Abin da ƙwararru ke cewa game da hukuncin zaɓen gwamnan Kaduna

Masana shari’a na ci gaba da tsokaci game da ruɗanin da aka samu a kan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kaduna.

Alƙalan kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Victor Oviawe sun sanar da hukuncin da suka yanke ne ranar Alhamis, inda dukkan lauyoyin bangaren jam’iyyar APC mai mulki, da na PDP mai adawa suka yi ikirarin samun nasara.

Mutane da yawa sun bayyana cewa hukuncin yana cike da ruɗani. Lauyoyin kowanne ɓangare sun yi iƙirarin nasara, yayin da duka 'yan takarar biyu suka fitar da sanarwar murna a kan nasarar da suka ce kotu ta ba su.

Sai dai, wasu lauyoyi kamar Barista Audu Bulama Bukarti na cewa bisa fahimtar da suka yi wa shari'a, babu wani ruɗani a hukuncin da alƙalan suka karanta ta manhajar Zoom.

"Kotu ta kori ƙarar Isa Ashiru bisa hujjar da lauyoyin APC da ɗan takararta Uba Sani suka kafa na cewa masu korafin sun gaza cika wata ƙa'idar doka a da'awar da suka yi," in ji Bukarti.

A cewarsa, bisa tanadin tsarin mulkin Najeriya, ko da ƙaramar kotu ta kori ƙara, to sai ta saurari shari'ar, saboda idan aka ɗaukaka ƙara, matakin zai sauƙaƙa wa kotun gaba aiki.

Ya ce a fahimtarsa lauyoyin APC sun yi suka ne kan da'awa uku da ɗan takarar PDP da jam'iyyarsa suka shigar.

"Lauyoyin APC sun nemi a kori shari'ar Isa Ashiru saboda bai shigar da ita a kan lokaci ba, saboda a tanadin kundin zaɓe, duk wani mai ƙorafi yana da kwana 21 daga ranar da aka ayyana wanda ya ci zaɓe, ya shigar da ƙara.

"Sun ce mai ƙorafin bai shigar da ƙarar a cikin wannan wa'adi ba, amma dai kotu ta yanke hukuncin cewa Isa Ashiru ya shigar da ƙara a kan lokaci."

Sai kuma sukar da lauyoyin APC suka yi wa wasu daga cikin shaidun da ɗan takarar PDP ya gabatar a yayin zaman sauraron shari'ar, in ji Barista Bukarti.

"A nan kotun ta amince da buƙatar lauyoyin Uba Sani ta kori wasu shaidun da Isa Ashiru ya gabatar, bisa hujjar cewa ba su da inganci."

Haka kuma a cewarsa, kotu ta kori ƙarar Isa Ashiru saboda lauyoyin APC sun kafa hujja ga kotu cewa mai ƙorafin bai cika ƙa'idar da doka ta shimfida ba. "A cewarsu lauyoyin PDP ba su nemi pre-action notice ba."

Wannan dai, wata takarda ce ko wasiƙa da mai ƙara yake neman kotu ta bai wa wanda aka yi ƙara don sanar da shi cewa yana da niyyar neman haƙƙin da yake jin an take masa.

Ya ce bisa ƙa'idar dokokin Najeriya, idan kotu ta yanke hukuncin korar wata ƙara, bayan an soki da'awa, duk da haka kamata ya yi ta shiga cikin shari'ar ta duba shaidun kowanne ɓangare.

Bisa wannan hujja, idan aka ɗaukaka ƙara a kotun gaba, matuƙar kotun ƙasa ba ta yanke hukunci ba, to su kotunan gaba ba za su iya tabbatarwa ko su kore wani hukunci ba, matuƙar kotun ƙaramar kotu korar ƙara kawai ta yi, ba ta saurari shari'a ta yi hukunci ba.

A cewar Bulama Bukarti abin da kotun Kaduna ta yi kenan, cewa ta kori da'awa amma, da ba ta kori da'awar ba, ga yadda hukunci zai kasance:

"Hukuncin kuma shi ne ta gamsu da takardun da PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru suka gabatar cewa zaɓen Kaduna bai kammala ba, kamata ya yi a koma a yi zaɓe a tashoshin zaɓe 22 cikin kananan hukumomi 4.

