulkin Gaza tsawon wata shida bayan yaƙin.
Hukumar PA za ta karɓi ikon Gaza bayan haka a ƙarƙashin shirin. "Abin da muka sa a gaba yanzu shi ne dawo da batun teburin tattaunawa," in ji shi.
Mai sharhi a jaridar Haaretz ta Isra'ila, Gideon Levy ya ce: " Babu wata ƙasar Larabawa da za ta jefa dakarunta cikin haɗari a Gaza.
"Zai zama babban bala'i gare su kuma ba abu ne da za a iya cikawa ba ko da an yi alƙawari."

Asalin hoton, Mohammed Saber / EPA
Daftarin Witkoff

Asalin hoton, EPA
Daftarin da wakilin Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff ya gabatar ya ƙunshi tsagaita wuta na kwana 60, inda a lokacin Hamas za ta saki Isra'ilawa tara da gawar mutum 18.
Ya kuma ƙunshi matakai biyu a cikin mako ɗaya, a madadin haka dakarun Isra'ila za su fice daga kwararon Netzarim da ke Gaza.
Za a yi ta tattaunawa a daidai wannan lokacin domin kawo ƙarshen yaƙin. Idan ba a cimma wata matsaya ba Isra'ila za ta iya cigababa da yaƙi, ko kuma tattaunawa a madadin sakin ƙarin wasu mutanenta.

Asalin hoton, Mohammed Saber / EPA






