Koriya ta Arewa: Harba makamai masu linzami 10 ya razana makwabtanta

File photo of a North Korean missile test

Asalin hoton, Getty Images

Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami, wanda ya ratsa sararain samaniyar makwabciyarta Koriya ta Kudu.

Wannan ne karon farko da wani makami irin wannan ya ratsa kan iyakar kasashen biyu tun bayan da aka raba kasar gida biyu.

Wannan makamin mai gajeren zango ne, kuma ya fada cikin tekun da ke kusa da gabar tekun Koriya ta Kudu daf da wani tsibiri mai suna Ulleungdo.

Jami'an gwamantin Koriya ta Kudun sun ce makamai 10 aka harba da safiyar ranar Laraban nan.

Nan take gwamantocin Japan da na Koriya ta Kudu suka soki matakin makwabciyar ta su na harba makaman - wadanda suka auku gabanin karfe 9 na safe, wato karfe 12n dare agogon GMT.

Kuma shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol ya kira wani taron gaggawa da manyan jami'an tsaron kasar domin tattauna batun.

Koriya ta Arewa ta harba wadannan makama masu linzai ne bayan da ta gargadi Amurka da Koriya ta Kudu da su daina gudanar da wani atisayen da sojojinsu ke yi a yankin.