Mece ce Ebola kuma me ya sa annobar da ta ɓarke a Uganda ta yi ƙamari?

Asalin hoton, AFP
Annobar cutar Ebola a ƙasar Uganda na ƙoƙarin ganin ta gagari hukumomi fiye da sauran annoba da suka faru a baya-bayan nan, amma shugaban ƙasar ya ce ba zai saka dokar kulle ba.
Zuwa yanzu an tabbatar da mutum 31 da suka harbu da ita duk da cewa ana tunanin akwai wasu da suka kamu.
Mece ce Ebola?
Wata cuta ce mai haɗarin gaske wadda alamunta suka ƙunshi zazzaɓi nan take, da rashin ƙarfin jiki, ciwon gaɓɓai da kuma bushewar maƙogwaro.
Sauran abubuwan da za a gani sun haɗa da amai, da gudawa - a wasu lokuta - zubar a ciki da wajen jiki.
Lokacin da ƙwayoyin cutar ke ɗauka kafin su ƙyanƙyashe a jikin mutum kan fara daga kwana biyu zuwa sati uku.
Ebola ka iya samun alaƙa da sauran cutuka kamar zazzaɓin maleriya da kuma na tayifod.
Me ya sa wannan annobar ta fi ƙamari?
Dalilin da ya sa sai da aka shafe mako uku kafin a gano mutum na farko da ya kamu da ita a ranar 20 ga watan Satumba, hakan ya jawo fargaba.
Ebola na yaɗuwa a tsakanin mutane ta hanyar yin taɓa jiki ko kuma ababen da ke fitowa daga jiki, ko muhallin da mai cutar ya taɓa.
Akwai haɗari mai girma idan masu yi wa gawa wanka suka taɓa jikin mamacin. Akasarin mutum 31 da suka kamu da cutar sun fito ne daga yankin Mubende na Uganda waɗanda shida daga cikinsu suka mutu.
Sai dai kuma adadin zai iya zarta haka. Ma'aikatar lafiya ta ce mutum 18 suka mutu kuma aka binne su tun kafin a yi musu gwaji.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yiwuwar mutuwa bayan kamuwa da cutar na tsakanin kashi 41 zuwa 100 cikin 100.
Ko akwai rigakafi?

Asalin hoton, Getty Images
Wani abin damuwar shi ne; wannan nau'in na Ebola na Sudan ne wanda zuwa yanzu babu wata rigakafinsa da aka amince da shi, saɓanin wanda aka fi sani na Zaire.
Hakan na nufin ba za a iya yi wa ma'aikatan lafiya rigakafin cutar ba, waɗanda shida daga cikinsu suka mutu.
Nau'in Zaire ne ya fi haddasa bala'in annobar Ebola a Yammacin Afirka daga Disamban 2013 zuwa 2016. Mutum fiye da 11,000 ne suka mutu.
Yayin da mutum fiye da 28,000 suka kamu a Guinea da Liberiya da Saliyo, masana kimiyya sun yi ta binciken nemo rigakafin cutar.
Ta yaya Ebola ke yaɗuwa?
Ebola na tasowa ne daga jikin dabbobi kamar birai da jemagu da gwanki zuwa mutane.
An yi imanin cewa naman dabbobin daji da mutane ke kamawa ne suka fi zama da cutar.
Daga nan sai ta yaɗu tsakanin mutane ta hanyar mu'amala kai-tsaye ko kuma abin da ke fita daga jiki kamar jini, da yawu, da amai, da maniyyi, da ruwan farjin mata, da fitsari, da gumi.
Mazan da suka warke daga cutar, akan same ta a cikin maniyyinsu bayan tsawon wani lokaci.
Wane irin matakin kariya ake iya ɗauka?

Asalin hoton, EPA
Don kare yaɗuwar cutar, ma'aikatan lafiya na ba da shawarar a guji taɓa jikin mai ɗauke da ita, kamar musabaha, da kuma yawan wanke hannu da sabulu da wanke dandariyar ƙasa da ruwa mai sinadari.
Abu ne kuma mai muhimmanci a dinga keɓance masu ɗauke da cutar da kuma waɗnda suka yi mu'amala da su.
Akasari ƙasashe kan samar da wuraren killace mutanen da ake zargin suna ɗauke da ita da kuma wuraren gwaji na musamman don gano waɗanda ke ɗauke da cutar.
A gabashin Congo wadda ke da iyaka da Uganda, mutanen da suka warke daga cutar na taka muhimmiyar rawa wajen kulawa da sabbin kamuwa saboda an tabbatar cewa ba za su sake kamuwa ba.











