BBC Hausa@67: 'Na zama shugaban sashen Hausa duk da ba na jin harshen sosai'

Graham

A yau 13 ga watan Maris ne sashen Hausa na BBC ke cika shekaru 67 da fara watsa shirye-shirye da harshen Hausa a fadin duniya.

Albarkacin wannan rana, shugaban sashen na yanzu, Aliyu Abdullahi Tanko ya tattauna da Dr Graham Mytton, mutum na hudu a jerin shugabannin sashen na Hausa.

Wane ne Graham Mytton?

"Sunana Graham Mytton, ni ne tsohon shugaban sashen Hausa na BBC. Na gai da ma’aikatan sashen Haysa na BBC.

An nada ni ina tunanin a watan Disamba ne na shekarar 1976, kuma na karkare zama da sashin bayan shekaru shida, ina tunanin a watan Satumbar skekarar 1982 lokacin da na tafi gudanar da aikin bincike kan masu saurare.

Na yi shekaru shida cif-cif da sashen hausa na BBC.

Na karbi jagoranci daga wani mutum da ake kira Bill Everingham wanda ya kwashe shekaru da dama yana tsara shirye-shirye a harshen Turanci kadai, kafin ya zama mai gudanar da shirye-shirye a sashen Hausa duk da cewa kwata-kwata ba ya jin Hausa.

Ni ma ba na jin Hausa amma na koyi wadatacciyar da ta ba ni damar sanin abin da ke wakana." In ji Dr Graham Mytton.

Dr Graham Mytton ya kuma yi karin bayani dangane da wasu shugabannin na sashen Hausa na BBC kamar Bill Everigham da Chris Falmer.

Wane ne Chris Falmer?

Dr Graham Mytton ya yi karin haske dangane da Chris Farmer kamar haka:

"Shi ne mutum na farko da ya fara rike mukamin mai gudanar da shirye-shirye a sashen Hausa na BBC mukamin da ake kira 'Program organizer' da Turanci.

An samu wasu da suka gabace shi wajen jagorantar sashen kuma babu wanda a cikinsu yake jin Hausa.

Chris Farmer, tsohon ma’aikacin Turawan mulkin mallaka ne. Ba ni da tabbacin mukamin da ya rike amma dai ya yi aiki a arewacin Najeriya kuma ya san yankin sosai sannan kuma yana magana da harshen Hausa da kyau.

Ya ci gaba da aikin nasa har zuwa wuraren shekarun 1970, ba ni da tabbacin hakikanin shekarar amma dai ina ganin har zuwa 1974, lokacin da ya zama babban mai kula da ma’aikata a sashen BBC mai yada shirye-shiryensa a duniya.

Amma ya ci gaba da nuna sha’awarsa ga sashen Hausa, inda yake ziyarar mu tunda yana jin Hausa sosai." In ji Graham Mytton.

Bill Everigham

Dr Graham Mytton ya yi bayani kan Bill Everigham wanda ya ce ba ya jin Hausa kwata-kwata.

"Duk da cewa Bill Everigham ba ya jin Hausa amma yana da mataimaki wanda mai tsara shirye-shirye ne mai suna David Warren.

Shi ma Dvaid Warren ya kasance tsohon ma’aikacin gwamnatin mulkin mallaka ne a arewacin Najeriya kuma yana jin harshen Hausa kwarai da gaske.

Lokaci zuwa lokaci yana watsa shirye-shirye sannan ma ya kan karanta labarai. Ba na tsammanin yana raye.

Shi ake tunanin za a nada shugaban sashen na Hausa amma kuma sai aka nada ni a maimakonsa." In ji Graham.

Yawan ma'aikatan sashen Hausa a farko-farko

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Graham wanda ya jagoranci sashen na Hausa na BBC a shekarar 1976 zuwa 1982, ya ce zai iya tuna sunayen wasu daga cikin ma'aikatan na sashen Hausa kamar haka:

"A lokacin ina tsammanin muna da ma’aikata guda takwas. Zan iya tuna sunayen wasunsu daga ciki kamar Saleh Aliyu Hadejia da Halilu Getso da Yahaya Musa da Yunusa Ibrahim.

Wani babban ma’aikaci a wannan lokaci shi ne mataimakina mai suna Barry Burgess wanda kamar yadda ka sani yake magana da harshen Hausa watakila fiye da duk wani dan Ingila ko kuma dan Burtaniya.

Sai dai kuma abin takaici ba ya raye ya rasu kimanin shekaru hudu da suka gabata."

Dangane kuma da babban labarin da Dr Graham zai iya tunawa sun yi a lokacin shi ne na kama mulkin Alhaji Shehu Shagari a matsayin zababben shugaban Najeriya.

"Zamanina kusan duk lokacin mulkin sojoji ne har zuwa karshe-karshe lokacin da aka koma mulkin dimokradiyya inda Sshehu Shagari zai zama shugaban Najeriya. Mun yi hira da shi. Yunusa Ibrahim ne ya tattauna da shi." In ji Dr Graham.

Jerin sunayen shugabannin sashen Hausa na BBC

  • John Massingham: 1957 - 1965
  • Chris Farmer: 1965 - 1974
  • Bill Everringham: 1974 - 1976
  • Dr Graham Mytton: 1976 -1982
  • Barry Burgess: 1982 - 1998
  • Carlos Araujo: 1998 - 1999
  • Isa Abba Adamu: 1999 - 2005
  • Jamila Tangaza: 2005 - 2011
  • Dr Mansur Liman: 2011 - 2016
  • Jimeh Saleh: 2016 - 2019
  • Aliyu Tanko: 2019 - zuwa yau