Tsohon minista ya karkatar da kudin kiwon lafiya

Ana tuhumar Oly Llungu da laifukan cin hanci

Asalin hoton, AFP / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ana tuhumar Oly Llungu da laifukan cin hanci da karkatar da kudaden yaki da Ebola

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, jami'an tsaro sun damke tsohon ministan lafiya na kasar a kan tuhumar da ake masa cewa ya aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Oly Llunga ne ya jagoranci shirin yaki da annobar cutar Ebola na kasar na tsawon fiye da shekara guda.

Fiye da mutum 2000 sun rasa rayukansu tun da cutar ta bayyana a yankunan gabashin kasar na Ituri da Arewacin Kivu.

Tsohon ministan yayi farin jini a shekarun baya, amma yanzu ana tuhumarsa da karkatar da kudaden da aka ware domin yakar annobar Ebola.

Ma'aikatan lafiya na duba wadanda ake tuhuma da kamuwa da Ebola

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ma'aikatan lafiya na duba wadanda ake tuhuma da kamuwa da Ebola

Jami'an 'yan sandan Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun fara gudanar da bincike kan batun kuma Oly Llunga ya sha tambayoyi a hannun su, sai dai ya musanta aikata wani laifi kan wannan batun.

A ranar Asabar, 'yan sanda sun ce suna da kwararan dalilai da suka tabbatar da tsohon ministan na shirin tserewa daga kasar.

Amma BBC ba ta iya tabbatar da ikirarin na jami'an tsaron ba.

Mista Lunga wanda ya ajiye aikinsa na minista ne a watan Yulin da ya gabata, jim kadan bayan an tube shi daga mukamin jagoran hukumar da ke yaki da cutar Ebola ta kasar, zai fuskanci shari'a.

A ranar Litinin a ke sa ran za a mika batun nasa ga ofishin mai shigar da kara domin gurfanar da shi a gaban kotu.