Bayanai kan gawurtacciyar Masarautar Qatar da ɗumbin arzikin ƙasar

Tun da aka fara buga Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 a Qatar, ƙasar ta kasance tana jan hankalin mutane a sassa daban-daban na duniya, musamman ta fannin irin makuɗan kuɗaɗen da ta kashe wajen karɓar baƙuncin gasar.

Qatar ta daɗe da fara neman karbar baƙuncin gasar amma ba ta samu ba sai a shekarar 2010, wani lamari mai cike da ce-ce-ku-ce.

Ƙasar ta yi nasara a kan Amurka da Koriya ta Kudu da Japan da Australiya da su ma suka nemi a ba su baƙuncin gasar.

Sai dai an yi ta zargin Qatar ɗin da bai wa jami’an Fifa cin hancin dala miliyan 3.7 don neman ta samu baƙuncin, amma an wanke ta daga zargin bayan da Fifa ta shafe shekara biyu tana bincike kan hakan.

To sai dai duk da haka ba a daina zargin ta kan cin hanci ba har zuwa yanzu.

Nasarar ta Qatar ta jawo ce-ce-ku-ce mai tarin yawa musamman kan batun zarge-zargen take haƙƙin ɗan adam kamar na hana shan barasa da hana nuna goyon bayan ƴan luwaɗi da maɗigo da kuma zargin gallazawa ma’aikatan ƙwadago na wasu ƙasashen da ta ɗauka don yin aikin gina filayen wasannin.

Wasu kuma sun yi ta Allah-wadan ba ta baƙuncin ne saboda tsananin zafin ƙasar, kasancewarta a yankin hamada.

Sai dai duk da sarƙaƙiyar da ta dabaibaye batun karɓar baƙuncin, Qatar ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ƙayatar da ƙasashen duniya, inda ta narka biliyoyin daloli don gina sabbin filayen wasa har bakwai, baya ga ɗaya da aka yi wa kwaskwarima.

Baya ga haka kuma, ƙayatuwa irin ta ƙasar bai hana ta sake gina wasu wuraren masu ban sha’awa da ɗaukar hankalin duniya ba, kamar wuraren sauƙar baƙi na tanti wato Fans Village.

Irin wannan gagarumin shiri da Qatar ta yi wa karbar baƙuncin ƙwallon ƙafar ya sa mutane tambayar ko nawa ƙasar ta kashe wajen lamarin.

Mujallar Forbes ta ruwaito cewa Qatar ta kashe dala biliyan 220.

Abu na gaba da ke kara-kaina a zuƙatan mutane a faɗin duniya shi ne, wane irin arziki Qatar ke da shi da har za ta kashe waɗannan makuɗan kuɗaɗe?

Amsar ita ce, kasancewar ta ɗaya daga cikin ƙasashen duniya mafiya ɗumbin arzikin man fetur.

Wace ce Qatar?

Qatar - wadda a baya take cikin ƙasashen matalauta a yankin Gulf - a yanzu tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi arziki a yankin Gulf.

Ƙasar na amfani da ɗumbin kuɗaɗen da take samu daga tarin arzikin gas domin gina kanta, da kuma karfafa matsayinta a idon ƙasashen duniya, ciki kuwa har da batun samun damar ɗaukar gasar Kofin Duniya na 2022 mai cike da ce-ce-ku-ce.

Shugabbanin ƙasashen Larabawa ba su fiye la'akari da katsalandan da ƙasar ke yi a yankin ba, kamar goyon bayan ƙungiyar Falasdinawa ta Hamas, da kuma ƙungiyar ISIS a ƙasashen Masar da Siriya.

A shekarar 2017 ƙasar Saudiyya ta jagoranci yunƙurin dakatar da ƙasar da zargin da suke yi mata na goyon bayan ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.

Sai dai da baya an sasanta dangantakar diflomasiyyar.

Ƙasar na amfani da kuɗin mai da take samu wajen inganta rayuwar al'ummarta, yayin da gwamnati ke biyan tallafi mai yawa kan abubuwa da dama a ƙasar.

To sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na sukar ƙasar game da yadda take tafiyar da lamarin ma'aikata 'yan ci-rani.

Qatar na da yawan al'umma da ya kai miliyan biyu da dubu 900, kuma kashi 99 cikin 100 na al'ummar ƙasar na zaune ne a birane.

Yaya Masarautar Qatar take?

Ita ce masarautar da iyalanta ke bayyana cikakkiyar ma'anar bambanci tsakanin masu kuɗi da 'hamshaƙan' attajirai.

