Gobara ta kashe ɗalibai 17 a makarantar kwana a Kenya

Shugaba Ruto

Asalin hoton, Ephantus Maina

Lokacin karatu: Minti 1

'Yansandan Kenya sun ce akalla ɗalibai 17 suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wata makaranta da ke Nyeri a tsakiyar ƙasar.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar na cewa gobarar da ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai na makarantar Hillside Endarasha Academy, ta raunata wasu ɗalibai guda 14.

Har yanzu dai babu wasu bayanai kan abin da ya haddasa gobarar.

Sannan ana sake nuna fargabar yiwuwar alƙaluma mamatan ya zarta abin da aka tabbatar kawo yanzu.

Shugaban ƙasar, William Ruto ya kira gobarar da ''mummunar gobara mai tayar da hankali'' sanan ya buƙaci gudanar da bincike game da lamarin.

"Duk wanda aka samu da sakacin da ya haddasa gobarar zai fuskanci hukunci ," kamar yadda Mista Ruto ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Rundunar 'yansandan ƙasar ta ce tuni aka tura tawagar masu bincike zuwa makarantar.

Kakakin rundunar 'yansandan ƙasar, Resila Onyango ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa gawarwakin da aka gano sun ƙone sosai ''ta yadda ba za aiya gane su ba''.

"Akwai yiwuwar sake gano ƙarin gawarwaki idan masu aikin ceto suka tsananta aikinsu a wurin'' in ji ta..

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ƙasar ta ce za ta kwantar wa ɗaliban makarantar da iyayensu da malaman makarantar hankalinsu ta yadda zai rage musu raɗaɗi da damuwa game da abin da ya faru.

Gobara a makarantu ba sabon al'amari ba ne a makarantun kwana a Kenya

Ko a shekarar 2017, ɗalibai 10 ne suka mutu sakamakon wata gobara a makarantar sakandiren mata ta Moi a birnin Nairobi.

Haka ma a shekarar 2014 aƙalla ɗalibai 67 ne suka mutu a gundumar Machakos da ke kudu maso gabashin birnin Nairobi, sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wata makaranta.