Roma na son dawo da Salah, Man Utd za ta sayar da Fernandes

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na shirin sayen ɗanwasan baya na Club Brugge da Ecuador Joel Ordonez, mai shekara 21 a watan Janairu kan kuɗi har fam miliyan 43. (Mirror)
Roma na son sake dawo da ɗanwasan Liverpool da Masar mai shekara 33 Mohamed Salah amma sai a bazara za ta taya ɗanwasan. (La Repubblica - in Italian, subscription)
Manchester United na son ɗanwasan gaba na Crystal Palace da Faransa mai shekara Jean-Philippe Mateta da kuma ɗanwasan baya na Rennes mai shekara 20 Jeremy Jacquet. (Sky Sports)
Manchester United na shirin sayar da ɗanwasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 31, kuma akwai yiyuwar faruwar hakan a Janairu. (Football Insider)
West Ham na ci gaba da farautar ɗanwasan gaba na Fulham da Spain Adama Traore, mai shekara 29, kodayake albashinsa na iya kawo cikas ga yarjejeniyar. (Telegraph - subscription)
Real Madrid ana sa ran za ta ci gaba da tattaunawa kan sabunta kwangilar ɗanwasan Brazil Vinicius Jr, wanda ke son ci gaba da taka leda a ƙungiyar. (AS - in Spanish)
Chelsea na tunanin taya matashin ɗanwasan baya na Santos ta Brazil mai shekara 19 Souza, kodayake tana fuskantar hamayya daga AC Milan. (AS - in Spanish)
Fulham da Crystal Palace da Sunderland na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na Algeria Ilan Kebbal da ke murza leda a Paris FC mai shekara 27. (Football Insider)
Chelsea na son ɗauko ɗanwasan tsakiya na Girka da Genk Konstantinos Karetsas, wanda ake alaƙantawa da Arsenal. (Mirror)
Inter Milan na son kammala cinikin ɗanwasan baya na Switzerland Manuel Akanji da ta karɓo aro daga Manchester City. (Gazzetta - in Italian)
Bayern Munich za ta sayar da ɗanwasan tsakiya na Jamus Leon Goretzka a Janairu inda Tottenham da Arsenal da Manchester United suka nuna suna so.











