Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Uba Sani ya lashe zaɓen jihar Kaduna
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ayyana ɗan takarar APC Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Kaduna.
Bayan share sama da kwana biyu ana jiran sakamakon jihar, a ranar Litinin kuma aka kawo karamar hukuma ta ƙarshe, Kudan, wadda ɗan takarar PDP Isa Ashiru ya fito daga cikinta.
Sakamakon da hukumar zaben ta sanar ya nuna cewa APC ta samu kuri'a 730,002 - yayin da jam'iyyar PDP wadda ta zo ta biyu ta samu kuri'a 719,194.
Uba sani da ke jam'iyyar APC zai gaji gwamnan jihar na yanzu Malam Nasi El Rufa'i da wa'adinsa zai ƙare a watan Mayu. Hakan na nufin jam'iyyar APC mai mulki za ta ci gaba da jan ragamar jihar har zuwa nan da wasu shekaru huɗu masu zuwa.
Jihar Adamawa da Kebbi na daga cikin waɗanda aka gaza samun sakamako ƙarshe da za bayyana wanda ya lashe.
Yanzu haka an ɗage zaɓen har zuwa lokaci na gaba da ba a bayyana ba.
Fafatawa ta yi zafi tsakanin APC da PDP a Adamawa kamar yadda ta yi a jihar Kaduna.