Rayuwar sSarkin Qatar tare da iyalansa na bayyana cikakkiyar ma'anar ƙarfin mulki da kuma ƙarfin kuɗi.

An san iyalan gidajen sarauta da yin rayuwa ta facaka, to amma iyalan masarautar Qatar sun kai 'maƙura' a fagen rayuwar facakar.

Kama daga manyan gidaje na alfarma zuwa manya-manyan jiragen ruwa, da ƙananan motocin alfarma, iyalan masarautar sun kafa tarihi a rayuwar jin daɗi a duniya.

Gawurtacciyar masarauta ce mai ɗumbin arzikin da ya zarta na Elon Musk da Jeff Bezos idan aka haɗe su waje guda. Mujallar Forbes ta yi ƙiyasin cewa dukiyar masarautar ta kai dala biliyan 335.

Masarauta ce mai ƙunshe da tarin attajirai da sarakuna da ke zaune a manyan fadoji, kuma suna da jirgin Boeing 747 a matsayin jirgin hawa mallakinsu.

Gidan Masarautar Qatar, wanda a yanzu Sarki Tamim bin Hamad Al Thani ke jagoranta na ɗaya daga cikin iyalai mafiya arziki a faɗin duniya.

Manya-manyan gine-gine a Doha da Landan

Baya ga Babbar fadar masarautar da ke birnin Doha, wasu iyalan masarautar na rayuwa a birane da dama ciki har da tsakiyar birnin Landan.

Matar sarkin ƙasar mai suna Mozah bint Nasser Al Missned ta sayi wani gini da ake kira Cornwall Terrace a tsakiyar birnin Landan wanda kuɗinsa ya kai dala miliyan 80.

Haka kuma ta biya ƙarin dala miliyan 40 domin mallakar wasu gine-ginen da ke kusa da shi, lamarin da ya sa shi zama ɗaya daga cikin rukunin gidaje mafiya tsada a birnin.

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa katafaren ginin na ƙunshe da wuraren ninƙaya, da wuraren gyaran gashi, da ɓangaren renon yara da wuraren wasanni da wuraren gyaran jiki, da wuraren aika saƙonni, da kuma ɓangaren da ke ɗauke da na'urorin motsa jiki.

Haka kuma an ɗauki hoton Yariman ƙasar Khalifa bin Hamad bin Khalifa Al Thani a lokacin da yake tuka wata karamar motar alfarma ƙirar 'Bugatti Divo' a tsakiyar birnin da aka ƙiyasta kuɗinta ya kai dala miliyan shida.

An aika masa motar zuwa birnin Landan ne tare da wasu motocin biyu ƙirar 'Lamborghini Sian FKP 37' da kuma 'Ferrari Monza SP2 '.

Mallakar jirgin sama na hawa

Masarautar Qatar tana da jirgin sama na hawa ƙirar Boeing 747-8, wanda kuɗinsa ya kai dala miliyan 600.

Ƙaton jirgi ne mai hawa biyu wanda ke ɗauke da ban-ɗaki 10, da kuma ɗakunan kwanciya masu ɗauke da gadajen alfarma a cikinsu.

Jirgin tamkar wata ƙaramar fada ce da aka yi wa cikinsa kwalliya da launin shuɗi da fari da kuma ruwan zinare.

Haka kuma jirgin zai iya ɗaukar fasinjoji 76 da ma'aikatan jirgi 18.

Wani abin ban sha'awa shi ne jirgin na ɗauke da wani ɗan ƙaramin asibiti a cikinsa.

Zuba jari a ɓangaren wasanni

Soyayyar da masarautar Qatar ke yi wa wasanni ta samo asali ne daga soyayyar da suke yi wa abubuwa na jin daɗi.

Sarkin ƙasar Tamim bin Hamad Al Thani ya yi ƙoƙari matuƙa wajen ganin ƙasar ta karbi baƙuncin Gasar kwallon kafa ta cin Kofin Duniya na 2022.

A matsayinsa na shugaban kwamitin wasannin Olympic na ƙasar, shi ne ya jagoranci neman ɗaukar nauyin baƙuncin gasar ta Kofin Duniya.

Yana daga cikin na gaba-gaba a masu ƙarfin hannun jari a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain.

Haka kuma a shekarar 2010, ɗaya daga cikin iyalan masarautar mai suna Sheikh Abdullah Bin Nasser Al-Thani ya sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Malaga a ƙasar Sifaniya.