Liverpool ta bi sahun Man U kan Baleba, Aston Villa na zawarcin Marmoush

Carlos Baleba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Carlos Baleba
Lokacin karatu: Minti 3

Kawo yanzu Napoli na son ta sayi ɗan wasan tsakiyar Manchester United Kobbie Mainoo, mai shekara 20, amma za ta iya sayen ɗan wasan na Ingila ne kawai idan dan kasar Netherlands Noa Lang, mai shekara 26, ya bar kungiyar ta Italiya.(La Gazzetta dello Sport, via Football Italia), external

Real Madrid ta ci gaba da zawarcin ɗan wasan tsakiya na Sfaniya Rodri, sai dai ba za ta yi wani yunkuri daukar ɗan wasan mai shekara 29 sai a bazara saboda a lokacin ne zai shiga shekarar sa ta karshe a kwantaraginsa da Manchester City. (Marca - in Spanish), external

Chelsea na shirin yi wa ɗan wasan Ingila da Aston Villa Morgan Rogers, mai shekara 23 tayin Yuro miliyan 150 (Fichajes - in Spanish), external

Aston Villa na zawarcin ɗan wasa mai kai hari na Masar Omar Marmoush, mai shekara 26,wanda ba ya taka leda akai-akai a Manchester City. (Teamtalk), external

Dan wasan Ingila Jahmai Simpson-Pusey,mai shekara 20, na shirin yin baluguro zuwa Cologne a matsayin aro daga Manchester City.(Sun), external

Fulham ta yi wa ɗan wasan tsakiyar Faransa ,Arthur Atta mai shekara 22 tayin yuro miliyan 20 , sai dai kungiyar Udinese ta Italiya ta yi watsi da tayin . (Fabrizio Romano), external

Barcelona ce a kan gaba a zawarcin da ake yi wa ɗan wasa mai kai hari na Juventus Dusan Vlahovic, wanda zai kasance ba shi da kwantaragi a bazara kuma AC Milan da Bayern Munich su ma duk su na bibiyar halin da ɗan wasan kasar Serbia mai shekara 25 ya ke ciki . (La Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Ita ma Manchester City na cikin kungiyoyin da ke son ɗan wasan Troyes Mathys Detourbet, mai shekara 18,sai dai za ta fuskanci gogaya daga Roma da Monaco. (L'Equipe - in French), external

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Watakila ɗan wasan Manchester United da Ingila Harry Amass, mai shekara 18, ya rage yarjejeniyar aro da suka kulla da Sheffield Wednesday domin ya koma Stoke a sauran kakar wasani . (Sun), external

Liverpool ta bi sahun Manchester United da Tottenham wajen zawarcin dan wasan Brighton dan kasar Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 22.(CaughtOffside), external

Sai dai Liverpool ta yi watsi da zawarcin da take yi wa dan wasan baya na Newcastle United Sven Botman saboda damuwar ake nunawa akan raunin da dan wasan Netherlands din mai shekara 25 ke fama da shi.(Chronicle), external

Tottenham na bibiyar ɗan wasan Club Brugge da Girka Christos Tzolis mai shekara 23. (Teamtalk), external

Eintracht Frankfurt za ta biya yuro miliyan 1.5 don Nottingham Forest ta ba ta aron ɗan wasan Faransa mai kai hari Arnaud Kalimuendo mai sheakaa 23 kuma yarjejeniyar ta ba ta damar sayan dan wasan kan yuro miliyan 27. (Florian Plettenberg), external

Kungiyoyin Firimiya biyu ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar Lazio, Matteo Guendouzi,mai shekara 26, sai dai Fenerbache ta sha gabansu inda ta yi wa dan wasan Faransa tayin yuro miliyan 27 (L'Equipe - in French), external

Roma ta na son ta inganta bangaren 'yan wasanta masu kai hari kuma dan wasan Liverpool da Italiya Federico Chiesa mai shekara 28 na cikin wadanda take so (Corriere dello Sport - in Italian), external