Mai kyautar littattafai da jana'izar tsohon shugaban Ivory Coast
Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya

Asalin hoton, AMANUEL SILESHI/AFP
Yayin da ake daf da fara wasannin gasar Olympic ta 2024 a Paris, tuni masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na ƙasar Habasha suka fara atisaye a Addis Ababa, babban birnin ƙasar a ranar Asabar.

Asalin hoton, SAYED HASSAN/GETTY IMAGES
Wani mutum kenan ɗauke da wani bunsuru ranar Alhamis a kasuwar birnin Giza na ƙasar Habasha, inda ake shirye-shiryen babbar sallar layya.

Asalin hoton, ALAISTER RUSSELL/REUTERS
Yadda al'umma ke taruwa a bakin teku, inda ruwa ke taroƙo yana rufesu, yana komawa a birnin Durban na ƙasar Afirka ta Kudu a ranar Lahadi.

Asalin hoton, RAJESH JANTILAL/AFP
Lardin KwaZulu-Natal na gabashin Cape Varde na ƙasar Afirka ta Kudu inda aka fuskanci ambaliyar ruwa a ranar Talata sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.

Asalin hoton, GIANLUIGI GUERCIA/AFP
Fiye da mutum 20 ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwan. Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kenan suka fito suna wanke dattin da ambaliyar ta janyo a ranar Laraba.

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP
Wakilan sarkin Ashanti na Ghana kenan ɗauke da kayan al'adu a wajen bikin binne marigayi shugaban ƙasar Ivory Coast, Henri Konan Bédié wanda aka binne wata goma bayan mutuwarsa a ƙauyensu Pépressou dake gabashin ƙasar.

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP
Wakilai daga sassa daban daban na Afirka sun halarci taron domin girmama Bédié, wanda ya zama shugaban ƙasar Ivory Coast daga 1993 zuwa 1999, wanda aka yi masa juyin mulki.

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP
Hoton wanda ya yi shigar zaki a wajen wasan al'adu na da ake yi a bakin teku na birnin Dakar a ranar Laraba.

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP
A wajen taron na al'adu da ake yi bakin ruwa a Dakar kenan, inda aka gudanar da gasar tseren kwale-kwale.

Asalin hoton, BONIFACE MUTHONI/GETTY IMAGES
Wata yarinya ƴar shekara huɗu kenan a lokacin da za ta dasa icce a filin tsohon gidansu da ambaliyar ruwa ta mamaye a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.

Asalin hoton, KOLA SULAIMON/AFP
Ranar litinin kenan wasu ɗaliban Najeriya suka je makaranta suka samu an kulle sakamakon yajin aikin da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta yi, saboda neman ƙarin mafi ƙarancin albashi.

Asalin hoton, MOHAMED ABD EL GHANY/REUTERS
Mohamed Azzam kenan wani mutum a ƙasar Egypt da yake yawo da littafai a mota yana bai wa waɗanda ke wucewa domin ba su ƙwarin guiwar karance-karance.











