Thiago Silva zai koma Fluminese daga Chelsea

Tuni dai Chelsea ta tabbatar cewar Thiago Silva zai bar Stamford Bridge da zarar an kammala kakar bana, zai koma kungiyar Fluminese ta Brazil.

Mai shekara 39 ya buga wa Chelsea wasa sama da 150 da lashe Champions League da FIFA Club World Cup da kuma UEFA Super Cup.

Chelsea ta amince dan wasan ya yi atisaye tare da Fluminense, kafin kwantiraginsa ya kare a farkon watan Yuli, wanda ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyu.

Silva mai shekara 39 ya koma Chelsea a lokacin da Frank Lampard ke kociyan kungiyar, ya kuma taka leda karkashin Thomas Tuchel da Graham Potter da kuma Mauricio Pochettino.

Ya buga wasa 34 a dukkan karawa a kakar nan a Chelsea a bana har da wasa 25 da aka fara da shi a Premier League.

Tsohon dan wasan AC Milan ya buga wa tawagar Brazil wasa 113, ya ce yana fatan sake komawa Stamford Bridge, domin yin wani aikin na daban.

Chelsea, wadda take ta bakwai a teburin Premier League ta doke West Ham 5-0 ranar Lahadi a gasar mako na 36.

Wasa uku ya rage a gaban Chelsea a Premier League:

Premier League Asabar 11 ga watan Mayu

  • Nottm Forest da Chelsea

Premier Leagu Laraba 15 ga watan Mayu

  • Brighton da Chelsea

Premier League Lahadi 19 ga watan Mayu

  • Chelsea da Bournemouth