Ebola ta tilasta rufe makarantu a Uganda

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Uganda ta bayar da umarnin rufe makarantun kasar makonni biyu kafin lokacin da aka tsara saboda barkewar annobar Ebola.
Hukumomin kasar sun yi haka ne a kokarin dakile barkewar cutar mafi yaduwa a tarihin kasar.
Ministar kiwon lafiya ta kasar Dr Jane Ruth Aceng ta fada wa BBC cewa an dauki matakan tabbatar da tsaron lafiyar yaran da ke fita da kuma shiga cikin yankin da cutar ta yi kamari da aka sanya wa dokar kulle.
Matakin ya biyo bayan kamuwa da cutar da mutum 141 suka yi a babban birnin kasar, Kampala, inda 55 da suka rasa rayukansu.
Kwashe yara daga gundumomin Mubende da kassanda wadanda wurare ne da aka fi samun yawan mutanen da suka harbu da cutar sun kasance wuraren da ministar kiwon lafiyar ta fi nuna damuwa.
Ministar ta ce za a hana iyaye zuwa wadannan yankuna biyu da aka sanya wa dokar kulle.
A maimakon haka za a yi amfani da motar makaranta domin zuwa da su Kampala babban birnin kasar daga nan kuma za su shiga motocin bas-bas da gwamnati ta bayar wadanda za su wuce da su gidajensu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa yaran ba su yi mu'amulla da al'ummomin yankunan da aka samu barkewar annobar ta Ebola ba.
Yayin da suke barin makarantun kwana wadanda kawo yanzu ba a samu wani da ya kamu da cutar a ciki ba.
Sai dai duk da cewa dalibai sun samu damar zuwa gida da wuri domin hutun Kirismeti wasu na ganin cewa gwamnati ta yi hanzarin daukar matakin rufe makarantu makonni biyu kafin a kammala karatun zango.
Ana ganin ta yi hakan ne domin dakile bazuwar annobar Ebola wadda ba a taba ganin irinta ba a tarihin kasar ta gabashin Afirka.
Wasu masana sun nuna rashin jin dadinsu game da matakin rufe makaruntun saboda a cewarsu idan aka bar yaran suka kara makonni biyu a cikin makaruntu wannan zai fi tasiri wajen dakile yaduwar cutar.
Saboda a ganinsu kwayar cutar kan dauki kwana biyu zuwa makonni uku kafin ta soma bayyana a jikin mutum.
A cikin kwanakin watanni biyu da suka gabata mutum 55 suka rasa rayukasu ciki har da yara 23.
Kwayar cutar Ebolar ta Uganda nau'in ta Sudan ce, wadda babu wani tabbataccen riga-kafinta a yanzu.
Ba kamar irin ta Zaire ba wadda ta yadu a kwanan nan a Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo.











