Firaiministan Canada, Justin Trudeau ya sanar da yin murabus

Trudeau

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 1

Shekaru tara a matsayinsa na firaiministan Canada sun zo ƙarshe bayan ya sanar da yin murabus a matsayinsa na jagoran jam'iyya mai mulki ta Liberal Party.

Hakan na nufin jam'iyyar tasa za ta fito da sabon mutumin da zai maye gurbinsa a babban zaɓen da za a yi da alkaluma ke nuna cewa ba za su yi nasara ba.

"Na ƙudiri niyyar yin murabus a matsayina na jagora kuma firaiminista, bayan jam'iyya ta zaɓi jagoranta a nan gaba," kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Babu dai cikakken bayani kan har zuwa wane tsawon lokaci ne Trudeau zai ci gaba da kasancewa a ofis a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

Trudeau ya tabbatar da cewa ya samu sahhalewar gwamna Janar na Canada wajen rushe duk wani aikin majalisa har zuwa ranar 24 ga watan Maris.

Hakan ana ganin zai bai wa jam'iyyar Liberal Party wadataccen lokaci wajen zaɓar shugabanta a majalisar, sannan zai kange jam'iyyun adawa a koƙarinsu na kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna.

Ana yi wa murabus ɗin da Trudeau ya yi kallon ƙarshen wani salon siyasar ƙasar Canada.

Justin Trudeau dai ya hau kujerar firaiministan Canada ne a 2025, lokacin jam'iyyarsa ta Liberal ta samu gagarumar nasara bayan kwashe dogon lokaci tana fuskantar rashin kuzari a siyasance kasancewar jam'iyyar ta zama kurar baya a majalisar dokoki.

Trudeau, wanda ɗa ne ga tsohon firaiministan ƙasar, Pierre Trudeau ya ceci jam'iyyar sannan ya sake gina ta.

Yanzu dai ƴan jam'iyyar Liberal ɗin na buƙatar ƙara wa jam'iyyar kuzari idan dai har suna son samun nasara a babban zaɓen da ke tafe wanda ra'ayoyin jama'a ke nuna jam'iyyar ka iya fuskantar matsala.