Pogba ya buga wasan farko cikin wata uku

Asalin hoton, Getty Images
Paul Pogba ya buga wasansa na farko tun watan Mayu yayin da Juventus ta yi kunnen doki a gidan Bologna a gasar Seria A.
Dan wasan Scotland Lewis Ferguson ne ya ci wa Bologna, kafin Dusan Vlahovic ya farke ana saura minti 10.
Tsohon dan wasan Manchester United, Pogba ya koma Turin a bazarar da ta wuce bayan ya shafe shekaru shida a Ingila, amma ya buga minti 161 kacal a kakar wasan da ta wuce.
Ya yi fama da raunuka da suka hada da tiyatar da aka yi masa a gwiwa wadda ta kawo wa dan wasan cikas kuma ta hana Bafaranshen mai shekaru 30 damar buga gasar cin kofin duniya.
An canja Pogba ne bayan minti 24 a karawar da suka yi da Cremonese a wasansa na karshe a Juventus ranar 14 ga Mayu - wanda shine wasansa na farko cikin sama da shekara daya kuma na farko tun bayan dawowarsa daga Old Trafford.
Bai buga wasannin share fage na tunkarar kakar wasa ta bana ba, kuma ya kasance wanda ba a yi amfani da shi ba a wasan farko da Juventus ta doke Udinese, amma ya sami daman buga minti 24 daga benci a wasan da suka yi canjaras a ranar Lahadi.