"Amma wannan hukunci, cewa ta yi da ba ta kori da'awar ba. To, da ga hukuncin da za ta yi. Ka ga amma tun da ta kori da'awa, korar da'awa shi ne hukuncinta yanzu."

Ya ce idan aka ɗaukaka ƙara, kotun ɗaukaka ƙara da kuma Kotun Koli suka gamsu da korar da'awar da kotun ƙasa ta yi na cewa Isa Ashiru bai nemi sanarwar kafin fara shari'a a cikin kwana bakwai ba, to ba ma za su shiga cikin maganar hukuncin da kotun ƙasa ta yanke ba.

Amma idan ba su gamsu da korar ƙarar ba, to a nan ne za su shiga cikin hukuncin.

Masanin shari'ar ya ce a matakin da ake ciki yanzu matuƙar kowanne ɓangare bai ɗaukaka ƙara ba, tsakanin Sanata Uba Sani da Isa Ashiru, to Uba Sani ne zai ci gaba da zama gwamnan jihar Kaduna, har zuwa lokacin da wa'adin da tsarin mulki ya ƙayyade.

Ya ce bisa yadda al'amura suke a yanzu, Isa Ashiru ne ke da wajabcin ɗaukaka ƙara, amma idan bai yi ba, to bisa la'akari da hukuncin kotu, Uba Sani ne ya yi nasara.

Mataki na gaba 'Ya rage wa Isa Ashiru' - Uba Sani

Da yake magana, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da nasarar da ya samu ne a lokacin zaɓe, saboda a cewar sa zaɓe ne da aka gudanar cikin gaskiya da adalci.

"Mu da Allah ya bai wa nasara, da takwarana na PDP da bai yi nasara ba, dukkanmu mu sani cewa Allah ne ke ba da mulki. Ina son in jaddada wa mutanen Kaduna cewa za mu yi wa kowa adalci," in ji Uba Sani.

"Zuwa kotu da Isa Ashiru ya yi abu ne mai kyau, saboda a kotu ne za ka je ka nemi hakkinka."

Ya ce kafofin sada zumunta ne da kuma wasu mutane suka riƙa yaɗawa cewa Isa Ashiru ne ya yi nasara a kotun wanda kuma ya ce farfaganda ce kawai.

"Mu ba ma bin maganar jita-jita saboda kowa ya ji hukuncin da alkalai suka yanke. Ya rage ga Isa Ashiru na ya yi tawakalli ga Allah," in ji shi.

Gwamna Sani ya ce ba su da wata fargaba ko da ɗan takarar jam'iyyar ta PDP zai ɗaukaka ƙara a gaba.

Sanata Sani ya ƙara da cewa abin da suka mayar da hankali a yanzu shi ne ci gaba da cika alkawura da gwamnatinsa ta yi wa ƴan jihar Kaduna.

Shure-shure ba ya hana mutuwa - Isa Ashiru

Sai dai shi ma a martaninsa, Hon Isa Ashiru, ɗan takarar gwamnan jihar ta Kaduna karkashin jam'iyyar PDP, ya ce shure-shure ba ya hana mutuwa kuma nasara ta su ce.

Ya ce "Kotu ta ce Hukumar zaɓe ba ta yi daidai ba wajen bai wa Uba Sani takardar cin zaɓe."

"Biyu daga cikin alƙalan sun ce a janye satifiket ɗin sai an je an sake zaɓuka a wasu rumfuna na jihar Kaduna.

Ya ƙara da cewa "Mun bai wa lauyoyin mu su duba hukuncin da aka gabatar don sanin mataki na gaba da za mu ɗauka."

Ashiru ya ce ba kan raɗin kansa yake kalublantar sakamakon zaɓen ba, illa don al'ummar jihar Kaduna.

Ya ce za su duba hukuncin kotun idan bai yi musu ba za su dangana gaba saboda wannan matakin farko ne ake.

"Wannan batutuwan zaɓe da muke zuwa kotu, zan tabbatar muku ba don kaina nake yi ba, magana ce ta al'ummar jihar Kaduna."

Tun farko Isah Ashiru na jam’iyyar PDP ne ya shigar da ƙarar, inda ya yi zargin tafka maguɗi a zaɓensu na watan Maris.

Sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, ta fitar a watan Maris, ya nuna cewa Sanata Uba Sani na APC, ya samu ƙuri’a 730,002.

Yayin da Isa Ashiru na PDP ya tashi da ƙuri’a 719,194.