City ta ƙara nuna ɓarakar Real Madrid, Arsenal ta ci gaba da jan zarenta

Asalin hoton, Getty Images
Ihun da aka yi wa tsohon mai horas da ƙungiyar Barcelona, Pep Guardiola a lokacin da ya shiga filin wasa na Bernabéu ya rikide zuwa sowar murna a lokacin da Manchester City ta shiga gaban Real Madrid, kuma a ƙarshe ta lakada wa mai masaukin bakin kashi a karawar da suka yi ta gasar Champions League a ranar Laraba.
Wannan rashin nasara da Real Madrid ta yi a gida ya ƙara ɗora ayar tambaya kan makomar koci Xabi Alonso a ƙungiyar.
Real din ta sha kashi ne da ci 1-2 a hannun City, wasan da ya kasance mafi jan hankali a ranar Laraba, was ana shida a matakin rukuni a gasar zakarun Turai ta Champions League a kakar 2025-26.
A ɗaya was an da aka yi ta muhawara kafin buga shi, Arsenal ta bi Club Brugge har gida ta sharara mata ƙwallo 3, inda aka tashi 0-3.
Ɗan wasa Noni Madueke ne ya shana a wasan, inda ya zura ƙwallo biyu kafin daga ƙarshe kyaftin Gabriel Martinelli ya cike ta uku da ƙayatacciyar ƙwallon da ya zura.
Arsenal ce ƙungiya daya tilo da har yanzu ba a doke ta ba a gasar ta wannan kaka.
Club Brugge 0-3 Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Wasa ɗaya Club Brugge ta yi nasara daga fafatawa 18 a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Ingila, aka doke ta 15 da canjaras uku.
Yanzu ƙungiyar ta Belgium an doke ta wasa uku daga 19 a gasar ta zakarun Turai a gida da lashe 12 da canjaras biyar.
Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a fafatawa tara da ƙungiyoyin Belgium a gasar zakarun Turai daga ciki ta lashe bakwai da canjaras biyu.
A bana Gunners ce kaɗai ta lashe dukkan wasa shida da fara kakar nan - Gasar zakarun Turai da ta fara da cin wasa biyar a jere ita ce a 2005/06, wadda ta kare a kwata fainal.
Real Madrid 1-2 Manchester City

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu haka Real Madrid da Manchester City sun kara da juna sau 15 a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai, inda Real Madrid ta yi nasara biyar, City ta ci biyar da canjaras biyar.
Sun fuskanci juna a kowacce kaka huɗu baya a Champions League.
A bara ne Real Madrid ta fitar da City a zagayen cike gurbi da suka yi 3-2 a wasan farko a Manchester da cin 3-1 a Sifaniya.
Real Madrid ta yi nasara 14 daga wasa 14 a Champions League zagayen cikin rukuni a gida da rashin nasara ɗaya.
Sakamakon wasannin da aka buga ranar Laraba:
- Athletic Bilbao 0-0 Paris St-Germain
- Borussia Dortmund 2-2 Bodo Glimt
- Bayern Leverkusen 2-2 Newcastle United
- Benfica 2-0 Napoli
- Club Brugge 0-3 Arsenal
- Juventus 2-0 Pafos
- Qarabag 2-4 Ajax
- Real Madrid 1-2 Man City
- Villarreal 2-3 Copenhagen











