Abu huɗu da suka kamata ku sani game da zaɓen jihar Ondo

Duka manyan 'yan takara biyu a zaɓen, tsoffin mataimakan tsohon gwamnan jihar, marigayi Rotimi Akeredolu ne.
Lokacin karatu: Minti 4

A yau Asabar ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Jihar Ondo na daga cikin jihohin ƙasar da ba a gudanar da zaɓukansu lokaci guda da na sauran jihohi.

Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta ce mutum miliyan 2,053,061 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, yayin da matasa ke da kashi 35.41 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar zaɓen.

Ga wasu abubuwa guda huɗu da suka kamata ku sani dangane da zaɓen na jihar Ondo na yau Asabar.

1) Ondo na cikin jihohi takwas da ake zaɓensu daban

Jihar Ondon na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya takwas da ake gudanar da zaɓensu ba tare da sauran jihohin ƙasar ba. Jihar Ondo ta tsinci kanta a tsakanin sauran jihohin da ba sa zaɓen ne a shekarar 2007.

A zaɓen gwamnan jihar na 2007 wanda fafatawar ta fi zafi tsakanin Olusegun Agagu na PDP da Olusegun Mimiko na Labour Party waɗanda a baya abokan juna ne.

An Olushegun Aganga ya kayar da Olusegun Mimiko kuma bayan rantsar da Aganga ne sai Mimiko ya je kotu inda a ranar 25 ga watan Yulin 2008 kotun ta ayyana cewa Mimiko ne ya ci zaɓen ba Agagu ba.

2) Rasuwar Gwamna Rotimi

Ya rasu yana da shekara 67, bayan ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da ta mafitsara.

Asalin hoton, ROTIMI AKEREDELU/FACEBOOK

Zaɓen na jihar Ondo dai na zuwa ne wata 11 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, wanda ya shafe tsawon lokaci yana fama da jinya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan ya rubuta wasikar tafiya jinya, inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kafin sannan, an yi ta dambarwar siyasa a jihar Ondo, a kan yunƙurin tsige mataimakin gwamnan daga kujerarsa, amma daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani.

Gwamnan dai ya shafe kusan wata uku a ƙasar Jamus yana jinya, daga bisani ya koma Najeriya a watan Satumba.

Sama da wata biyu bayan komawar Rotimi Akeredolu daga tafiyar jinyarsa ta farko, ba a iya ganinsa a bainar jama'a ba.

Da ya koma ɗin kuma, ya aika wa majalisar dokokin jihar wasiƙa, inda ya sake neman ƙarin hutun jinya a ranar 15 ga watan Yuli.

Yayin da rashin lafiyarsa ya tsananta, Gwamna Akeredolu ya fuskanci matsin lambar neman ya yi murabus ko ya miƙa harkokin mulki ga mataimakinsa, daga jam'iyyun adawa da 'yan fafutuka, kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

A watan Oktoba, majalisar dokokin jihar ta rubuta wa alƙalin alƙalan Ondo wasiƙa, inda ta sake neman ya kafa kwamitin da zai binciki Lucky Aiyedatiwa a kan zarge-zargen aikata ba daidai ba. Mataimakin gwamnan ya garzaya kotu inda ya fara ƙalubalantar ƙoƙarin raba shi da muƙaminsa.

3) Mataimakan gwamnan biyu na fafatawa

An haifi Lucky Aiyedatiwa a garin Obe-Nla na yankin ƙaramar hukumar Ilaje ranar 12 ga watan Janairun 1965.

Asalin hoton, @LuckyAiyedatiwa/X

Bayanan hoto, Lucky Aiyedatiwa na APC

Duka manyan 'yan takara biyu a zaɓen, tsoffin mataimakan tsohon gwamnan jihar, marigayi Rotimi Akeredolu ne.

Agboola Ajayi na jam'iyyar PDP da Lucky Aiyedatiwa na APC mai mulkin jihar sun yi wa marigayi Akeredolu mataimaki a wa'adin mulki daban-daban.

Ajayi ne ya fara yi masa mataimaki a wa'adin mulkinsa na farko daga 2016 kafin wani saɓani ya shiga tsakaninsu a 2020.

Lamarin da ya sa suka raba gari a 2020, inda har Ajayi ya tsaya takara a zaɓen 2020 a jam'iyyar hamayya ta ZLP.

Bayan samun saɓani tsakanin Akeredolu da Ajayi a 2020, a wa'adinsa na biyu ya ɗauki Aiyedatiwa a matsayin mataimaki.

Daga baya kuma Aiyedatiwa shi ma ya riƙa samun saɓani da Akeredolu a lokacin rashin lafiyarsa, lamarin da har ta kai ga fadar shugaban ƙasa kiran duka ɓangarorin biyu domin yi musu sulhu.

Shi ne tsohon mataimakin Akeredolu a wa'adin farko, kafin daga baya ya koma jam'iyyar ZLP bayan tsamin dangantaka da ubangidan nasa.

Asalin hoton, @A_AgboolaAjayi/x

Bayanan hoto, Agboola Ajayi na PDP

4) Jam'iyyu 18 ke fafatawa

Ƴantakara 18 ne fafatawa a wannan takara kuma ga sunansu kamar haka:

  • Lucky Aiyedatiwa na APC
  • Agboola Ajayi na PDP
  • Sola Ebiseni na LP
  • Abbas Mimiko na ZLP
  • Falaiye Abraham Ajibola - A
  • Akinuli Fred Omolere - AA
  • Ajayi Adekunle Oluwaseyi - AAC
  • Nejo Adeyemi - ADC
  • Akinnodi Ayodeji Emmanuel - ADP
  • Popoolqa Olatunji Tunde - APGA
  • Ogunfeyimi Isaac Kolawole - APM
  • Fadoju Amos Babatunde - APP
  • Olugbemiga Omogbemi Edema - NNPP
  • Ajaunoko Funmilayo Jenyo - NRM
  • Alli Babatunde Francis - PRP
  • Akingboye Benson Bamidele - SDP
  • Adegoke Kehinde Paul - YP
  • Akinmurele John Otitoloju - YPP